Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Kwarin Elah

Labarin Dauda da Goliyat​—⁠Ya Faru da Gaske Kuwa?

Labarin Dauda da Goliyat​—⁠Ya Faru da Gaske Kuwa?

Wasu suna tunani ko labarin Dauda da Goliyat ya faru da gaske ko kuwa ƙage ne. Shin ka yi wannan tunanin sa’ad da kake karanta talifin da ya gabata? Idan haka ne, to ka yi la’akari da waɗannan tambayoyi uku.

1 | Shin zai yiwu tsayin mutum ya kai kafa tara da rabi ne, wato mita biyu da ɗigo tara?

Littafi Mai Tsarki ya ce tsayin Goliyat “kamu shida ne da taƙi.” (1 Sama’ila 17:⁠4) Kamu shida, inci goma sha bakwai da ɗigo biyar ne. Taƙi ɗaya kuma inci takwas da ɗigo saba’in da biyar ne. Idan an haɗa duka, ya zama wajen kafa tara da inci shida. Wasu sun ce ba zai yiwu tsayin Goliyat ya kai haka ba. Amma ka yi la’akari da mutum mafi tsayi a duniya a zamaninmu. Wannan mutumin yana da tsawon sama da kafa takwas da inci sha ɗaya, wato mita biyu da ɗigo bakwai. Shin zai yiwu a ce Goliyat ya fi wannan mutumin tsayi da inci shida kawai? Shi ɗan ƙabilar Rephaim ne kuma an san su da yin tsayi sosai. Wani littafin da Masarawa suka rubuta a ƙarni na 13 kafin haihuwar Yesu ya ce wasu ƙattai a yankin Ka’aniyawa suna wuce tsawon kafa takwas, wato mita biyu da ɗigo huɗu. Saboda haka, ko da yake tsayin Goliyat abin mamaki ne, amma abin da Littafi Mai Tsarki ya ce gaskiya ne.

2 | Dauda ya wanzu kuwa da gaske?

Akwai wani lokacin da marubuta suke neman su ce labarin Sarki Dauda ƙage ne, amma sun ci tura. Masu tone-tonen ƙasa sun gano wani dutse da aka rubuta “birnin Dauda.” Bugu da ƙari, Yesu ya yi magana game da Dauda. (Matta 12:3; 22:​43-45) An rubuta sunan Sarki Dauda sau biyu cikin sunayen mutanen da aka ce kakan-kakannin Yesu ne. (Matta 1:​6-16; Luka 3:​23-31) Babu shakka, Dauda ya wanzu da gaske.

3 | Shin wuraren da aka ambata a wannan labarin sun wanzu da gaske kuwa?

Littafi Mai Tsarki ya ce an yi yaƙin a Kwarin Elah. Ya kuma ƙara da cewa Filistiyawan sun kafa sansani a tsakanin garuruwa biyu, wato Sokoh da Azekah. Isra’ilawa kuma sun taru a bisa dutsen a wancan hayi. Shin waɗannan wuraren sun wanzu da gaske?

Ka lura da abin da wani da ya ziyarci yankin a kwana-kwanan nan ya ce: “Mutumin da ya kai mu yawon zagaya ba mai bin addini ba ne. Ya kai mu Kwarin Elah. Sai ya haura da mu kan wani dutse. Sa’ad da muka kai saman, sai ya karanta mana littafin 1 Sama’ila 17:​1-3. Bayan haka, sai ya ce mana: ‘Garin Sokoh wanda mutane sun daina zama a ciki yana ta hannun hagu.’ Sai ya sake juyawa ya ce, ‘A gefen dama kuma za ku ga garin Azekah da mutane sun riga sun daina zama a ciki. Filistiyawa sun kafa sansani a tsakanin garurrukan nan biyu a wannan tudun da muka fuskanta. Saboda haka, wataƙila a inda muke tsaye ne Isra’ilawa suka kafa sansani.’ Sai na soma tunanin yadda Saul da Dauda suka tsaya a inda nake tsaye. Bayan haka, sai muka gangara kuma muka tsallake wani kogi da ya kusan bushewa kuma yana cike da duwatsu. Sai na soma tunanin yadda Dauda ya tsuguna a wurin ya kwashe duwatsu biyar da ya yi amfani da ɗaya cikinsu wajen kashe Goliyat.” Wannan mutumin da kuma sauran mutanen sun yi mamaki sosai yadda Littafi Mai Tsarki yake ɗauke da labaran da suka taɓa faruwa.

Babu dalilin yin shakkar labaran da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Mutane da kuma wuraren da aka ambata a ciki sun wanzu. Abu mafi muhimmanci kuma shi ne cewa hurarriyar Kalmar Allah ce. Saboda haka, Allah na gaskiya Wanda ba zai yiwu ya yi “ƙarya” ba, shi ne ya faɗe su.​—⁠Titus 1:2; 2 Timotawus 3:16.