Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 27

Ku Yi Shiri Yanzu Don Tsanantawa

Ku Yi Shiri Yanzu Don Tsanantawa

“Duk wanda yake so ya yi rayuwa irin hali na Allah a cikin Almasihu Yesu zai sha tsanani.”​—2 TIM. 3:12.

WAƘA TA 129 Za Mu Riƙa Jimrewa

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Me ya sa muke bukatar mu yi shiri don tsanantawar da za mu fuskanta?

A DARE na ƙarshe kafin a kashe Yesu, ya ce za a tsani dukan mutanen da suke so su zama mabiyansa. (Yoh. 17:14) Tun daga lokacin, dukan Kiristoci masu aminci sun fuskanci tsanantawa daga mutanen da ba sa son bauta ta gaskiya. (2 Tim. 3:12) Kuma yayin da ƙarshe yake kusatowa, maƙiyanmu za su daɗa tsananta mana.​—Mat. 24:9.

2-3. (a) Me ya kamata mu sani game da jin tsoro? (b) Me za mu tattauna a wannan talifin?

2 Ta yaya za mu shirya kanmu yanzu don tsanantawar da za mu fuskanta? Ba zai dace mu zauna muna tunani a kan yanayoyi dabam-dabam da za mu iya fuskanta a nan gaba ba. Idan mun yi hakan, tsoro da kuma alhini za su mamaye mu. Idan mun damu sosai don yanayoyi dabam-dabam da za mu iya fuskanta, za mu iya yin sanyin gwiwa tun ba a tsananta mana ba. (K. Mag. 12:25; 17:22) ‘Abokin gābanmu Shaiɗan’ yana yin amfani da tsoro don ya sa mu sanyin gwiwa kuma yana yin nasara sosai. (1 Bit. 5:​8, 9) Me za mu yi don mu kasance a shirye?

3 A wannan talifin, za mu tattauna yadda za mu iya ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah da kuma abin da ya sa yake da muhimmanci mu yi hakan. Za mu kuma tattauna abin da za mu iya yi don mu daɗa ƙarfin zuciya. Kuma na ƙarshe, za mu tattauna yadda za mu jimre da ƙiyayya daga masu tsananta mana.

YADDA ZA MU ƘARFAFA ABOTARMU DA JEHOBAH

4. Kamar yadda littafin Ibraniyawa 13:​5, 6 suka nuna, mene ne muke bukatar mu tabbata da shi, kuma me ya sa?

4 Ka kasance da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar ka kuma ba zai yasar da kai ba. (Karanta Ibraniyawa 13:​5, 6.) Shekaru da yawa da suka shige, an wallafa a Hasumiyar Tsaro cewa: “Mutumin da ke da dangantaka mai kyau da Allah zai dogara gare shi sa’ad da yake fuskantar jarrabawa.” Babu shakka, hakan gaskiya ne! Idan muna so mu yi nasara sa’ad da muke fuskantar tsanantawa, muna bukatar mu ƙaunaci Jehobah kuma mu dogara gare shi da dukan zuciyarmu, kada mu taɓa yin shakka cewa ba ya ƙaunar mu.​—Mat. 22:​36-38; Yaƙ. 5:11.

5. Mene ne zai taimaka maka ka san cewa Jehobah yana ƙaunar ka?

5 Ka riƙa karanta Littafi Mai Tsarki a kowace rana don ka kusaci Jehobah. (Yaƙ. 4:8) Sa’ad da kake karanta Kalmar Allah, ka mai da hankali ga halayensa masu kyau. Ka yi ƙoƙari ka fahimci yadda yake ƙaunar ka sa’ad da ka karanta wani abu da ya yi ko kuma ya ce. (Fit. 34:6) Yana iya kasancewa da wuya wasu su yarda cewa Allah yana ƙaunar su domin ba a taɓa nuna ana ƙaunar su ba. Idan kana fama da wannan matsalar, ka yi ƙoƙari kowace rana don ka lissafa hanyoyin da Jehobah ya nuna maka jinƙai da kuma alheri. (Zab. 78:​38, 39; Rom. 8:32) Sa’ad da ka yi tunani sosai a kan abubuwan da suka faru da kai da kuma abubuwan da ka karanta a Littafi Mai Tsarki, hakan zai taimaka maka ka iya lissafa abubuwan da Jehobah ya yi maka. Idan kana nuna godiya domin abubuwan da Jehobah yake yi, hakan zai sa dangantakarka da shi ta yi ƙarfi sosai.​—Zab. 116:​1, 2.

