Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 55

Kada Ku Ji Tsoron Su!

Kada Ku Ji Tsoron Su!

(Matta 10:28)

 1. 1. Ku ci gaba, Ya bayina,

  Ku yi wa’azin Mulkin.

  Kada ku ji tsoron su.

  Ku gaya wa mutane

  Cewa Ɗana, Yesu Kristi,

  Ya yi yaƙi da Shaiɗan,

  Kuma za ya halaka shi,

  Sa’an nan za mu huta.

  (AMSHI)

  Kar ku ji tsoro bayina,

  Ko sun yi barazana.

  Zan kiyaye duk bayina

  Kamar ƙwayar idona.

 2. 2. Ko da maƙiya sun dāge

  Suna hamayya da ku,

  Ko da sun yi murmushi,

  Domin su yaudare ku.

  Ba zan yi watsi da ku ba,

  Kada ku ji tsoron su.

  Don zan kāre mai aminci

  A yaƙin Armageddon.

  (AMSHI)

  Kar ku ji tsoro bayina,

  Ko sun yi barazana.

  Zan kiyaye duk bayina

  Kamar ƙwayar idona.

 3. 3. Ba zan yi watsi da ku ba,

  Ni ne Madogararku.

  Ko da kun rasa ranku,

  Zan iya tayar da ku.

  Kar ku ji tsoron ʼyan Adam

  Don ni ne Mahalicci.

  In kuka riƙe aminci

  Zan yi maku albarka!

  (AMSHI)

  Kar ku ji tsoro bayina,

  Ko sun yi barazana.

  Zan kiyaye duk bayina

  Kamar ƙwayar idona.

(Ka kuma duba K. Sha. 32:10; Neh. 4:14; Zab. 59:1; 83:​2, 3.)