Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ta Annabawan Allah Ne Za Mu Koya Game da Shi

Ta Annabawan Allah Ne Za Mu Koya Game da Shi

A dā, Allah ya yi amfani da annabawa wajen idar da saƙonni masu muhimmanci ga ’yan Adam. Me za mu iya koya game da Allah daga saƙonnin da ya turo? Bari mu ga abin da za mu iya koya daga annabawa uku masu aminci.

ANNABI IBRAHIM

Allah ba ya nuna bambanci kuma yana so ya albarkaci kowa.

Allah ya yi wa annabi Ibrahim alkawari cewa “dukan ƙabilun duniya” za su sami albarka ta wurinsa.​—Farawa 12:3.

Mene ne darasin? Allah yana ƙaunarmu sosai, kuma yana so ya saka wa dukan ƙabilu ko iyalai da suka yi masa biyayya, maza da mata, har ma da yara.

ANNABI MUSA

Allah mai jin ƙai ne kuma yana saka wa waɗanda suke ƙoƙari su san shi.

Allah maɗaukaki ya ba wa annabi Musa ikon yin mu’ujizai da yawa. Duk da haka, annabi Musa ya roƙi Allah ya ce: “Ka nuna mini hanyoyinka domin in san ka, in kuma ci gaba da samun farin jini a gare ka.” (Fitowa 33:13) Allah ya amince da roƙon da annabi Musa ya yi, kuma ya taimaka masa ya ƙara fahimtar halayensa. Alal misali, annabi Musa ya gane cewa Mahaliccinmu “Allah mai jin ƙai ne, mai alheri.”​—Fitowa 34:​6, 7.

Mene ne darasin? Allah yana so ya saka wa dukanmu ko da mu maza ne ko mata ko yara, idan muka ƙoƙarta don mu san gaskiya game da shi. A cikin Nassosi Masu Tsarki, Allah ya bayyana mana yadda ya dace mu bauta masa, kuma ya nuna mana cewa yana so ya saka mana da albarka.

YESU (ANNABI ISAH)

Almasihu ya tausaya wa marasa lafiya kuma ya warkar da su

Idan muka koya game da Yesu Almasihu, muka bincika koyarwarsa, da kuma abubuwan da ya yi, hakan zai taimaka mana mu sami rai na har abada.

An yi bayani sosai a kan rayuwar Yesu Almasihu da kuma koyarwarsa a cikin Nassosi Masu Tsarki. Allah ya ba Almasihu ikon yin mu’ujizai, ya warkar da makafi, da kurame, da guragu, har ma ya ta da waɗanda suka mutu. Mu’ujizan nan da Almasihu ya yi sun nuna irin albarkun da Allah zai yi wa ’yan Adam a nan gaba. Ƙari ga haka, Almasihu ya faɗi abin da kowannenmu zai iya yi don ya sami albarkun nan. Ya ce: “Rai na har abada kuwa shi ne, mutane su san ka, kai da kake Allah makaɗaici na gaskiya, su kuma san Yesu Almasihu wanda ka aiko.”​—Yohanna 17:3.

Yesu Almasihu mai tausayi ne da kuma alheri. Yara da manya, maza da mata sun yi ta binsa don shi da kansa ya ce: “Ku . . . koya daga wurina, domin ni mai tawali’u ne, mai sauƙin kai, kuma za ku sami hutu a zuciyarku.” (Matiyu 11:29) Ko da yake mutane a zamaninsa suna wulaƙanta mata, Almasihu ya damu da mata, ya kyautata musu, kuma ya daraja su.

Mene ne darasin? Almasihu ya ƙaunaci mutane, kuma ya koya mana yadda ya kamata mu mutunta juna.

YESU ALMASIHU BA ALLAH BA NE

Nassosi Masu Tsarki sun ce, “mu dai a gare mu kam, Allah ɗaya ne,” kuma sun nuna cewa Allah ne ya aiko Yesu Almasihu. (1 Korintiyawa 8:6) Almasihu da kansa ya ce Allah ya fi shi girma, ya kuma ce Allah ne ya aiko shi duniya.​—Yohanna 11:​41, 42; 14:28. *

^ sakin layi na 17 Don samun ƙarin bayani game da Yesu Almasihu, ka duba sashe na 8 da 9 na ƙasidar nan, Cikakken Imani​—Zai Sa Ka Yi Farin Ciki a Rayuwa. Za ka iya samunsa a dandalin www.jw.org/ha.