Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 17

Jehobah Yana Taimaka Mana Mu Yi Tsayayya da Mugayen Ruhohi

Jehobah Yana Taimaka Mana Mu Yi Tsayayya da Mugayen Ruhohi

Muna “kokawa . . . da mugayen ruhohi ne na sammai.”​—AFIS. 6:12.

WAƘA TA 55 Kada Ku Ji Tsoron Su!

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Kamar yadda aka bayyana a Afisawa 6:​10-13, a wace hanya ta musamman ce Jehobah yake nuna ya damu da mu? Ka bayyana.

HANYA ta musamman da Jehobah yake nuna ya damu da mu ita ce ta wajen taimaka mana mu yi tsayayya da abokan gābanmu. Ainihin maƙiyanmu su ne Shaiɗan da aljanunsa. Jehobah ya yi mana gargaɗi game da waɗannan abokan gāba, kuma ya taimaka mana don mu iya yin tsayayya da su. (Karanta Afisawa 6:​10-13.) Za mu yi nasarar yin tsayayya da Iblis idan muka amince da taimakon Jehobah kuma muka dogara gare shi. Ya kamata mu kasance da gaba gaɗi kamar manzo Bulus da ya ce: “Idan Allah yana tare da mu, wa ya isa ya yi gāba da mu?”​—Rom. 8:31.

2. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

2 A matsayinmu na Kiristoci, bai kamata mu mai da hankali ainun ga Shaiɗan da aljanunsa ba. Amma ya kamata mu fi mai da hankali ga bauta wa Jehobah da kuma koya game da shi. (Zab. 25:5) Saboda haka, ya kamata mu san ainihin abubuwan da Shaiɗan yake yi. Me ya sa? Don kada ya ruɗe mu. (2 Kor. 2:11) A wannan talifin, za mu tattauna hanya ta musamman da Shaiɗan da aljanunsa suke ƙoƙari su yaudari mutane. Ban da haka, za mu bincika yadda za mu yi tsayayya da su.

YADDA MUGAYEN RUHOHI SUKE RUƊAN MUTANE

3-4. (a) Mene ne sihiri? (b) Mutanen da suka yi imani da sihiri suna da yawa kuwa? Ka bayyana.

3 Sihiri ne hanya ta musamman da Shaiɗan da aljanu suke yin amfani da ita don su yaudari mutane. Waɗanda suke sihiri suna da’awa sun san abubuwan da mutane ba su sani ba. Alal misali, wasu sun ce za su iya sanin abin da zai faru a nan gaba ta wajen yin duba ko kuma bokanci. Wasu kuma suna yi kamar suna magana da matattu. Ƙari ga haka, wasu suna maita ko tsafi, kuma su yi ƙoƙarin yi wa mutum asiri. *

4 Mutanen da suka yi imani da sihiri suna da yawa kuwa? Wani bincike da aka yi a ƙasashe 18 da ke Amirka ta Tsakiya da kuma Karibiya ya nuna cewa aƙalla mutum ɗaya cikin uku na mutanen da aka gana da su sun yi imani da tsafi ko maita ko kuma bokanci. Kuma da yawa cikinsu sun yi imani cewa za a iya yin sha’ani da ruhohi. An yi wani bincike kuma a ƙasashen Afirka guda 18, kuma an gano cewa mutane fiye da rabi da aka gana da su sun yi imani da maita. Hakika, ko a ina ne muke da zama, wajibi ne mu guji sihiri. Ballantana ma, Shaiɗan yana neman “ya ruɗi dukan duniya.”​—R. Yar. 12:9.

5. Mene ne ra’ayin Jehobah game da sihiri?

5 Jehobah Allah ne “mai aminci.” (Zab. 31:5) Saboda haka, mene ne ra’ayinsa game da sihiri? Ya tsani sihiri! Jehobah ya gaya wa Isra’ilawa cewa: “Ba za a sami waninku da zai miƙa ɗansa ko ’yarsa hadaya ta ƙonawa ba, ko kuwa ya zama mai duba, ko mai maita, ko mai dabo, ko mai sihiri, ko boka, ko mai sha’ani da ruhohi, ko mai haɗa kai da ruhohin matattu ba. Gama duk wanda ya aikata waɗannan abubuwa ya zama abin ƙyama ne ga Yahweh.” (M. Sha. 18:​10-12) Kiristoci ba sa bin Dokar da Jehobah ya ba Isra’ilawa. Amma, mun san cewa ra’ayin Jehobah game da sihiri bai canja.​—Mal. 3:6.

6. (a) Ta yaya Shaiɗan yake amfani da sihiri don ya ruɗi mutane? (b) Kamar yadda Mai-Wa’azi 9:5 ta nuna, mene ne gaskiya game da yanayin mattatu?

