Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

KA YI KOYI DA BANGASKIYARSU | DAUDA

‘Yakin Na Jehobah Ne’

‘Yakin Na Jehobah Ne’

DAUDA ya tsaya da ƙarfi don kada sojojin da ke gudu su ture shi. Sojojin sun zura idanu don tsoro sa’ad da suke tserewa daga bakin dāga. Me ya tsoratar da su? Babu shakka, Dauda yana jinsu suna ta maimaita wata kalma. Sunan mutum ne suke ta kira. Ga katon mutumin can tsaye kuma wataƙila Dauda bai taɓa ganin irin wannan katon ba.

Sunansa Goliyat ne! Dauda ya fahimci dalilin da ya sa sojojin suka tsorata don katon mutum ne da babu irinsa. Nauyin Goliyat ya kai na mutane biyu ko da bai riƙe wani makami ba. Amma yanzu yana ɗauke da makamai kuma yana da ƙarfi sosai. Ban da haka ma, ƙwararre ne a yaƙi. Sai Goliyat ya yi ihu don ya tsoratar da su. Ka yi tunanin yadda muryar Goliyat ta kasance sa’ad da yake ihu a duwatsu don ya zolayi rundunar Isra’ila da kuma sarkinsu Saul. Ya ce duk wanda ba ya jin tsoro ya fito don su raba raini!​—⁠1 Sama’ila 17:​4-10.

Isra’ilawa suka tsorata ba kaɗan ba. Sarki Saul ma ji tsoro. Dauda ya ji cewa Goliyat ya yi fiye da wata ɗaya yana zolayar Isra’ilawa. Rundunar Filistiyawa da Isra’ilawa sun ƙi su janye yayin da Goliyat ya ci gaba da tsokanar Isra’ilawa kowace rana. Dauda bai ji daɗi da hakan ba sam. Abin baƙin ciki ne cewa sarkin Isra’ila da kuma rundunarsa har da ‘yan’uwansa uku sun tsorata! A ganin Dauda, wannan kafirin, wato Goliyat bai raina rundunar Isra’ila kaɗai ba amma har da Allahnsu Jehobah. Amma mene ne Dauda matashi zai yi? Kuma mene ne za mu koya daga bangaskiyar Dauda?​—⁠1 Sama’ila 17:​11-14.

‘KA SHAFE SHI, GAMA WANNAN SHI NE!’

Bari mu tattauna abubuwan da suka faru a watannin baya kafin wannan lokacin. Dauda matashi ne mai kyan gaske kuma wataƙila yana tsakanin shekaru sha uku zuwa sha tara. Wata rana da yamma Dauda yana kiwon tumakin mahaifinsa a gefen dutse kusa da Bai’talami. Kuma Dauda yana yawan kaɗa molo a wuraren da babu surutu sa’ad da yake kiwo. Me yake motsa shi yin hakan? Halittun Jehobah ne kuma ya ƙware a kiɗi don ya jima yana koyo. Amma mahaifin Dauda ya gaya masa ya dawo gida nan da nan a wannan yammar.​—1 Sama’ila 16:12.

Da ya iso gida, sai ya ga mahaifinsa, wato Jesse yana magana da wani dattijo. Wane dattijo ke nan? Annabi Sama’ila ne. Jehobah ya aike shi ya je ya shafe wani da zai zama sarkin Isra’ila a cikin yaran Jesse! Jesse ya riga ya nuna wa Sama’ila yaransa bakwai, amma Jehobah bai zaɓe su ba. Sa’ad da Dauda ya dawo gida, sai Jehobah ya gaya wa Sama’ila cewa: “Ka shafe shi: gama wannan shi ne.” A gaban ‘yan’uwan Dauda, sai Sama’ila ya ɗauki ƙaho cike da māi ya shafe Dauda da shi. Rayuwar Dauda ta canja tun daga wannan ranar. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ruhun Ubangiji ya sauko da iko a kan Dawuda tun daga wannan rana zuwa gaba.”​—⁠1 Sama’ila 16:​1, 5-11, 13.

