Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 TARIHI

Mun Sami ‘Lu’ulu’u Mai Daraja Sosai’

Mun Sami ‘Lu’ulu’u Mai Daraja Sosai’

WINSTON da Pamela (Pam) Payne suna hidima a ofishinmu da ke yankin Australasia. A matsayinsu na ma’aurata, sun fuskanci ƙalubale da yawa kamar sabawa da wata al’ada da kuma jimrewa da rasuwa. Amma duk da haka, sun ci gaba da yin hidimarsu da farin ciki kuma ba su yarda ƙaunarsu ga Jehobah da mutanensa ta yi sanyi ba. Ku saurari ganawar da muka yi da su.

Ɗan’uwa Winston, ka gaya mana yadda ka koyi gaskiya.

An haife ni a wata gonar da ke jihar Queensland a Ostareliya kuma babu ruwan iyalinmu da addini. Da yake muna nesa da mutanen garin, danginmu ne muke yawan gani. Na soma neman in san Allah sa’ad da nake wajen ɗan shekara 12. Na roƙe Allah a addu’a cewa ya taimaka mini in san gaskiya game da shi. Daga baya, na sami wani aiki a birnin Adelaide, a Kudancin Ostareliya. Sa’ad da nake ɗan shekara 21, na haɗu da Pam a lokacin da na je hutu a birnin Sydney. Pam ta gaya min game da wata ɗarikar British-Israel wadda mabiyanta suke da’awa cewa ʼyan Biritaniya sun samo asali ne daga ƙabilun Isra’ila. Sun ce su ne ƙabilu goma da ke arewacin Isra’ila da suka je zaman bauta a ƙarni na takwas kafin haihuwar Yesu. Sa’ad da na koma birnin Adelaide, ni da wani abokin aikina da ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah mun tattauna batun. Bayan mun ɗan tattauna, musamman game da abin da Shaidu suka yi imani da shi, sai na fahimci cewa na soma samun amsar addu’ar da na yi sa’ad da nake ƙarami. Na soma koyan gaskiya game da Mahaliccina da kuma Mulkinsa. Babu shakka, na sami “lu’ulu’u . . . mai daraja sosai.”​—Mat. 13:​45, 46.

’Yar’uwa Pam, wane lu’ulu’u ne kika soma nema sa’ad da kike ƙarama. Kuma yaya kika samo shi?

Na yi girma a garin Coffs Harbour, da ke jihar New South Wales kuma iyalinmu suna son addini sosai. Iyayena da kakannina sun yi imani da koyarwar ʼyan British-Israel. An koya wa ni da ƙanena da yayata da kuma  ’ya’yan kawuna cewa Allah yana goyon bayan ’yan Biritaniya. Ban gamsu da wannan koyarwar ba sosai. Sa’ad da nake ’yar shekara 14, na je coci dabam-dabam, har da cocin Angilika da Baptist da Seventh-day Adventist. Amma duk da haka, ban gamsu ba sam.

Daga baya, mun ƙaura zuwa birnin Sydney, kuma a nan ne na haɗu da Winston, sa’ad da ya zo hutu. Kamar yadda ya ambata ɗazu, tattaunawar da muka yi ne ta sa ya soma nazari da Shaidun Jehobah. Bayan haka, wasiƙun da yake yawan tura min suna ɗauke da ayoyi dabam-dabam. A gaskiya, hakan bai faranta mini rai ba. Amma daga baya, na fahimci cewa abin da yake faɗa game da Allah gaskiya ne.

A shekara ta 1962, na ƙaura zuwa Adelaide don kada ni da Winston mu yi nisa da juna. Ya riga ya yi shiri don in sauka a gidan wasu Shaidu ma’aurata, wato Thomas Sloman da matarsa Janice. Waɗannan ma’auratan sun yi hidima a tsibirin Papua New Guinea. Sun kyautata mini sosai kuma a lokacin ni ’yar shekara 18 ce. Sai na soma nazarin Littafi Mai Tsarki kuma ba da daɗewa ba, na fahimci cewa na sami gaskiya. Bayan ni da Winston mun yi aure, sai muka soma hidimomi dabam-dabam ga Jehobah. Jarrabawar da muka fuskanta ta taimaka mana mu daɗa daraja wannan lu’ulu’u da muka samo.