6 Jehobah yana yi mana gargaɗi game da sihiri domin ya san cewa Shaiɗan yana amfani da shi don ya ruɗi mutane. Shaiɗan yana amfani da sihiri don ya yaɗa ƙaryace-ƙaryace, har da ƙarya cewa matattu suna lahira. (Karanta Mai-Wa’azi 9:5.) Ƙari ga haka, Shaiɗan yana amfani da sihiri don ya sa mutane su riƙa jin tsoro kuma su bijire daga bin Jehobah. Yana son waɗanda suke yin sihiri su dogara ga mugayen ruhohi maimakon Jehobah.

YADDA ZA MU YI TSAYAYYA DA MUGAYEN RUHOHI

7. Mene ne Jehobah ya gaya mana?

7 Kamar yadda aka ambata ɗazu, Jehobah yana gaya mana abin da ya kamata mu sani domin kada Shaiɗan da aljanunsa su ruɗe mu. Za mu tattauna wasu matakan da za mu iya ɗauka don mu yi tsayayya da Shaiɗan da aljanunsa.

8. (a) A wace hanya ta musamman ce za mu iya yin tsayayya da mugayen ruhohi? (b) Ta yaya Zabura 146:4 ta fallasa ƙaryar Shaiɗan game da yanayin matattu?

8 Ka karanta Kalmar Allah kuma ka yi bimbini a kai. Wannan hanya ce ta musamman da muke ƙin ƙaryace-ƙaryacen da mugayen ruhohi suke yi. Kalmar Allah tana kamar takobi mai kaifi da ke fallasa ƙaryace-ƙaryacen Shaiɗan. (Afis. 6:17) Alal misali, Kalmar Allah tana fallasa ƙarya cewa matattu za su iya yin sha’ani da mutane. (Karanta Zabura 146:4.) Ta kuma tuna mana cewa Jehobah ne kawai zai iya faɗin abin da zai faru a nan gaba. (Isha. 45:21; 46:10) Idan muna karanta Kalmar Allah da kuma yin bimbini a kai a kai, za mu kasance a shirye mu ƙi ƙaryace-ƙaryacen da mugayen ruhohi suke so mu yi imani da su.

9. Waɗanne irin ayyuka da suke da alaƙa da sihiri ne ya kamata mu guje wa?

9 Ka guji saka hannu a kome da yake da alaƙa da sihiri. Da yake mu Kiristoci ne na gaske, ba za mu taɓa yin sihiri ba. Alal misali, ba ma zuwa wurin boka ko kuma mu yi sha’ani da matattu. Kamar yadda muka tattauna a talifin da ya gabata, ba ma saka hannu a al’adun jana’iza da ke ɗaukaka koyarwa cewa matattu suna lahira. Kuma ba ma yin bokanci ko kuma duba don mu san abin da zai faru a nan gaba. (Isha. 8:19) Mun san cewa dukan waɗannan ayyuka suna da lahani sosai kuma suna iya sa mu soma sha’ani da Shaiɗan da aljanu.

Ka bi misalin Kiristoci na farko ta wajen kawar da dukan abubuwan da suke da alaƙa da sihiri kuma ka guji yin nishaɗin sihiri (Ka duba sakin layi na 10-12)

10-11. (a) Mene ne wasu a ƙarni na farko suka yi sa’ad da suka koyi gaskiya? (b) Kamar yadda 1 Korintiyawa 10:21 ta nuna, me ya sa za mu bi misalin Kiristoci a ƙarni na farko, kuma ta yaya za mu iya yin hakan?

10 Ka kawar da abubuwan da suke da alaƙa da sihiri. Wasu mutane da suke zama a Afisa a ƙarni na farko sun saka hannu a sihiri. Amma sun ɗauki mataki nan da nan sa’ad da suka koyi gaskiya. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mutane da yawa kuwa masu yin sihiri, suka tattaro littattafansu suka ƙone su a gaban jama’a duka.” (A. M. 19:19) Waɗannan mutane sun yi iya ƙoƙarinsu don su yi tsayayya da mugayen ruhohi. Waɗannan littattafan suna da tsada sosai. Amma sun halaka littattafan maimakon su ba wasu ko kuma su sayar. Sun fi son faranta wa Jehobah rai maimakon kuɗin da suka kashe wajen sayan littattafan nan.

11 Ta yaya za mu iya bin misalin waɗannan Kiristoci na ƙarni na farko? Zai dace mu kawar da duk abin da muke da shi da ke da alaƙa da sihiri. Hakan ya ƙunshi layu ko kuma wasu abubuwa da mutane suke sakawa don su kāre kansu daga mugayen ruhohi.​—Karanta 1 Korintiyawa 10:21.