Dauda ya ɗaukaka Jehobah don zaki da bear da ya kashe

Shin Dauda ya yi ƙoƙari ya yi wa Saul juyin mulki ne? Sam, bai yi hakan ba. A maimakon haka, ya jira har sai ruhun Jehobah ya nuna masa lokacin da ya dace ya soma sarautar. Saboda haka, sai ya ci gaba da kiwon da yake yi. Kuma ya yi wannan aikin da ƙwazo da kuma ƙarfin hali. Akwai lokacin da zaki da kuma bear suka so su cinye tumakin mahaifinsa sau biyu. Dauda bai kori waɗannan dabbobin ba, amma ya kashe su don ya kāre tumakin mahaifinsa. A lokutan nan biyu, shi kaɗai ne ya kashe waɗannan dabbobin.​—1 Sama’ila 17:​34-36; Ishaya 31:4.

Daga baya, sarki Saul ya ce a kirawo Dauda. Domin abubuwan da yake yi sun shiga kunnen Sarkin. Saul ya kasa samun tagomashin Jehobah domin bai bi umurninsa ba ko da yake shi mayaƙi ne mai ƙarfi. Jehobah ya janye ruhunsa daga Saul, don haka, sai mummunan ruhu ya shige shi kuma ya soma nuna wasu halayen da ba su dace ba kamar su fushi da ƙishi da kuma faɗa. Sa’ad da wannan mummunan ruhu ya shigi Saul, waƙa ce take kwantar masa da hankali. Wasu cikin bayin Saul sun san cewa Dauda ya iya waƙa da kuma yaƙi. Don haka, an kirawo Dauda ya zama mai waƙa a fādar Saul da kuma mai-ɗauka masa makamai.​—1 Sama’ila 15:​26-29; 16:​14-23.

Babu shakka, matasa za su iya koyan darussa daga bangaskiyar Dauda. Ka lura cewa ya yi amfani da lokacinsa don ya kusaci Jehobah. Ƙari ga haka, ya koyi wasu abubuwa masu kyau da suka taimaka masa ya sami aiki. Mafi muhimmanci ma, ya bi ja-gorar ruhun Jehobah. Waɗannan darussa ne masu kyau da ya kamata mu koya, ko ba haka ba?​—⁠Mai-Wa’azi 12:⁠1.

‘KADA GABAN KOWA YA FAƊI SABODA SHI’

A lokacin da Dauda yake yi wa Saul hidima, yakan dawo gida a wasu lokuta na dogon lokaci don ya yi kiwon tumakin mahaifinsa. A wannan lokacin ne Jesse ya aiki Dauda ya je ya dubo ‘yan’uwansa uku da suke hidima a matsayin sojojin Saul. Dauda ya ɗauki wasu abubuwan da zai ba ‘yan’uwansa kuma ya kama tafiya zuwa Kwarin Elah. Da ya iso wurin, bai ji daɗi ba don ya sami rundunar nan biyu sun kafe kamar yadda aka ambata a farkon talifin nan. Sun tsaya suna fuskantar juna ga kwari a tsakaninsu.​—⁠1 Sama’ila 17:​1-3, 15-19.

Dauda yana ganin ba zai iya ƙyale wannan rainin ba. Ta yaya rundunar Allah mai rai, za su ji tsoron wannan mutumin da ba ya bauta wa Jehobah? Dauda yana ganin abin da Goliyat yake yi raini ne a gaban Jehobah. Sai ya soma gaya wa sojojin da gaba gaɗi cewa zai iya yaƙi Goliyat. Kafin a ce kwabo, sai ɗan’uwan Dauda, wato Eliyab ya ji abin da ƙaninsa Dauda yake faɗa. Sai ya tsauta wa ƙaninsa yana cewa ya zo ne don ya ga dumbin mutanen da za a kashe. Amma Dauda ya ce masa: “Me na yi yanzu? Ba magana kaɗai na yi ba?” Sai ya ci gaba da gaya wa mutane da gaba gaɗi cewa zai iya yaƙan Goliyat. Ana nan sai wani ya gaya wa sarki Saul. Sai sarkin ya ce a kirawo Dauda.​—⁠1 Sama’ila 17:​23-31.

Dauda ya zo gaban sarki kuma ya gaya masa albishiri game da Goliyat cewa: “Kada gaban kowa shi faɗi saboda shi.” Saul da mutanensa sun ɗauka cewa ba za su iya yaƙan Goliyat ba. Wataƙila sun yi tunani irin na mutumtaka cewa ba za su iya gwada kansu da wannan katon mutumin ba, da yake suna ganin tsayinsu bai kai ƙirjinsa ba ma. Suna ganin da yake wannan katon yana ɗauke da makamai, babu shakka zai yi nasara a kansu. Amma Dauda bai yi wannan tunanin ba. Kamar yadda za mu gani a gaba, tunaninsa ya yi dabam da nasu. Sai ya shirya ya yi maganin Goliyat.​—⁠1 Sama’ila 17:⁠32.

