Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 TARIHI

Na Sami Albarka Don Na Yi Koyi da Abokan Kirki

Na Sami Albarka Don Na Yi Koyi da Abokan Kirki

YA YI mini wuya sosai in yi wa’azi sa’ad da nake matashi. Sa’ad da na yi girma, an ba ni ayyukan da nake gani ban zan iya yi ba. Bari in gaya muku wasu abokan kirki da suka taimaka mini in daina jin tsoro yin wa’azi kuma hakan ya sa in ji daɗin yin hidima ta cikakken lokaci har shekaru 58.

An haife ni a yankin da ake Farasanci a ƙasar Kanada da ake kira Quebec City, a lardin Quebec. Iyayena Louis da Zélia masu kirki ne kuma sun ƙaunace ni. Mahaifina ba ya yawan magana amma yana son karatu. Ina jin daɗin yin rubutu kuma na sa rai cewa wata rana zan zama ɗan jarida.

Sa’ad da nake ɗan shekara 12, wani abokin aikin babanmu mai suna Rodolphe Soucy da abokinsa sun ziyarce mu. Su Shaidun Jehobah ne. Ban san Shaidu sosai ba kuma ba na son in koya game da addininsu. Duk da haka, yadda suke amsa tambayoyi da Littafi Mai Tsarki ya burge ni. Hakan ya sa iyayena ma sun so su. Shi ya sa muka yarda su soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mu.

A lokacin, ina zuwa makarantar ’yan Katolika. A wasu lokatai, nakan tattaunawa da ’yan ajinmu game da abin da nake koya. Daga baya, malamanmu firistoci sun ji cewa ina tattaunawa da ’yan ajinmu. Maimakon su yi amfani da Littafi Mai Tsarki don su ƙaryata abin da nake faɗa, wani a cikinsu ya faɗa a gaban dukan ajinmu cewa ni ɗan tawaye ne! Ko da yake wannan yanayin ya jawo matsala, hakan ya kawo sakamako mai kyau. Ta yaya? Domin hakan ya taimaka mini in ga cewa abin da ake koyarwa a makarantar bai jitu da koyarwar Littafi Mai Tsarki ba. Sai na ga cewa ya kamata in bar makarantar. Iyayena sun taimaka mini in koma wata makaranta.

YADDA NA SOMA JIN DAƊIN WA’AZI

Na ci gaba da nazarin Littafi Mai Tsarki, amma ban sami ci gaba ba domin ina jin tsoron yin wa’azi gida-gida. Cocin Katolika  tana da iko sosai kuma tana adawa da wa’azin da muke yi. Wani shugaban ’yan siyasa mai suna Maurice Duplessis yana goyon bayan cocin. Da taimakonsa, taron ’yan iska sukan kai wa Shaidu hari. Don haka, muna bukatar ƙarfin zuciya kafin mu fita wa’azi a wannan lokacin.

Wani ɗan’uwa da ya taimaka min in daina jin tsoro shi ne John Rae da ya sauke karatu a aji na tara a Makarantar Gilead. John ya ƙware a wa’azi kuma shi mai sauƙin kai ne. Ban da haka, yana wa mutane sauƙi su gaya masa abin da ke damunsu. Ba ya saurin yi mini gargaɗi kuma na koyi abubuwa da yawa daga wurinsa. John bai iya Farasanci sosai ba. Saboda haka, nakan fita wa’azi da shi a kai a kai don in taimaka masa. Yin cuɗanya da John ya taimaka min in tsai da shawarar zama Mashaidin Jehobah. Na yi baftisma a ranar 26 ga Mayu, 1951, wato bayan shekara goma da na fara haɗuwa da Shaidu.

Misali mai kyau na Ɗan’uwa John Rae (A) ya taimaka mini (B) in daina jin tsoron yin wa’azi gida-gida

Yawancin masu shela a ƙaramar ikilisiyarmu da ke Quebec City suna hidimar majagaba. Yin cuɗanya da su ya sa na soma hidimar majagaba. A lokacin, muna wa’azi gida-gida ta yin amfani da Littafi Mai Tsarki kaɗai. Tun da yake ba ma amfani da littattafai, ya dace mu yi amfani da Nassosi da kyau. Saboda haka, na yi ƙoƙari na san ayoyin Littafi Mai Tsarki da za su taimaka min in kāre imanina. Amma, mutane da yawa sun ƙi karanta Littafi Mai Tsarki da Cocin Katolika ba ta amince da shi ba.

Na auri matata Simone Patry a shekara ta 1952. Simone ’yar’uwa ce mai aminci a yankin. Sai muka ƙaura zuwa birnin Montreal kuma bayan shekara ɗaya, muka haifi ’yarmu mai suna Lise. Na daina hidimar majagaba kafin mu yi aure, duk da haka, ni da matata mun yi ƙoƙari mu sauƙaƙa salon rayuwarmu don mu riƙa saka hannu sosai a ayyukan ikilisiya.