Ɗan’uwa, ka gaya mana game da lokacin da ka soma bauta wa Jehobah.

A. Taswirar da ke nuna wuraren da muka je sa’ad da muke hidimar kula da da’ira

B. Tambarin wasu tsibiran. A dā, ana kiran Kiribati da Tuvalu, Tsibiran Gilbert da Ellice

C. Tsibirin Funafuti da ke yankin Tuvalu yana da kyaun gaske. Ɗaya ne cikin tsibiran da muka je kafin a tura masu wa’azi a ƙasashen waje wurin

Jim kaɗan bayan mun yi aure, Jehobah ya soma buɗe mana zarafofi da yawa na yin hidimomi dabam-dabam. (1 Kor. 16:9) Ɗan’uwa Jack Porter, wanda shi ne mai kula da da’irarmu ne Jehobah ya fara yin amfani da shi wajen ƙarfafa mu. (A yau, muna hidima tare a matsayin Kwamitin da Ke Kula da Ofishin Shaidun Jehobah a Australasia.) Ɗan’uwa Jack da matarsa Roslyn sun ƙarfafa mu mu yi hidimar majagaba kuma mun ji daɗin hidimar har shekara biyar. A lokacin da nake ɗan shekara 29, an tura ni da matata yin hidimar mai kula mai ziyara a tsibiran da ke Kudancin Tekun Fasifik kuma ofishin da ke tsibirin Fiji ne ke kula da tsibiran. Tsibiran su ne tsibirin American Samoa da Samoa da Kiribati da Nauru da Niue da Tokelau da Tonga da Tuvalu da kuma Vanuatu.

A lokacin, mutane a wasu cikin waɗannan tsibiran ba sa son Shaidun Jehobah. Saboda haka, muna mai da hankali sosai sa’ad da muka je wuraren. (Mat. 10:16) Babu ʼyan’uwa da yawa a ikilisiyoyin kuma wasu ba sa iya ba mu masauƙi. Don haka, muna neman masauƙi a wurin wasu a ƙauyukan kuma suna yawan mutunta mana.

Ɗan’uwa, mun lura cewa kana son aikin fassara sosai. Me ya sa ka soma son aikin nan?

Winston yana gudanar da makarantar dattawa a tsibirin Samoa

A lokacin, ʼyan’uwan da ke tsibirin Tonga ba su da warƙoƙi da kuma ƙasidu da yawa a yarensu. Suna yin amfani da littafin nan Gaskiya Mai-bishe Zuwa Rai Madawwami na Turanci don yin nazari da mutane. Saboda haka, sa’ad da muke makarantar dattawa na mako huɗu, wasu dattawa uku da ba su iya Turanci ba sosai sun fassara littafin zuwa yaren Tonga. Matata ta taimaka wajen kofan littafin da Tafireta, sai muka tura zuwa ofishinmu da ke Amirka don su buga shi. Mun kwashi wajen mako takwas muna fassarar. Ko da yake fassarar sai-a-hankali, amma littafin ya taimaka wa ʼyan Tonga da yawa su koyi gaskiya. Ni da matata ba mafassara ba ne, amma wannan aikin ya sa mu soma son fassara.

’Yar’uwa, ta yaya rayuwa a wannan tsibirin ya bambanta da Ostareliya?

Ɗaya cikin masaukin da muka zauna sa’ad da muke kula da da’ira

Ya yi dabam sosai! A wasu wuraren da muka je, mun yi fama da damin sauro da zafi da hunturu da ɓeraye da rashin lafiya. A wasu lokuta kuma, muna fama da ƙarancin abinci. Duk da waɗannan ƙalubalen,  a ƙarshen hidimarmu kowace rana, muna yin farin ciki yayin da muke zaune cikin masauƙinmu wanda rumfa ne kawai da aka rufe jinka a saman. A wasu ranaku daddare, wata na yin haske sosai har muna ganin itatuwan kwakwa. Abubuwan nan sun sa mun sami zarafin yin bimbini da addu’a da kuma tunanin kirki.