Sai Saul ya ce: “Ba za ka iya yaƙi da wannan Bafiliste ba, gama kai ɗan saurayi ne, shi kuwa ya saba da yaƙi tun yana saurayi.” Da gaske ne cewa Dauda ba zai iya yaƙan Goliyat ba? A’a, amma shekarunsa ba su kai na shiga soja ba kuma daga ganinsa, za a san cewa shi yaro ne. Duk da haka, an riga an san cewa Dauda mayaƙi ne kuma a yanzu, wataƙila shekarunsa sun kusan ashirin.​—⁠1 Sama’ila 16:18; 17:​33, Littafi Mai Tsarki.

Dauda ya ƙarfafa Saul ta wurin tuna masa da abin da ya faru sa’ad da zaki da bear suka zo su cinye tumakin mahaifinsa. Shin fahariya yake yi? A’a. Dauda ya san abin da ya taimaka masa ya yi nasara a waɗannan lokutan. Shi ya sa ya ce: “Ubangiji wanda ya cece ni daga bakin zaki, da bakin bear kuma, za ya cece ni daga hannun wannan Ba-philisti.” Da Saul ya ga cewa yaƙin ya fi ƙarfinsa, sai ya ce wa Dauda: “Je ka, Ubangiji kuma za ya yi tare da kai.”​—⁠1 Sama’ila 17:⁠37.

Shin kana so ka yi koyi da bangaskiyar Dauda? Ka lura cewa bangaskiyar Dauda ba zato ba ne kawai. Ya kasance da bangaskiya bisa ga sani da kuma abubuwan da ya shaida. Ya san cewa Jehobah mai ƙauna ne da ke kāre mutane kuma yana cika alkawuransa. Idan muna son mu kasance da irin wannan bangaskiyar, zai dace mu ci gaba da koyo game da Allahn da aka ambata a Littafi Mai Tsarki. Kuma idan muka aikata abin da muke koya, za mu amfana kuma bangaskiyarmu za ta yi ƙarfi.​—Ibraniyawa 11:1.

“UBANGIJI ZA YA BASHE KA CIKIN HANNUNA”

Da farko, Saul ya so ya kure Dauda da makamansa. Makaman sun yi kama da na Goliyat da aka yi da janganci kuma wataƙila ya haɗa da rigar ƙarfe. Dauda ya saka wannan rigar kuma ya yi ƙoƙarin zagayawa, amma ya gane cewa ba zai yi masa amfanin kome ba. Da yake ba a horar da shi a matsayin soja ba, ba zai iya ɗaukan waɗannan makaman ba, musamman waɗanda Saul yake sakawa domin shi ne mutum mafi tsayi a Isra’ila baki ɗaya! (1 Sama’ila 9:⁠2) Don haka, sai ya tuɓe rigar kuma ya saka wadda ya saba kiwo da ita.​—1 Sama’ila 17:​38-40.

Dauda ya ɗauki sandar da yake kiwo da shi da majajjawa da kuma jaka a kafaɗarsa. Za a gani kamar cewa majajjawa ba ya baƙin kome, amma makami ne mai amfani sosai. Majajjawa tana da igiya biyu masu ɗan tsayi kuma makiyaya sun saba amfani da ita. Makiyayi zai saka dutse a tsakiya sai ya kada kuma ya sake igiya ɗaya don dutsen da ke ciki ya sami abin da yake fakonsa. Majajjawa tana da amfani sosai shi ya sa rundunar sojoji suke amfani da ita a wasu lokuta don yaƙi.

Da yake Dauda yana shirye, sai ya hanzarta don ya sami magabcinsa. Babu shakka, Dauda ya yi addu’a sosai a gefen kogin sa’ad da yake sunkuyawa don ya ɗebi ƙananan duwatsu biyar da zai yi amfani da su. Bayan haka, sai ya fita da gudu zuwa filin yaƙi!