Sai bayan shekara goma ne na soma yin tunanin sake soma hidimar majagaba. A shekara ta 1962, na halarci Makarantar Hidima ta Mulki don dattawa da aka yi na tsawon wata ɗaya a Bethel ɗin Kanada. An saka ni a ɗaki ɗaya da Ɗan’uwa Camille Ouellette. Yadda Camille yake da ƙwazo a wa’azi ya burge ni sosai, musamman da yake yana da iyali. A lokacin, da ƙyar ka ji cewa iyaye da ke renon yara suna hidimar majagaba, amma  abin da Camille yake yi ke nan. A lokacin da muke tare, ya ƙarfafa ni in yi tunani game da soma hidimar majagaba. Bayan ’yan watanni, sai na lura cewa zan iya sake soma hidimar majagaba. Wasu ’yan’uwa sun ce suna ganin hakan bai dace ba, amma na sake soma hidimar majagaba. Ina da tabbaci cewa Jehobah zai albarkace ni.

MUN KOMA QUEBEC CITY A MATSAYIN MAJAGABA NA MUSAMMAN

A shekara ta 1964, an naɗa ni da matata majagaba na musamman a garinmu Quebec City, kuma mun yi hidima shekaru da yawa a wurin. A lokacin, ba a yawan tsananta mana, amma wasu suna adawa da mu.

Wata ranar Asabar, an kama ni a Sainte-Marie, wani ƙaramin gari da ba shi da nisa daga Quebec City. Wani ɗan sanda ya kai ni ofishinsu kuma ya saka ni a bayan kanta domin ina wa’azi gida-gida ba tare da takardar izini ba. Daga baya aka kai ni gaban wani mugun alƙali mai suna Baillargeon. Sai ya tambaye ni wanda zai zama lauya na. Sa’ad da na ambata sunan Ɗan’uwa Glen How, * wani sanannen lauya Mashaidi, sai alƙalin ya ce da tsoro: “A’a, ba zai yiwu ba!” Ya faɗi hakan don a lokacin an san Ɗan’uwa Glen How da yin nasara sosai wajen kāre Shaidun Jehobah. Ba da daɗewa ba, sai kotun ta ce an wanke ni daga laifi.

Yana da wuya mu yi hayar wurin yin taro da ya dace a Quebec don yadda ake tsananta mana. Ba mu da yawa a ikilisiyarmu kuma muna taro a wani tsohon gareji mai sanyi sosai. ’Yan’uwan sun yi amfani da hita mai amfani da māi don su riƙa ɗumama wurin a lokacin da ake sanyi. Mukan taru kusa da hitar na ’yan sa’o’i kafin a soma taron don mu ba da labaransu.

Abin ban mamaki ne ganin yadda aka sami ci gaba sosai a yankin. A tsakanin shekara ta 1960 zuwa 1969, ikilisiyoyi da ke kusa da Quebec City da yankin Côte-Nord da kuma gaɓar Gaspé ba su da yawa. Amma a yanzu, akwai fiye da da’irori biyu a waɗannan wuraren, kuma ’yan’uwa suna taro a Majami’un Mulki masu kyau.

MUN SOMA HIDIMAR MAI KULA MAI ZIYARA

A 1977, na halarci taron da aka yi don masu kula masu ziyara a Toronto, Kanada

An tura ni da matata hidimar kula da da’ira a shekara ta 1970. Sa’an nan muka soma hidimar mai kula da gunduma a 1973. A lokacin, na koyi abubuwa da yawa daga ’yan’uwa da suka manyanta kamar su Ɗan’uwa Laurier Saumur * da Ɗan’uwa David Splane, * don dukansu sun yi hidimar mai kula mai ziyara. Bayan kowane taro, ni da Ɗan’uwa Splane mukan tattauna yadda za mu iya kyautata koyarwarmu. Na tuna lokacin da Ɗan’uwa Splane ya gaya mini cewa: “Léonce, na ji daɗin jawabinka na ƙarshe. Yana da kyau sosai, amma zan iya shirya jawabai uku daga wannan jawabinka!” Ya faɗi hakan ne domin ina faɗin abubuwa da yawa a jawabaina.  Ya kamata in koyi yadda zan gajarta jawabina.

Na yi hidima a birane dabam-dabam a gabashin Kanada

Masu kula da gunduma suna da hakkin ƙarfafa masu kula da da’ira. Amma, masu shela da yawa a Quebec sun san ni sosai. Sukan so su yi wa’azi tare da ni sa’ad da na ziyarce da’irarsu. Ko da yake ina jin daɗin yin wa’azi da su, ba na zama da mai kula da da’irar yadda ya kamata. Akwai lokacin da wani mai kula da da’ira ya tuna mini cewa: “Yana da kyau da kake fita wa’azi sosai da ’yan’uwan, amma ka tuna cewa ka zo nan wannan makon don ka ziyarce ni. Ni ma ina bukatar ƙarfafawa!” Irin shawarar nan ta taimaka mini sosai.

