Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Dutsen laka da ke ɗauke da sunan Belshazzar (Ainihin girman dutsen)

Ka Sani?

Ka Sani?

Ta yaya masu tone-tonen ƙasa suka tabbatar da cewa Belshazzar sarkin Babila ne?

SHEKARU da yawa, masu sūkar Littafi Mai Tsarki sun ce Sarki Belshazzar da aka ambata a littafin Daniyel bai taɓa wanzuwa ba. (Dan. 5:1) Sun gaskata da hakan domin masu tonon ƙasa ba su samo abin da ya nuna cewa Belshazzar ya taɓa rayuwa ba. Amma wannan ra’ayin ya canja a shekara ta 1854. Me ya sa?

A shekarar, wani jakadar Birtaniya mai suna J. G. Taylor ya yi bincike a kangon birnin Ur ta dā, da yanzu yake kudancin Iraƙi. A kusa da wata babbar hasumiya, ya ga duwatsun laka da yawa. Kowannensu na da tsayin misalin inci 4, kuma an yi rubutu a jikinsu. Ɗayan dutsen na ɗauke da wata addu’a da aka yi cewa Allah ya ja zamanin Sarki Nabonidus na Babila da ɗansa na fari mai suna Belshazzar. Masu sūka ba su yi mūsu ba: Wannan abin da aka tono ya nuna cewa Belshazzar ya taɓa rayuwa.

Amma masu sūkar ba su yarda cewa Belshazzar sarki ne ko da Littafi Mai Tsarki ya nuna hakan. Alal misali, wani masani a ƙarni na 19 mai suna William Talbot ya rubuta cewa wasu sun ce “Bel-sar-ussur, wato Belshazzar ya yi sarauta a lokaci ɗaya da babansa Nabonidus. Amma babu abin da ya tabbatar cewa hakan gaskiya ne.”

An tabbatar cewa Belshazzar sarki ne sa’ad da wasu rubuce-rubuce da ke jikin duwatsun laka suka nuna cewa akwai lokacin da Sarki Nabonidus, wato baban Belshazzar ya yi tafiya na shekaru da yawa. Wane ne ya yi mulki sa’ad da ya yi tafiyar? Kundin nan Encyclopædia Britannica ya ce: “Ya ɗanka wa Belshazzar yawancin sojojinsa da kuma karagar mulkin.” Ta hakan Belshazzar ya zama sarki a Babila a lokacin. Shi ya sa wani masani mai suna Alan Millard ya ce ya dace da “Littafin Daniyel ya kira Belshazzar ‘sarki.’”

Hakika, bayin Allah sun san cewa Littafi Mai Tsarki ne ya fi tabbatar da cewa abin da ke littafin Daniyel gaskiya ne kuma hurarre ne daga Allah.​—2 Tim. 3:16.