Koma ka ga abin da ke ciki

Allah Ne Ya Halicci Iblis?

Allah Ne Ya Halicci Iblis?

Amsar Littafi Mai Tsarki

Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Allah bai halicci Iblis ba. Maimakon haka, ya halicci wani da ya mai da kansa Iblis. Littafi Mai Tsarki ya ce game da Allah: “Aikinsa cikakke ne; gama dukan tafarkunsa shari’a ne: Shi Allah mai-aminci ne, mara-mugunta, kuma, mai-adalci ne shi mai-gaskiya.” (Kubawar Shari’a 32:3-5) Daga cikin wannan ayar, mun sani cewa a wani lokaci Shaiɗan Iblis kamiltacce mai adalci ne, ɗaya daga cikin mala’iku ’ya’yan Allah.

A Yohanna 8:44, Yesu ya ce Iblis “ba ya tsaya a kan gaskiya ba,” yana nuna cewa akwai lokacin da Shaiɗan ya nuna gaskiya kuma bai yi laifi ba.

Amma, daidai kamar sauran halittun Jehobah masu basira, mala’ikan nan da ya zama Shaiɗan yana da ’yancin yin zaɓe tsakanin nagarta da mugunta. Ya mai da kansa Shaiɗan, wato, “Ɗan adawa” ta wurin matakin da ya ɗauka na hamayya da Allah kuma ya zuga ma’aurata na farko su bi shi.—Farawa 3:1-5; Ru’ya ta Yohanna 12:9.