6. Kamar yadda Zabura 94:​17-19 suka nuna, ta yaya yin addu’a da dukan zuciyarka zai taimake ka?

6 Ka riƙa addu’a a kai a kai. Ka yi tunanin yadda mahaifi mai ƙauna yake ɗaukan yaronsa a hannu. Yaron zai iya faɗa wa mahaifinsa dukan abubuwan da ke faruwa da shi domin ya san cewa zai sami kāriya. Kai ma kana iya moran irin wannan dangantakar idan ka kusaci Jehobah ta yin addu’a a kowace rana. (Karanta Zabura 94:​17-19.) Sa’ad da kake addu’a ga Jehobah, ka gaya masa abin da ke zuciyarka, wato ka “zuba shi kamar ruwa.” Ka gaya masa dukan abubuwan da ke sa ka jin tsoro da kuma damuwa. (Mak. 2:19) Wane sakamako ne za ka samu? Littafi Mai Tsarki ya ce za ka sami “salama iri wadda ta wuce dukan ganewar ɗan Adam.” (Filib. 4:​6, 7) Idan ka ci gaba da yin addu’a ga Jehobah a wannan hanyar, za ka kusace shi.​—Rom. 8:​38, 39.

Za mu kasance da ƙarfin zuciya idan muka yi imani da Jehobah da kuma Mulkinsa

Ɗan’uwa Stanley Jones ya ƙarfafa bangaskiyarsa ta wajen kasancewa da tabbaci cewa Mulkin Allah zai zo (Ka duba sakin layi na 7)

7. Me ya sa kake bukatar ka kasance da tabbaci cewa alkawuran Allah za su cika?

7 Ka kasance da tabbaci cewa dukan alkawuran Allah za su cika. (L. Ƙid. 23:19) Idan kana shakka cewa alkawuran Allah za su cika, Shaiɗan da mutanensa za su sami damar tsorata ka. (K. Mag. 24:10; Ibran. 2:15) Ta yaya za ka ƙarfafa bangaskiyarka game da Mulkin Allah yanzu? Ka yi nazarin alkawuran da Allah ya yi da kuma dalilan da suka sa ka tabbata cewa alkawuran za su cika. Ta yaya yin hakan zai taimaka maka? Ka yi la’akari da misalin Ɗan’uwa Stanley Jones da aka saka a kurkuku na tsawon shekara bakwai domin imaninsa. Mene ne ya taimaka masa ya riƙe aminci? Ya ce: “Na kasance da bangaskiya domin na san Mulkin Allah da kuma abubuwan da Mulkin zai cim ma, kuma ban taɓa yin shakka ba. Don haka, babu wanda zai iya sa in daina bauta wa Jehobah.” Idan ka yi imani cewa alkawuran Allah za su cika, za ka kusaci Jehobah kuma ba za ka bar wani abu ya hana ka bauta masa ba.​—K. Mag. 3:​25, 26.

8. Mene ne ra’ayinmu game da halartan taro yake nunawa? Ka bayyana.

8 Ka riƙa halartan taro a kai a kai. Halartan taro yana taimaka mana mu kusaci Jehobah. Ra’ayinmu game da halartan taro zai nuna ko za mu jimre sa’ad da aka soma tsananta mana a nan gaba. (Ibran. 10:​24, 25) Me ya sa muka ce hakan? Idan muka bar wani ƙaramin abu ya hana mu zuwa taro a yanzu, me zai faru idan a nan gaba muka bukaci saka ranmu a cikin haɗari don mu halarci taro? Amma idan muka ƙuduri niyyar halartan taro, ba za mu yi sanyin gwiwa ba sa’ad da masu tsananta mana suke so su hana mu yin taro. Yanzu ne ya kamata mu soma son halartan taro. Idan muna son halartan taro, ko da ana tsananta mana ko kuma idan gwamnati ta saka wa aikinmu taƙunƙumi, ba za mu daina yi wa Allah biyayya ba.​—A. M. 5:29.

