Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Allah “mai jin addu’o’i” yana so mu gaya masa abin da ke zuciyarmu.​—ZABURA 65:2

Ku Ci Gaba da Rokon Allah Ya Yi Muku Alheri

Ku Ci Gaba da Rokon Allah Ya Yi Muku Alheri

Allah ya ba ’yan Adam wani babban gata, wato, gatan gaya masa duk abin da yake damunmu ta wajen yin addu’a. Annabi Dauda ya yi addu’a ya ce: “Ya kai mai jin addu’o’i! A gare ka ne dukan halitta za su zo.” (Zabura 65:2) Amma, ta yaya za mu yi addu’a Allah ya ji, kuma ya amsa addu’ar?

KA YI ADDU’A CIKIN LADABI KUMA KA FAƊI ABIN DA KE ZUCIYARKA

Idan kana addu’a, za ka iya faɗa wa Allah duk abin da ke zuciyarka, wato, za ka iya gaya masa ainihin yadda kake ji. (Zabura 62:8) Allah Maɗaukaki yana so mutane su riƙa addu’a daga zuciyarsu.

KA KIRA ALLAH DA SUNANSA YAYIN DA KAKE ADDU’A

Allah yana da laƙabi da yawa, kamar Mahalicci, da Mai rahama da Mai jin ƙai, amma sunansa ɗaya ne. Allah da kansa ya ce: “Ni ne Yahweh, * sunana ke nan.” (Ishaya 42:8) An ambaci sunan Allah wajen sau 7,000 a cikin Nassosi Masu Tsarki. Annabawa da dama sun daraja sunan Allah kuma sun kira shi da sunan. Annabi Ibrahim wanda a dā Ibram ake kiransa, ya ce: “Ya Ubangiji Yahweh, ta yaya zan sani cewa lallai ƙasar za ta zama gādona?” (Farawa 15:8) Zai dace mu riƙa kiran Allah da sunansa wato, Yahweh ko Jehobah, sa’ad da muke addu’a.

ZA KA IYA YIN ADDU’A DA YARENKU

Allah ya san abin da muke tunani da yadda muke ji ko da wane yare ne muke yi. Kalmar Allah ta tabbatar mana cewa: “Allah ba ya nuna bambanci, amma yana karɓar duk mai tsoronsa da kuma mai aikata adalci a kowace al’umma.”​—Ayyukan Manzanni 10:​34, 35.

Amma ba yin addu’a ne kaɗai zai sa Allah ya albarkace mu ba. A talifofi na gaba za mu ga wasu abubuwan da ya kamata mu yi.

^ sakin layi na 6 Yahweh ko Jehobah shi ne sunan Allah a Nassosi Masu Tsarki.