Muna kuma son ƙananan yara masu ban dariya da suke yawan mamaki sa’ad da suka ga turawa. Akwai wata rana da muka je tsibirin Niue, sai wani ƙaramin yaro ya zo ya taɓa gashin hannun maigidana, ya ce: “Gaskiya ina son gashinka.” Babu shakka, yaron bai taɓa ganin mutumin da ke da gashi a hannu haka ba!

Irin talaucin da mutane da yawa a tsibiran suke fama da shi ya sa mu baƙin ciki sosai. Suna da mahalli mai kyau amma ba su da isashen asibitoci da kuma ruwan sha mai tsabta. Duk da yanayin nan, ʼyan’uwanmu ba su damu ba domin sun saba da yanayin. Sun gamsu domin suna zama tare a matsayin iyali, suna da wurin taro kuma suna da zarafin bauta wa Jehobah. Misalinsu ya taimaka mana mu mai da hankali a kan abubuwa mafi muhimmanci kuma mu sauƙaƙa salon rayuwarmu.

’Yar’uwa, a wasu lokuta kina dafa wa kanki abinci kuma kina ɗibar ruwa da kanki. Yaya kike yin hakan?

Pam tana wanki a tsibirin Tonga

A gaskiya, ina godiya don yadda mahaifina ya rene ni. Ya koya mini abubuwa da yawa kamar yin dahuwa da murhu da kuma yin maneji. Akwai wani lokaci da muka ziyarci tsibirin Kiribati, mun zauna a wani ƙaramin gida da aka gina da kara, aka yi daben da ma’adanai da ke ƙasan teku kuma an rufe jinka a saman. Idan ina so in dafa abinci, ina haƙa rami a ƙasa, sai in zuba ɓawon kwakwa a ciki, sa’an nan in cinna wa ɓawon kwakwar wuta. Idan ina son ruwa, ina zuwa rijiyar da saura mata a ƙauyen suke zuwa. Matan suna yin amfani da guga don su ɗebi ruwa a rijiyar kuma suna yin hakan bi-da-bi. Kowace mace tana zuwa ta saka gugar cikin rijiyar, sai ta fitar da gugar cike da ruwa. Ban san cewa yin hakan ba wasan yara ba ne, sai da aka zo kaina. Na saka gugar sau da yawa, amma ko ɗigon ruwa bai shiga gugar ba! Matan suna ta sheƙa dariya, da suka gama, sai ɗaya cikinsu ta taimaka mini. Mutanen suna da kirki da kuma ban taimako sosai.

Mun lura cewa kun saba da zama a tsibirin. Ku gaya mana wasu abubuwa na musamman da kuka shaida?

Winston: Mun ɗan jima kaɗan kafin mu saba da al’adar mutanen yankin. Alal misali, ʼyan’uwan suna yawan ba mu dukan abincin da suka dafa. Da farko, mukan cinye abincin domin ba mu san cewa ya kamata mu ɗebi namu, kuma mu ba su sauran ba! Amma da muka sani, mun daina cinye abincin. ʼYan’uwan ba su yi fushi ba duk da kurakuren da muka yi. Suna murnar ganin mu bayan wajen wata shida sa’ad da muka kawo musu ziyara. Mu kaɗai ne Shaidu daga wata ƙasa da mutanen suka taɓa gani a lokacin.

Winston yana wa’azi da wasu ʼyan’uwa a tsibirin Niue

Ziyararmu ta shafi mazaunan tsibiran ma. A dā, mutane da yawa a tsibirin suna tsammani cewa Shaidun da ke wurin ne suka ɓaro addinin. Saboda haka, sa’ad da muka ziyarci ʼyan’uwan, mazaunan tsibiran sun san cewa akwai Shaidun Jehobah a faɗin duniya.