Haddace nassosi da waƙoƙi zai taimaka maka sa’ad da kake fuskantar tsanantawa (Ka duba sakin layi na 9) *

9. Me ya sa haddace nassosi zai taimaka mana mu yi shiri don tsanantawa?

9 Ka haddace Nassosin da kake so. (Mat. 13:52) Da yake dukanmu ajizai ne, muna mantuwa, amma Jehobah zai yi amfani da ruhunsa mai tsarki don ya sa ka tuna nassosin da ka karanta. (Yoh. 14:26) Ka yi la’akari da misalin wani ɗan’uwa da aka saka a kurkuku a Gabashin Jamus. Ya ce: “Na yi farin ciki sosai cewa a lokacin, na riga na haddace nassosi da yawa! Duk da cewa ni kaɗai ne a kurkukun, na yi tunani a kan batutuwa dabam-dabam a Littafi Mai Tsarki.” Nassosin nan sun taimaka masa ya kusaci Jehobah kuma ya jimre.

(Ka duba sakin layi na 10) *

10. Me ya sa ya kamata mu haddace waƙoƙinmu?

10 Ka haddace da kuma rera waƙoƙin ibada. A lokacin da Bulus da Sila suke kurkuku a Filibi, sun rera waƙoƙin yabo da suka haddace. (A. M. 16:25) Hakazalika, abin da ya taimaka wa ’yan’uwanmu a Ƙasashen Tarayyar Soviet da aka kai zaman bauta a Saiberiya ke nan. ’Yar’uwa Mariya Fedun ta ce: “Mun rera dukan waƙoƙin da muka sani da ke littafinmu na waƙa.” Ta ce waƙoƙin nan sun ƙarfafa dukansu kuma sun taimaka musu su kusaci Jehobah. Shin kana samun ƙarfin gwiwa sa’ad da kake rera waƙoƙin ibada da kake so sosai? Idan haka ne, ka haddace waɗannan waƙoƙin yanzu!​—Ka duba akwatin nan “ Ka Ba Ni Ƙarfin Hali.”

YADDA ZA KU SAMI ƘARFIN ZUCIYA

11-12. (a) Kamar yadda 1 Sama’ila 17:37 da 45-47 suka nuna, me ya ba Dauda ƙarfin zuciya? (b) Wane darasi mai muhimmanci ne muka koya daga labarin Dauda?

11 Muna bukatar ƙarfin zuciya don mu yi nasara sa’ad da muke fuskantar tsanantawa. Mene ne za ka yi idan kana ganin ba ka da ƙarfin zuciya? Ka tuna cewa zama mai ƙarfin zuciya bai dangana ga girmanka ko ƙarfinka ko kuma baiwarka ba. Ka yi la’akari da misalin Dauda sa’ad da ya yaƙi Goliyat. Idan aka gwada Dauda da Goliyat, Dauda ƙaramin yaro ne marar ƙarfi kuma ba shi da makamai. Dauda ba shi da takobi, duk da haka, yana da ƙarfin zuciya. Cike da gaba gaɗi, Dauda ya yaƙi Goliyat mai girman kai.

12 Me ya taimaka wa Dauda ya kasance da ƙarfin zuciya? Ya tabbata cewa Jehobah yana tare da shi. (Karanta 1 Sama’ila 17:​37, 45-47.) Dauda bai mai da hankali ga girmar Goliyat ba. A maimakon haka, ya mai da hankali ga yadda Jehobah yake da iko fiye Goliyat. Wane darasi ne wannan labarin ya koya mana? Za mu kasance da ƙarfin zuciya idan muna da tabbaci cewa Jehobah yana tare da mu kuma muka tabbatar wa kanmu cewa Jehobah ya fi maƙiyanmu iko. (2 Tar. 20:15; Zab. 16:8) Ta yaya za mu kasance da ƙarfin zuciya a yanzu kafin mu soma fuskantar tsanantawa?