Kana ganin me Goliyat ya tuna sa’ad da ya ga abokin faɗansa? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Sai ya rena shi; gama [saurayi] ne kaɗai, ja ne, mai-kyaun fuska.” Sai Goliyat ya ce wa Dauda: “Kare ne ni da za ka zo wurina da sanduna?” Wataƙila ya ga sandar amma bai san yana riƙe da majajjawa ba. Sai Goliyat ya zagi Dauda da sunan allolin Filistiyawa kuma ya ce tsuntsayen sama da dabbobi za su ci naman wannan saurayin.​—1 Sama’ila 17:​41-44.

Har wa yau, amsar da Dauda ya bayar misali ne mai kyau na bangaskiya a gare mu. Ka yi tunanin yadda matashin nan ya gaya wa Dauda cewa: “Kai kana zuwa wurina da takobi, da māshi, da kunkeli: amma ni na zo wurinka cikin sunan Ubangiji mai-runduna, Allah na rundunan yaƙi na Isra’ila, wanda ka zarge” shi. Dauda ya san cewa ikon mutum da kuma makaman yaƙi ba su da wani muhimmanci. Kuma da yake Goliyat ya raina Jehobah, babu shakka, Jehobah zai koya masa hankali. Kamar yadda Dauda ya faɗa, ‘yaƙin na Jehobah ne.’​—1 Sama’ila 17:​45-47.

Ba wai Dauda bai ga girman Goliyat da kuma makaman da yake ɗauke da su ba. Amma, bai tsorata ba. Bai taɓa yin kuskuren da Saul da rundunarsa suka yi ba. Ƙari ga haka, Dauda bai gwada kansa da Goliyat ba. A maimakon haka, ya gwada ikon Goliyat da na Jehobah. Ko da yake tsayin Goliyat ya kai kafa tara da rabi, wato mita biyu da ɗigo tara amma a gaban Maɗaukaki Jehobah, shi ba kome ba ne. Goliyat yana kamar ƙwaro ne kuma ba zai yi wa Jehobah wuya ya murje shi ba!

Sai Dauda ya matsa kusa da magabcinsa kuma ya ciro dutsen da ke cikin jakarsa. Ya saka dutse cikin majajjawa sai ya kada ta sosai. Goliyat kuma ya matso kusa da Dauda, wataƙila yana kusa da mai ɗauke da makamansa. Tsayin Goliyat illa ce a gare shi domin mai riƙe da makamansa ba zai iya kāre kan Goliyat ba saboda tsayinsa. Kuma wannan wurin da mai ɗaukan makaman Goliyat bai kai ba ne Dauda yake fako da majajjawarsa.​—⁠1 Sama’ila 17:⁠41.

Dauda ya fahimta cewa jarumi ba kome ba ne a gaban Jehobah

Dauda ya saki majajjawar kuma dutsen ya fita. Ka yi tunanin yadda ko’ina ya yi tsit sa’ad da dutsen ya bugi Goliyat. Babu shakka, Jehobah ya tabbatar da cewa dutse ɗaya da Dauda ya yi amfani da shi zai sami Goliyat, ba sai ya ƙara saka wani ba. Sai katon mutumin nan ya faɗi a ƙasa! Babu shakka, mai riƙe masa makamai ya tsere don tsoro. Dauda ya ɗauki takobin Goliyat kuma ya fille kan katon.​—1 Sama’ila 17:​48-51.

Bayan haka, sai Saul da rundunarsa suka sami gaba gaɗi. Suka soma kururuwa kuma suka nufi wajen Filistiyawa. Yaƙin ya zama daidai yadda Dauda ya gaya wa Goliyat: Jehobah ‘za ya bashe ku a cikin hannunmu.’​—⁠1 Sama’ila 17:​47, 52, 53.

A yau, bayin Jehobah ba sa yin yaƙi na zahiri domin tsohon yayi ne. (Matta 26:52) Duk da haka, muna bukata mu yi koyi da bangaskiyar Dauda. Kamar Dauda, muna bukata mu san cewa Jehobah yana wanzuwa kuma shi ne ya kamata mu bauta wa da zuciya ɗaya. Ko da yake a wasu lokuta za mu ga cewa mun kasa don yawan damuwa da muke fama da ita, amma zai dace mu tuna cewa ikon Jehobah ya fi ƙarfin matsalolinmu. Idan muka yanke shawarar bauta wa Jehobah kuma muka ba da gaskiya gare shi kamar yadda Dauda ya yi, babu ƙalubale ko matsala da za su iya tsoratar da mu. Domin babu wani abin da ya fi ƙarfin Jehobah!