Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | MENE NE YAKE FARUWA A SAMA?

Tambayoyi Game da Ruhohin da Ke Sama

Tambayoyi Game da Ruhohin da Ke Sama

Shin ka taɓa yin tunani game da sama da kuma waɗanda ke zama a wurin? Idan ka taɓa yi, to ka san cewa ba kai kaɗai ba ne. Mutane sun yi shekaru da yawa suna muhawwara a kan wannan batun. Wasu sun gaskata cewa kakanninmu ne suke zama a sama kuma ya kamata mu riƙa daraja su. Wasu kuma sun ce wuri ne mai kyau da mala’iku da kuma mutane masu kirki da suka mutu suke zama. Ƙari ga haka, wasu sun gaskata cewa sama wurin zaman miliyoyin alloli ne.

Mutane da yawa sun gaskata cewa ba zai taɓa yiwu mu san abin da ke faruwa a sama ba domin babu wani mutumin da ya sauko daga sama da zai iya ba mu labarin. Amma irin wannan ra’ayin bai dace ba sam. Me ya sa? Domin Yesu ya yi rayuwa a sama kafin ya zo duniya. Kuma ya gaya wa malaman addinai a ƙarni na farko dalla-dalla cewa: “Na sauko daga sama, ba domin in yi nufin kaina ba, amma nufin wanda ya aiko ni.” Saboda haka, Yesu yana gaya wa almajiransa abin da shi da kansa ya shaida sa’ad da ya ce: “A cikin gidan Ubana akwai wurin zama da yawa.”​—⁠Yohanna 6:38; 14:⁠2.

Babu shakka, Jehobah shi ne Uban Yesu kuma sama ne ‘gidansa.’ (Zabura 83:18) Don haka, babu wanda zai iya bayyana sama fiye da Jehobah da kuma Yesu Kristi. Kuma sun bayyana wa wasu mutane masu aminci yadda sama yake ta wajen saukar musu da wahayi.

Talifi na gaba zai tattauna yadda Littafi Mai Tsarki ya kwatanta wahayin da mutane suka gani game da sama. Yayin da kake bincika waɗannan wahayin, ka san cewa sama ba wuri ba ne na zahiri da ake da abubuwa da za mu iya gani ko kuma taɓawa ba. Allah bai yi amfani da kalamai da kuma furucin da ba za mu iya fahimta ba wajen bayyana mana waɗannan wahayin. A maimakon haka, ya tsara su a hanya mai sauƙi da za mu iya fahimta. Bincika waɗannan wahayin zai taimaka maka ka san waɗanda suke zama a “wurin zama da yawa” da ke sama.