13. Ta yaya za mu zama masu ƙarfin zuciya? Ka bayyana.

13 Za mu yi ƙarfin zuciya idan muna yi wa mutane wa’azi game da Mulkin Allah. Me ya sa? Domin sa’ad da muke wa’azi, muna koyan yadda za mu dogara ga Jehobah kuma mu guji jin tsoron mutane. (K. Mag. 29:25) Kamar yadda motsa jiki yake sa jijiyoyinmu ƙarfi, za mu zama masu ƙarfin zuciya idan muna zuwa wa’azi gida-gida da yin wa’azi a inda jama’a suke da a kasuwa da kuma yin wa’azi sa’ad da muke yin ayyukanmu na yau da kullum. Idan muna wa’azi da ƙarfin zuciya yanzu, ba za mu daina yin wa’azi ba sa’ad da aka saka wa aikinmu taƙunƙumi.​—1 Tas. 2:​1, 2.

’Yar’uwa Nancy Yuen ta ƙi daina yin wa’azi (Ka duba sakin layi na 14)

14-15. Wane darasi ne za mu iya koya daga labarin Nancy Yuen da Valentina Garnovskaya?

14 Muna iya koyan darussa masu kyau daga misalin wasu ’yan’uwa mata biyu da suka nuna ƙarfin zuciya sosai. ’Yar’uwa Nancy Yuen wadda tsayinta bai wuce kafa biyar ba ta nuna ƙarfin zuciya sosai. * Ta ƙi daina yin wa’azin Mulkin Allah. A sakamakon haka, an saka ta a kurkuku na tsawon shekaru 20 a ƙasar Caina. Hukumomin da suka tuhume ta sun ce ita ce “mace mafi taurin kai” a ƙasarsu!

’Yar’uwa Valentina Garnovskaya tana da tabbaci cewa Jehobah yana tare da ita (Ka duba sakin layi na 15)

15 Ban da haka, an saka wata ’yar’uwa mai suna Valentina Garnovskaya a kurkuku a ƙasashen Tarayyar Soviet sau uku na tsawon shekaru 21. * Me ya sa? Domin ta ƙuduri niyyar ci gaba da yin wa’azi. Saboda haka, hukumomi sun ce ta yi “laifi mai tsanani.” Mene ne ya taimaka wa mata biyun nan su kasance da ƙarfin zuciya? Sun tabbata cewa Jehobah yana tare da su.

16. Me muke bukata idan muna so mu zama masu ƙarfin zuciya?

16 Kamar yadda muka tattauna, idan muna so mu zama masu ƙarfin zuciya, bai kamata mu dogara da baiwarmu ba. A maimakon haka, muna bukatar mu gaskata cewa Jehobah yana tare da mu kuma zai taimaka mana. (M. Sha. 1:​29, 30; Zak. 4:6) Sanin hakan zai sa mu kasance da ƙarfin zuciya.

YADDA ZA MU JIMRE DA ƘIYAYYA

17-18. Wane gargaɗi ne Yesu ya yi mana a Yohanna 15:​18-21? Ka bayyana.

17 Muna so mutane su riƙa daraja mu, amma bai kamata mu raina kanmu idan mutane suka tsane mu ba. Yesu ya ce: “Masu albarka ne ku idan mutane suka ƙi ku, suka ware ku, suna zaginku, suna cewa ku mugaye ne, saboda ɗan mutum!” (Luk. 6:22) Mene ne Yesu yake nufi?