12. Waɗanne tambayoyi ya kamata mu yi wa kanmu game da nishaɗi?

12 Ka yi hankali da irin nishaɗin da kake yi. Ka tambayi kanka: ‘Ina karanta littattafai ko jaridu ko kuma wasu talifofi a Intane game da sihiri? Waɗanne irin waƙoƙi nake ji, kuma wane irin fina-finai da shirye-shiryen talabijin nake kallo? Waɗanne irin wasannin bidiyo nake yi? Nishaɗin da nake yi yana da alaƙa da sihiri ne? Ina kallon shirye-shiryen da ake nuna fatalwa ko kuma dodonni? A nishaɗin da nake yi, ana nuna cewa bokanci ko yi wa mutane tsafi ba laifi ba ne?’ Hakika, ba dukan shirye-shiryen da ake nuna abubuwan da ba za su iya faruwa ba ne suke da alaƙa da sihiri ba. Sa’ad da kake bincika nishaɗi da kake yi, ka ƙuduri niyyar yin zaɓin da zai taimaka maka ka guji duk abin da Jehobah ya tsana. Ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu don mu ‘kasance ba mu da shakka ko wani abin damuwa’ a gaban Allah.​—A. M. 24:16. *

13. Mene ne ya kamata mu guji yi?

13 Ka guji ba da labarai game da aljanu. Ya kamata mu bi misalin Yesu a wannan batun. (1 Bit. 2:21) Kafin Yesu ya zo duniya, yana sama kuma ya san abubuwa da yawa game da Shaiɗan da aljanunsa. Amma bai ba da labaran abubuwan da waɗannan mugayen ruhohi suka yi ba. Yesu ya so ya yi wa mutane wa’azi game da Jehobah ba Shaiɗan ba. Muna yin koyi da Yesu idan ba ma yaɗa labarai game da aljanu. Maimakon haka, muna nuna ta furucinmu cewa zuciyarmu tana cike da “kyawawan kalmomi,” wato gaskiya.​—Zab. 45:1.

Ba ma bukatar mu ji tsoron mugayen ruhohi. Jehobah da Yesu da mala’iku sun fi su ƙarfi sosai (Ka duba sakin layi na 14-15) *

14-15. (a) Me ya sa bai kamata mu ji tsoron mugayen ruhohi ba? (b) Mene ne ya nuna cewa Jehobah yana kāre mutanensa a yau?

14 Kada ka ji tsoron mugayen ruhohi. Mukan fuskanci matsaloli a wannan duniya kamar hatsari ko rashin lafiya ko kuma mutuwa. Waɗannan abubuwa suna iya faruwa farat ɗaya. Amma bai kamata mu riƙa tunani cewa mugayen ruhohi ne suka jawo mana waɗannan matsalolin ba. Littafi Mai Tsarki ya ce “sa’a” da tsautsayi sukan shafi kowannenmu. (M. Wa. 9:11) Jehobah ya nuna cewa ya fi aljanu ƙarfi. Alal misali, bai bar Shaiɗan ya kashe Ayuba ba. (Ayu. 2:6) A zamanin Musa, Jehobah ya nuna ya fi ƙarfin masu tsafi na Fir’auna a Masar. (Fit. 8:18; 9:11) Bayan haka, Jehobah ya ba Yesu ikon jefo Shaiɗan da aljanunsa daga sama zuwa duniya. Kuma a nan gaba, za a jefa su cikin rami marar matuƙa don kada su cutar da kowa.​—R. Yar. 12:9; 20:​2, 3.

15 A yau, muna ganin tabbaci cewa Jehobah yana kāre mutanensa. Alal misali, muna wa’azi da koyarwar a duk faɗin duniya. (Mat. 28:​19, 20) Ta yin hakan, muna fallasa mugayen ayyukan Iblis. Kuma da a ce Shaiɗan yana da ikon sa mu daina aikin da muke yi, da ya yi hakan. Amma ba zai iya ba. Saboda haka, bai kamata mu ji tsoron mugayen ruhohi ba domin “idanun Yahweh suna kai da kawowa ko’ina a duniya domin ya ƙarfafa waɗanda suka dogara gare shi da zuciya ɗaya.” (2 Tar. 16:9) Idan mun riƙe aminci ga Jehobah, aljanu ba za su iya jawo mana illa na dindindin ba.

JEHOBAH ZAI ALBARKACI WAƊANDA SUKA DOGARA DA SHI

16-17. Ka ba da misalin da ya nuna cewa muna bukatar gaba gaɗi don mu yi tsayayya da mugayen ruhohi.

