HASUMIYAR TSARO—NA NAZARI fabrairu 2020

Wannan fitowar tana dauke da talifofin nazari da za a yi daga ranar 6 ga Afrilu–3 ga Mayu, 2020.

Jehobah Ubanmu Yana Kaunar Mu Sosai

Muna da tabbaci cewa Ubanmu na sama yana kaunar mu, yana kula da mu kuma ba zai yasar da mu ba.

Muna Kaunar Jehobah, Ubanmu Sosai

Ku yi la’akari da wasu abubuwa da za mu iya yi don mu nuna kaunarmu ga Ubanmu, Jehobah.

Ku Guji Kishi Don Ku Yi Zaman Lafiya

A wasu lokuta muna iya soma kishi. Ka ga wasu hanyoyi da za mu iya guje wa wannan hali kuma mu yi zaman lafiya da mutane.

Bari Jehobah Ya Sanyaya Zuciyarka

Hannatu da manzo Bulus da kuma Sarki Dauda sun yi alhini. Wane darasi za mu iya koya daga yadda Jehobah ya karfafa da kuma sanyaya zuciyar kowannen su?

TARIHI

Na Sami Albarka Don Na Yi Koyi da Abokan Kirki

Léonce Crépeault ya fadi yadda yin koyi da masu aminci ya taimaka masa ya daina jin tsoron yin wa’azi. Kuma ya ji dadin yin hidima ta cikakken lokaci shekaru 58.

Ka Sani?

Ta yaya masu tone-tonen kasa suka tabbatar da cewa Belshazzar sarkin Babila ne?