Pam: Wani abu da ba zan taɓa mantawa ba shi ne abin da ya taɓa faruwa sa’ad da muka je tsibirin Kiribati. ʼYan’uwa ƙalilan ne kawai a tsibirin. Wani ɗan’uwa mai suna Itinikai Matera ne kaɗai dattijo kuma yana iya ƙoƙarinsa don ya kula da mu. Akwai wata rana da ya zo wurinmu riƙe da kwando kuma ya saka ƙwan kaza guda ɗaya a ciki. Sai ya ce: “Ga shi naku ne.” A lokacin, cin ƙwai abinci ne na musamman. Wannan karimcin da ɗan’uwan ya yi mana ya sosa zuciyarmu sosai.

 ’Yar’uwa, da akwai lokacin da cikinki ya ɓare. Mene ne ya taimaka miki ki jimre da rashin?

Na yi juna biyu a shekara ta 1973 sa’ad da muke Kudancin Tekun Fasifik. Da hakan ya faru, muka koma ƙasar Ostareliya kuma bayan wata huɗu, sai cikin ya ɓare. Wannan rashin ya sa maigidana baƙin ciki sosai. Ban gama warwarewa ba sai lokacin da aka wallafa Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Afrilu, 2009. An yi tambayar nan a “Tambayoyi Daga Masu Karatu” da ke mujallar: “Akwai begen tashi daga matattu ga jaririn da ya mutu a cikin mahaifar mamar shi?” A talifin, an tabbatar mana da cewa Jehobah, wanda yake yin abin da ya dace a kowane lokaci ne ya san yadda zai bi da batun. Zai warkar da takaicin da rayuwa a wannan mugun zamani ya jawo mana sa’ad da ya ja-goranci Ɗansa ya “halaka ayyukan Shaiɗan.” (1 Yoh. 3:8) Talifin ya kuma taimaka mana mu daraja gatan da muke da shi a matsayin bayin Jehobah! In ba don Jehobah ya yi mana tanadin Mulkinsa ba, da mun shiga uku mun lalace.

Bayan wannan aukuwar, sai muka sake soma hidima ta cikakken lokaci. Mun yi hidima na ʼyan watanni a ofishinmu da ke Ostareliya. Bayan haka, sai muka sake soma hidimar mai kula mai ziyara. A shekara ta 1981, bayan mun yi shekara huɗu muna hidima a karkarar da ke New South Wales da Sydney, sai aka sake gayyatar mu zuwa ofishinmu da ke Ostareliya (a yau ana kiran sa Australasia). A wurin ne muke hidima har yanzu.

Ɗan’uwa Winston, hidimar da ka yi a Kudancin tekun Fasifik ta taimaka maka a hidimar da kake yi yanzu a matsayin memban Kwamitin da Ke Kula da Ofishin Shaidun Jehobah a Australasia kuwa?

Ƙwarai kuwa, a hanyoyi da yawa. Na farko, an ce ƙasarmu ta kula da ayyukan da ake yi a American Samoa da Samoa. Bayan haka, sai aka haɗa ofishinmu da na New Zealand. A yau, ofisoshin nan ne suke ƙarƙashin Australasia: Ostareliya da American Samoa da Samoa da Tsibiran Cook da New Zealand da Niue da Timor-Leste da Tokelau da kuma Tonga. Na taɓa kai ziyarar ƙarfafawa da yawa zuwa ofisoshin nan. Hidimar da na yi a waɗannan tsibiran ta taimaka mini sosai domin a yau, ofishinmu ne yake kula da hidimarsu.

Winston da matata a ofishin Australasia

Daɗin daɗawa, mun koya daga abin da ya faru da mu cewa ba manya kaɗai ba ne suke neman su san Allah ba. Yara ma suna son su sami ‘lu’ulu’u mai daraja sosai’ ko da danginsu ba sa so. (2 Sar. 5:​2, 3; 2 Tar. 34:​1-3) Babu shakka, Jehobah Allah ne mai ƙauna da ke son kowane mutum, wato yara da manya su sami rai na har abada!

A lokacin da ni da matata Pam muka soma nazari a sama da shekaru 50 da suka shige, ba mu san cewa haka sakamakon zai kasance ba. Hakika, gaskiya game da Mulkin Allah lu’ulu’u ce mai darajar gaske! Mun ƙuduri niyyar riƙe wannan lu’ulu’un da hannu biyu-biyu!