Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Zai Yiwu Allah Mai Kauna Ya Kula da Kai Kuma Ya Kare Ka Har Abada

Zai Yiwu Allah Mai Kauna Ya Kula da Kai Kuma Ya Kare Ka Har Abada
  • Za ka so ka ga an daina yaƙi da cin zali da nuna ƙiyayya a duniyar nan?

  • Za ka so ka ga an daina rashin lafiya da shan wahala da kuma mutuwa?

  • Za ka so ka daina damuwa da rashin kwanciyar hankali?

  • Za ka so ka yi rayuwa a inda babu ambaliyar ruwa da muguwar guguwa da dai sauransu?

Allahnmu mai ƙauna, Wanda ya halicci duniyar nan, ya yi alkawari cewa zai sa mutane su yi rayuwa har abada cikin salama da kuma farin ciki. Wannan ba tatsuniya ba ce.

Za mu so ka karanta talifofi na gaba don ka ga,

  • Abin da ya nuna cewa Mahaliccinmu yana ƙaunarmu

  • Abin da za mu iya koya daga rubutacciyar Kalmar Allah

  • Abubuwa masu kyau da annabawa suka ce Allah zai yi

  • Ta yaya Allah zai taimaka mana mu yi farin ciki a yanzu da kuma a nan gaba?

Bari mu bincika abubuwan da Allah ya ba mu don ya nuna cewa ya damu da mu.