Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Allah yana amsa dukan addu’o’i kuwa?

SHIN ZA KA CE YANA AMSA ADDU’O’IN . . .

  • Kowa

  • Wasu mutane

  • Ba ya amsa addu’a

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE

“Ubangiji yana kusa da dukan . . . waɗanda suke kira gareshi da gaskiya.”​—Zabura 145:18.

ME KUMA ZA MU IYA KOYA DAGA LITTAFI MAI TSARKI?

  • Allah ba ya jin addu’o’in mutanen da ba sa masa biyayya. (Ishaya 1:15) Amma, za su iya ‘daidaita al’amari’ ta wajen canja salon rayuwarsu.​—Ishaya 1:​18, Littafi Mai Tsarki.

  • Idan muna so Allah ya amsa addu’armu, dole ne ta jitu da nufinsa da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki.​—1 Yohanna 5:⁠14.

Shin dole ne mu zauna ko durƙusa ko haɗa hannunmu ko kuma tsaya sa’ad da muke addu’a?

WASU SUN CE dole ne. Mene ne ra’ayinka?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE

Akwai misalan mutanen da Allah ya amsa addu’o’insu yayin da suka “zauna” ko “tashi” ko sunkuyar da “kansu” ko kuma “durƙusa.” (1 Labarbaru 17:16; 2 Labarbaru 30:27; Ezra 10:1; Ayyukan Manzanni 9:40) Zai iya amsa addu’armu a kowane irin yanayi.

ME KUMA ZA MU IYA KOYA DAGA LITTAFI MAI TSARKI?

  • Allah yana sauraron masu tawali’u.​—Zabura 138:6.

  • Kana iya yin addu’a a kowane yare ko kuma a cikin zuciyarka.​—2 Labarbaru 6:​32, 33; Nehemiya 2:​1-6.