Koma ka ga abin da ke ciki

Me Ya Sa Ya Kamata In Yi Addu’a? Allah Zai Ji Addu’ata Kuwa?

Me Ya Sa Ya Kamata In Yi Addu’a? Allah Zai Ji Addu’ata Kuwa?

Amsar da Littafi Mai Tsarki ya ba da

 Hakika, zai saurara. Misalan da ke cikin Littafi Mai Tsarki da abubuwan da mutane suka shaida sun nuna cewa Allah yana amsa addu’o’i. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Za ya biya muradin wadanda ke tsoronsa [wato, Allah]; Za ya kuma ji kukarsu, ya cece su.” (Zabura 145:19) Amma ko Allah zai amsa addu’arka ko babu, ya dangana ga yadda ka yi addu’ar ne.

Abu mafi muhimmanci a gaban Allah

  •   Allah ne za mu yi wa addu’a, ba Yesu ko Maryamu ko waliyai ko mala’iku ko kuma siffofi ba. Jehobah Allah ne kadai “Mai-jin addu’a.”​—Zabura 65:2.

  •   Ya kamata addu’armu ta jitu da nufin Allah, ko kuma ka’idodinsa da ke cikin Littafi Mai Tsarki.​—1 Yohanna 5:14.

  •   Yin addu’a cikin sunan Yesu, ya nuna cewa kana daraja Yesu. “Ba mai-zuwa wurin Uban sai ta wurina,” in ji Yesu.​—Yohanna 14:6.

  •   Ka yi addu’a ba tare da shakka ba, kuma ka roki Allah don ka kasance da bangaskiya sosai.​—Matta 21:22; Luka 17:5.

  •   Ka kasance da tawali’u da kuma gaskiya. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ubangiji madaukaki ne, yakan lura da masu tawali’u.”​—Zabura 138:6.

  •   Ka nace. Yesu ya ce: “Ku roka, za a ba ku,” kuma ku yi hakan babu fashi.​—Luka 11:9.

Abin da ba shi da muhimmanci a gaban Allah

  •   Kabilarka ko kasar da ka fito. “Allah ba mai-tara ba ne: amma a cikin kowace al’umma, wanda yake tsoronsa, yana aika adalci kuma, abin karba ne gare shi.”​—Ayyukan Manzanni 10:34, 35.

  •   Yadda za ka kasance kafin ka yi addu’a. Za ka iya yin addu’a ga Allah a zaune, ka durkusar da kai, a durkushe, ko kuma a tsaye.​—1 Labarbaru 17:16; Nehemiya 8:6; Daniyel 6:10; Markus 11:25.

  •   Ko ka yi addu’a da babbar murya ko kuma a zuci. Allah yana amsa addu’o’i har da wadanda ake yi a zuci ma.​—Nehemiya 2:1-6.

  •   Ko matsalolinka masu yawa ne ko kadan. Allah dai yana karfafa ka ka ‘zuba dukan alhininka a bisansa, domin yana kula da kai.’​—1 Bitrus 5:7.