Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Muna Bukatar Sabuwar Duniya!

Muna Bukatar Sabuwar Duniya!

Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya António Guterres ya ce: “Duniya tana cike da matsaloli.” Ka yarda da hakan?

Labaran duniya suna cike da abubuwa masu tā da hankali, kamar

  • Cututtuka da annoba

  • Bala’o’i

  • Talauci da yunwa

  • Gurɓata mahalli da ɗumamar yanayi

  • Aikata laifi da ta’addanci da cin hanci

  • Yaƙe-yaƙe

Lallai muna bukatar sabuwar duniya, inda za a sami

  • Ƙoshin lafiya

  • Zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali

  • Abinci a yalwace

  • Mahalli marar guba

  • Adalci don kowa

  • Salama a duk duniya

Amma me muke nufi idan muka yi maganar sabuwar duniya?

Me zai faru da duniyar da muke ciki yanzu?

Me za mu yi don mu yi rayuwa a sabuwar duniya?

Wannan fitowar Hasumiyar Tsaro tana ɗauke da amsoshin da Littafi Mai Tsarki ya bayar ga tambayoyin nan, da ma wasu.