18 Yesu ba ya nufin cewa Kiristoci za su yi farin ciki idan mutane sun tsane su. A maimakon haka, yana yi mana gargaɗi ne game da abubuwan da za mu fuskanta. Mu ba na duniya ba ne, muna bin koyarwar Yesu kuma muna yi wa mutane wa’azi. Saboda haka, mutanen duniya sun tsane mu. (Karanta Yohanna 15:​18-21.) Muna so mu riƙa faranta wa Jehobah rai. Saboda haka, idan mutane suka tsane mu domin muna ƙaunar Jehobah, hakan bai dame mu ba.

19. Ta yaya za mu bi misalin manzannin Yesu?

19 Kada ka bar abin da mutane suka ce ko kuma suka yi ya sa ka jin kunya cewa kai Mashaidin Jehobah ne. (Mik. 4:5) Za mu daina jin tsoron mutane idan muka yi tunani a kan abin da manzannin Yesu a Urushalima suka yi bayan an kashe Yesu. Sun san cewa malaman addinin Yahudawa sun tsane su. (A. M. 5:​17, 18, 27, 28) Amma a kowace rana, suna zuwa haikali kuma suna gaya wa kowa cewa su mabiyan Yesu ne. (A. M. 5:42) Ba su bar tsoro ya hana su yin haka ba. Mu ma za mu iya daina jin tsoro idan muka gaya wa mutane cewa mu Shaidun Jehobah ne a makaranta ko a wurin aikinmu ko kuma a unguwarmu.​—A. M. 4:29; Rom. 1:16.

20. Me ya sa manzannin Yesu suka yi farin ciki duk da cewa ana tsananta musu?

20 Mene ne ya sa manzannin Yesu farin ciki? Sun san dalilin da ya sa mutane suka tsane su, kuma a gare su, gata ne babba a wulaƙanta su domin suna yin abin da Jehobah yake so. (Luk. 6:23; A. M. 5:41) Manzo Bitrus ya ce: “Ko kun sha wuya saboda aikata adalci, ai, ku masu albarka ne.” (1 Bit. 2:​19-21; 3:14) Ba za mu daina bauta wa Allah ba idan muka fahimci cewa mutane suna tsananta mana domin muna yin abin da Jehobah yake so.

ZA KA AMFANA SOSAI IDAN KA YI SHIRI

21-22. (a) Me ka ƙuduri niyyar yi yanzu don tsanantawar da za ka iya fuskanta? (b) Me za mu tattauna a talifi na gaba?

21 Ba mu san lokacin da mutane za su soma tsananta mana ba ko kuma su saka wa aikinmu taƙunƙumi ba. Amma mun san cewa za mu iya yin shiri yanzu ta wajen ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah da zama masu ƙarfin zuciya da kuma koyan yadda za mu jimre sa’ad da mutane suka tsane mu. Idan muka yi shiri yanzu, za mu ci gaba da bauta wa Jehobah.

22 Amma idan aka saka wa aikinmu taƙunƙumi kuma fa? A talifi na gaba, za mu tattauna ƙa’idodin da za su taimaka mana mu ci gaba da bauta wa Jehobah sa’ad da aka saka wa aikinmu taƙunƙumi.

WAƘA TA 118 Ka “Ƙara Mana Bangaskiya”

^ sakin layi na 5 Babu wanda yake so a tsane shi. Amma ko mun ƙi ko mun so, za a tsananta wa dukanmu. Wannan talifin zai taimaka mana mu yi shiri don tsanantawar da za mu fuskanta.

^ sakin layi na 14 Ka kalli bidiyon nan Jehovah’s Name Will Be Made Known a sashen GANAWA DA LABARAI a Tashar JW.

^ sakin layi na 15 Ka duba littafin nan 2008 Yearbook of Jehovah’s Witnesses, shafuffuka na 191-192.

^ sakin layi na 66 BAYANI A KAN HOTO: Wasu iyaye suna amfani da katuna don su taimaka wa yaransu su haddace nassosi a lokacin da suke ibada ta iyali.

^ sakin layi na 69 BAYANI A KAN HOTO: Wasu iyali suna rera waƙoƙinmu a motarsu sa’ad da suke zuwa taro.