Wani abin baƙin ciki da ban yi zato ba ya faru a shekara ta 1976. Matata Simone ta soma rashin lafiya mai tsanani kuma ta rasu. Ita matar kirki ce domin ba ta sonkai kuma tana ƙaunar Jehobah sosai. Fita wa’azi a kowane lokaci ya taimaka min in jimre da mutuwarta, kuma na gode wa Jehobah don yadda ya taimaka mini a wannan mawuyacin lokaci. Daga baya, na auri Carolyn Elliott, wata majagaba mai ƙwazo da ta zo hidima a wurin da ake bukatar masu shela a Quebec kuma tana Turanci. Yana da sauƙi mutum ya yi magana da Carolyn kuma tana son mutane, musamman waɗanda suke jin kunya ko waɗanda suka kaɗaita. Ta taimaka mini sosai sa’ad da muka soma hidima tare.

WATA SHEKARA TA MUSAMMAN

A watan Janairu 1978, an ce in koyar da Makarantar Hidima ta Majagaba ta farko a Quebec. Na yi fargaba sosai domin ban taɓa halartar makarantar ba kuma ban taɓa ganin littafin da ake amfani da shi ba. Don haka, ina kamar ɗaliban domin kome sabo ne a gare ni. Na yi farin ciki domin akwai majagaba da yawa da suka ƙware a ajin. Ko da yake ni ne malaminsu, na koyi darasi daga wurinsu!

A shekara ta 1978, an yi Taron Ƙasashe mai jigo “Victorious Faith” a Filin Wasan Montreal. Wannan shi ne taro mafi girma da  aka yi a Quebec, kuma mutane 80,000 ne suka halarta. An tura ni yin aiki a Sashen Labarai. Na tattauna da ’yan jarida da yawa kuma na yi farin cikin ganin cewa sun rubuta abubuwa da yawa masu kyau game da Shaidun Jehobah. Ƙari ga haka, sun yi fiye da sa’o’i 20 suna ganawa da mu a talabijin da rediyo, kuma sun wallafa talifofi da yawa game da mu a jaridu. Hakan ya sa mutane da yawa suka san game da Jehobah!

MUN KOMA WANI YANKI

An tura ni yin hidima a wani yanki a 1996. An tura ni hidima a yankin da ake Turanci a Toronto kuma tun da na yi baftisma, wannan ne lokaci na farko da na bar yankin da ake Farasanci. Ina jin tsoron yin jawabi domin ban iya Turanci sosai ba. Na yi addu’a a kai a kai kuma na dogara ga Jehobah.

Ko da yake na ji tsoron yin wannan hidimar, amma yanzu da gaske zan ce na ji daɗin yin hidima na shekara biyu a yankin Toronto. Matata ta taimaka mini in kasance da gaba gaɗin yin Turanci, kuma ’yan’uwa sun ƙarfafa ni sosai. Ba da daɗewa ba, muka sami abokai da yawa.

Ban da ayyuka da nake yi da kuma shirye-shirye don manyan taro da ake yi a ƙarshen mako, nakan yi wa’azi gida-gida na awa guda da yamma a ranar Jumma’a. Wasu suna iya yin tunani, ‘Me ya sa yake fita wa’azi duk da yake zai shagala da aiki a manyan taro a ƙarshen mako?’ Duk da haka, na lura cewa tattaunawa da mutane yana ƙarfafa ni. Har yanzu, na fi yin farin ciki bayan na yi wa’azi.

A shekara ta 1998, an tura ni da matata yin hidimar majagaba na musamman a birnin Montreal. Na yi shekaru da yawa ina tsara yin wa’azi na musamman ga jama’a da yin aiki da ’yan jarida don na daidaita ra’ayin mutane game da Shaidun Jehobah. A yanzu, ni da matata muna farin cikin yin wa’azi ga mutane da suka ƙauro daga wata ƙasa zuwa Kanada. Sau da yawa waɗannan mutanen suna so su koyi Littafi Mai Tsarki.

Ni da matata Carolyn

Sa’ad da na yi tunani game da shekara 68 da na yi ina bauta wa Jehobah, nakan ga cewa Jehobah ya albarkace ni sosai. Na yi farin ciki domin na koyi jin daɗin yin wa’azi kuma na taimaka wa mutane da yawa su san Jehobah. ’Yata Lise da mijinta sun soma hidimar majagaba bayan da suka reni yaransu. Ganin yadda ta ci gaba da ƙwazo a hidima yana sa ni farin ciki matuƙa. Ina godiya musamman ga ’yan’uwa da suka taimaka mini in yi abota da Jehobah da kuma bauta masa a hanyoyi dabam-dabam. Sun yi hakan ta wurin sa in yi koyi da su da kuma ba ni shawarwari masu kyau. Na koya cewa za mu ci gaba da yin ayyukan da ƙungiyar Jehobah ta ba mu idan muka dogara ga Jehobah ya taimaka mana da ruhunsa. (Zab. 51:11) Na ci gaba da nuna godiya ga Jehobah domin ya ba ni gatar yabon sunansa!​—Zab. 54:6.

^ sakin layi na 16 Ka duba tarihin Ɗan’uwa Glen How a Awake ɗin 22 ga Afrilu, 2000.

^ sakin layi na 20 Ka duba tarihin Laurier Saumur a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Nuwamba, 1976 na Turanci.

^ sakin layi na 20 Ɗan’uwa David Splane memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ne.