Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Abin da Za Ka Iya Yi don Ka Shiga Sabuwar Duniya

Abin da Za Ka Iya Yi don Ka Shiga Sabuwar Duniya

Talifofin da suka gabata sun nuna mana cewa nan ba da daɗewa ba, Allah zai kawo ƙarshen wannan muguwar duniya da matsalolinta. Mun tabbata cewa hakan zai faru. Me ya sa? Domin Allah ya yi alkawari a cikin Kalmarsa wato Littafi Mai Tsarki cewa:

“Duniya . . . tana wucewa.”​—1 YOHANNA 2:17.

Muna da tabbaci cewa mutane za su tsira domin ayar da aka ambata a sama ta ƙara da cewa:

“Wanda ya aikata nufin Allah zai rayu har abada.”

Saboda haka, idan muna so mu tsira, muna bukatar mu yi nufin Allah. Amma sai mun san Allah kafin mu san nufinsa.

ZA KA TSIRA IDAN KA “SAN” ALLAH

Yesu ya ce: “Rai na har abada kuwa shi ne, mutane su san ka, kai da kake Allah makaɗaici na gaskiya.” (Yohanna 17:3) Don mu tsira wa ƙarshen duniya kuma mu rayu har abada, dole ne mu “san” Allah. Hakan ba ya nufin sanin cewa Allah yana wanzuwa ko kuma sanin waɗansu abubuwa game da shi kawai. Muna bukatar mu zama abokansa. Idan muna so abokantakarmu da wani ta yi ƙarfi, dole ne mu riƙa kasancewa da mutumin. Haka ma abokantaka da Allah take. Ka yi la’akari da wasu abubuwa da ke Littafi Mai Tsarki da za su taimaka mana mu zama aminan Allah.

KA KARANTA KALMAR ALLAH KULLUM

Za ka iya tsira wa ƙarshen wannan duniyar ta wajen yin addu’a ga Allah ya taimaka maka da kuma yin nufinsa

Muna cin abinci a kullum don mu rayu. Amma Yesu ya ce: “Ba da abinci kaɗai mutum zai rayu ba, sai dai da kowace kalmar da take fitowa daga wurin Allah.”​—Matiyu 4:4.

A yau, za mu iya karanta abin da Jehobah ya faɗa a cikin Littafi Mai Tsarki. Idan ka karanta Littafi Mai Tsarki, za ka san abin da Allah ya yi a dā, da abin da yake yi a yanzu, da kuma abin da zai yi a nan gaba.

KA ROƘI ALLAH YA TAIMAKA MAKA

Me za ka yi idan kana so ka bi abin da Allah ya faɗa, amma yana yi maka wuya ka daina yin abin da ya haramta? Sanin Allah sosai zai taimaka maka.

Ka yi la’akari da misalin wata mata da a dā ta yi fasiƙanci sosai da za mu kira ta Sakura. Sa’ad da ta soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki, ta koyi umurnin Allah cewa mu “guje wa halin lalata!” (1 Korintiyawa 6:18) Sakura ta yi addu’a ga Jehobah ya taimaka mata, kuma ta daina wannan halin. Amma bai yi mata sauƙi ta daina ba. Ta ce: “Idan na soma tunanin banza, ina addu’a ga Jehobah kuma in gaya masa dukan abin da ke zuciyata, domin na san cewa ba zan iya daina wannan halin da kaina ba. Yin addu’a ya sa na daɗa kusantar Jehobah.” Kamar yadda Sakura ta yi, miliyoyin mutane suna koya game da Jehobah. Jehobah yana ba su ƙarfin da suke bukata don su yi canje-canje a rayuwarsu kuma su soma yin irin rayuwar da yake so.​—2 Korintiyawa 4:7.

Yayin da kake daɗa sanin Allah, shi ma zai “san” da kai a matsayin amininsa. (Galatiyawa 4:9; Zabura 25:14) Hakan zai sa ka cancanci shiga sabuwar duniya. Amma yaya sabuwar duniyar nan za ta zama? Za a bayyana hakan a talifi na gaba.

^ sakin layi na 15 Jehobah ko Yahweh shi ne sunan Allah a Littafi Mai Tsarki.