16 Muna bukatar mu kasance da gaba gaɗi don mu yi tsayayya da mugayen ruhohi. Hakan gaskiya ne musamman sa’ad da abokai ko dangi suke tsananta mana. Amma Jehobah yana yi ma waɗanda suka kasance da gaba gaɗi albarka. Ka yi la’akari da misalin wata ’yar’uwa mai suna Erica da take da zama a Gana. Erica tana ’yar shekara 21 sa’ad da aka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da ita. Domin mahaifinta boka ne, an matsa mata ta saka hannu a wata al’ada da ta ƙunshi cin nama da aka miƙa wa allolin mahaifinta. Amma da Erica ta ƙi yin haka, sai iyalinta suka soma ganin ta rena allolin. Sun gaskata cewa allolin za su sa su soma rashin lafiya.

17 Iyalin Erica sun yi ƙoƙari su tilasta mata ta saka hannu a al’adar, amma ta ƙi yin hakan. Kuma suka kore ta daga gidan, sai ta koma zama da wasu Shaidu. Jehobah ya albarkaci Erica sa’ad da ta soma zama da Shaidu kuma suka zama kamar ’yan’uwa a gare ta. (Mar. 10:​29, 30) Ko da yake, danginta sun kore ta kuma suka ƙona kayanta, ta kasance da aminci ga Jehobah kuma ta yi baftisma. A yanzu, tana hidimar majagaba na kullum kuma ba ta tsoron aljanu. Erica ta ce game da iyalinta: “Ina addu’a kullum membobin iyalina su san cewa idan mutum ya bauta wa Jehobah zai yi farin ciki. Kuma su sami ’yanci don suna bauta wa Jehobah Allah mai ƙauna.”

18. Wace albarka za mu samu idan muka dogara ga Jehobah?

18 Ba dukanmu ba ne za mu fuskanci irin jarrabawa mai tsanani da Erica ta fuskanta ba. Amma dukanmu muna bukatar mu yi tsayayya da mugayen ruhohi kuma mu dogara ga Jehobah. Idan muka yi hakan, Jehobah zai albarkace mu sosai kuma Shaiɗan ba zai ruɗe mu da ƙaryace-ƙaryacensa ba. Ƙari ga haka, ba za mu riƙa jin tsoron aljanu ba. Ban da haka ma, dangantakarmu da Jehobah za ta yi danƙo. Almajiri Yaƙub ya ce: “Ku miƙa kanku ɗungum ga Allah. Kada ku ba Shaiɗan dama, shi kuwa zai guje muku. Ku yi kusa da Allah, shi kuwa zai yi kusa da ku.”​—Yaƙ. 4:​7, 8.

WAƘA TA 150 Mu Biɗi Allah Don Mu Sami Ceto

^ sakin layi na 5 Don Jehobah yana ƙaunar mu, ya yi mana gargaɗi game da mugayen ruhohi da kuma yadda za su iya jawo mana matsaloli. Ta yaya mugayen ruhohi suke yaudarar mutane? Waɗanne matakai za mu ɗauka don mu yi tsayayya da su? A wannan talifin, za mu tattauna yadda Jehobah yake taimaka mana don kada su rinjaye mu.

^ sakin layi na 3 MA’ANAR WASU KALMOMI: Sihiri yana nufin yin imani da abubuwan da suke da alaƙa da aljanu da kuma yin su. Hakan ya ƙunshi yin imani cewa ruhohin matattu sun tafi lahira kuma suna yin magana da masu rai, musamman ta wurin boka. Sihiri ya haɗa da yin maita da kuma duba. Kamar yadda aka yi amfani da shi a wannan talifin, tsafi yana nufin yin ayyukan da suka shafi maitanci. Ya ƙunshi yi wa mutum asiri ko kuma karya asiri. Amma hakan ba ya nufin yin alamu da hannaye don nishaɗi.

^ sakin layi na 12 Dattawa ba su da izinin kafa dokoki game da irin nishaɗin da ya dace. Maimakon haka, wajibi ne kowane Kirista ya zaɓi abin da zai karanta da shirin talabijin da zai kalla ko kuma irin wasannin da zai yi. Magidanta masu hikima sukan tabbatar da cewa nishaɗin da mambobin iyalinsu suke yi ya jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki.​—Ka duba talifin nan a jw.org® Shin Shaidun Jehobah Sun Haramta Kallon Wasu Fina-Finai ko Karanta Wasu Littattafai ko Kuma Saurarar Wasu Wakoki Ne?” ka danna GAME DA MU > TAMBAYOYIN DA AKE YAWAN YI.

^ sakin layi na 54 BAYANI A KAN HOTO: Hoton Yesu a matsayinsa na Sarki mai iko da ke ja-goranci a kan rundunar mala’iku a sama. Kursiyin Jehobah yana sama.