Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Tuna?

Ka Tuna?

Za ka iya amsa tambayoyin nan da aka ɗauko daga Hasumiyar Tsaro ta 2019?

Me ma’anar alkawarin nan: “Babu kayan yaƙin da aka ƙera domin a yaƙe ki wanda zai yi nasara”? (Isha. 54:17)

Muna da tabbaci cewa Jehobah zai kāre mu daga mugaye. (Isha. 25:​4, 5) Magabtanmu ba za su taɓa iya kawo mana illa na dindindin ba.​—w19.01, shafuffuka na 6-7.

Ta yaya yadda Allah ya bi da Kan’aniyawa da kuma Isra’ilawa masu taurin kai ya nuna adalcinsa?

Allah ya hukunta mutanen da suka saka hannu a lalata da kuma waɗanda suke cin zarafin mata da yara. Ya albarkaci mutanen da suke biyayya gare shi kuma suke mutunta mutane.​—w19.02, shafuffuka na 22-23.

Me ya kamata mu yi idan muna wurin da wani da ba Mashaidi ba yake addu’a?

Za mu iya yin shiru amma kada mu ce “amin” kuma kada mu riƙe hannu da sauran mutanen. Za mu iya yin tamu addu’a a cikin zuciyarmu.​— w19.03, shafi na 31.

Mene ne ra’ayin Jehobah game da cin zarafin yara?

Cin zarafin yara zunubi ne ga yaran da ikilisiya da hukumomi da kuma Allah. Idan hukuma ta ce a kai ƙarar mutanen da suka ci zarafin yara, dattawa suna yin biyayya da hakan.​—w19.05, shafuffuka na 9-10.

Ta yaya za mu iya canja ko kuma kyautata hankalinmu?

Matakan su ne: Yin addu’a ga Jehobah. Yin bimbini don ka bincika kanka. Zaɓan abokan kirki.​—w19.06, shafi na 11.

Ta yaya za mu iya yin shiri yanzu don tsanantawar da za mu iya fuskanta?

Muna bukatar mu ƙarfafa abotarmu da Jehobah. Ka kasance da tabbaci cewa yana ƙaunar mu kuma ba zai yasar da mu ba. Ka riƙa karanta Baibul da yin addu’a kullum. Ka tabbata cewa Allah zai kawo Mulkinsa. Ka haddace nassi da kuma waƙar da ka fi so.​—w19.07, shafuffuka na 2-4.

Mene ne za mu iya yi don mu taimaka wa danginmu su tsira?

Yana da muhimmanci mu nuna tausayi, mu kasance da hali mai kyau, mu zama masu haƙuri da basira.​—w19.08, shafuffuka na 15-17.

Ta yaya muke samun hutu kamar yadda Yesu ya ce a Matiyu 11:28?

Muna da dattawa Kiristoci masu ƙauna da abokan kirki da kuma aiki mafi kyau.​—w19.09, shafi na 23.

Ta yaya Allah zai iya ba mu ƙarfi da kuma marmari yin nufinsa? (Filib. 2:13)

Yayin da muke karanta Baibul kuma muke bimbini a kansa, Allah zai ba mu ƙarfi da marmarin yin nufinsa. Ruhunsa zai iya sa mu daɗa ƙwarewa.​—w19.10, shafi na 21.

Waɗanne matakai ne ya dace mu ɗauka kafin mu yanke muhimmiyar shawara?

Matakai biyar su ne: Ka yi bincike sosai. Ka ce Allah ya ba ka hikima. Ka bincika muradinka. Ka yanke takamaiman shawara. Ka nuna sanin yakamata.​—w19.11, shafuffuka na 27-29.

Koyarwar kurwa marar mutuwa tana da alaƙa da abin da Shaiɗan ya gaya wa Hauwa’u ne?

Da ƙyar. Shaiɗan ya gaya wa Hauwa’u cewa ba za ta mutu ba. Bai ce za ta zama kamar mutum da ya mutu ba. Babu shakka, ambaliyar zamanin Nuhu ta cire dukan addinan ƙarya. Ƙila koyarwar ta soma ne kafin Allah ya canja yaren mutanen da suka gina hasumiyar Babel.​—w19.12, shafi na 15.