Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 52

Iyaye, Ku Koyar da Yaranku Su Kaunaci Jehobah

Iyaye, Ku Koyar da Yaranku Su Kaunaci Jehobah

“’Ya’ya kyauta ne kuma gādo ne daga wurin Yahweh.”​—ZAB. 127:3.

WAƘA TA 134 Yara Amana Ne Daga Allah

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Wane aiki ne Jehobah ya ba iyaye?

JEHOBAH ya halicci ma’aurata na farko da sha’awar haifan yara. Ya dace da Littafi Mai Tsarki ya ce: “’Ya’ya kyauta ne kuma gādo ne daga wurin Yahweh.” (Zab. 127:3) Mene ne furucin nan yake nufi? A ce wani amininka ya ba ka ajiyar kuɗi mai yawa sosai. Yaya za ka ji? Babu shakka, za ka yi farin ciki cewa ya amince da kai. Amma, wataƙila hankalinka zai tashi don kada a saci kuɗin. Jehobah amininmu na kud da kud ya ba iyaye wata amana da ta fi kuɗi. Ya ba iyaye aikin tabbatar da cewa sun kula da yaransu kuma sun sa yaran farin ciki.

2. Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?

2 Wane ne ya kamata ya tsai da shawara a kan ko ma’aurata za su haifi yara da kuma lokacin da za su yi hakan? Mene ne iyaye za su iya yi don su taimaka wa yaransu su yi farin ciki a rayuwa? Ka yi la’akari da wasu ƙa’idodin da ke Kalmar Allah da za su taimaka wa ma’aurata su tsai da shawarwari masu kyau.

KU DARAJA SHAWARAR DA MA’AURATA SUKA YANKE

3. (a) Wane ne ya kamata ya tsai da shawara ko ma’aurata za su haifi yara? (b) Wace ƙa’idar Littafi Mai Tsarki ce ya kamata abokai da iyalin ma’aurata su riƙa tunawa?

3 A wasu al’adu, ana ganin ya kamata mata da miji da ba su daɗe da yin aure ba su soma haifan yara nan da nan. Iyalinsu da kuma wasu za su iya matsa musu su bi al’adar. Wani ɗan’uwa mai suna Jethro da ke Asiya ya ce: “A ikilisiya, wasu da suke da yara suna matsa wa ma’aurata da ba su da yara su soma haifan yara.” Wani ɗan’uwa kuma mai suna Jeffrey a Asiya ya ce: “Wasu suna gaya wa ma’aurata da ba su da yara cewa babu wanda zai kula da su sa’ad da suka tsufa.” Duk da haka, ma’aurata ne suke da hakkin tsai da shawara ko za su haifi yara ko a’a. (Gal. 6:5) Hakika, abokai da iyalai suna so ma’aurata su yi farin ciki. Amma ya kamata kowa ya san cewa mata da mijin ne za su tsai da shawarar haifan yara ko a’a.​—1 Tas. 4:11.

4-5. Waɗanne batutuwa biyu ne ya kamata ma’aurata su tattauna, kuma a wane lokaci ne ya kamata su yi hakan? Ka bayyana.

4 Ya kamata ma’aurata da suka tsai da shawarar haifan yara su tattauna muhimman tambayoyin nan biyu: Na farko, a wane lokaci ne suke so su soma haifan yara? Na biyu, yara nawa ne za su haifa? A wane lokaci ne ya dace ma’aurata su tattauna waɗannan batutuwa? Kuma me ya sa waɗannan batutuwa biyu suke da muhimmanci sosai?

5 A yawancin lokuta, ya kamata namiji da ta mace da suke so su yi aure su tattauna batun haifan yara kafin su yi aure. Me ya sa? Dalili ɗaya shi ne domin yana da muhimmanci su kasance da ra’ayi ɗaya a wannan batun. Ƙari ga haka, za su bukaci su tattauna ko suna a shirye su ɗauki wannan hakkin. Wasu ma’aurata sun tsai da shawara cewa za su jira sai bayan shekara ɗaya ko biyu da aure kafin su haifi yara domin renon yara zai ci lokaci da kuma kuzarinsu sosai. Sun ce jira kaɗan zai sa su saba da aurensu kuma su kusaci juna kafin su zama iyaye.​—Afis. 5:33.

6. Mene ne wasu ma’aurata suka tsai da shawarar yi domin mawuyanci lokaci da muke ciki?

6 Wasu Kiristoci sun zaɓi su bi misalin yaran Nuhu da matansu. Waɗannan ma’aurata uku ba su haifi yara nan da nan ba. (Far. 6:18; 9:​18, 19; 10:1; 2 Bit. 2:5) Yesu ya gwada zamaninmu da “kwanakin Nuhu,” kuma babu shakka cewa muna zama a kwanakin ƙarshe da “za a sha wahala sosai.” (Mat. 24:37; 2 Tim. 3:1) Saboda haka, wasu ma’aurata sun tsai da shawara cewa ba za su haifi yara ba domin su ƙara ƙwazo sosai a hidimar Jehobah.

Ma’aurata masu hikima suna yin ‘lissafi’ sosai sa’ad da suke so su tsai da shawara ko za su haifi yara da kuma yawan yara da za su haifa (Ka duba sakin layi na 7) *

7. Ta yaya ƙa’idodin da ke Luka 14:​28, 29 da kuma Karin Magana 21:5 za su taimaka wa ma’aurata?

7 Ma’aurata masu hikima za su ‘yi lissafi’ sosai sa’ad da suke tattauna ko za su haifi yara da kuma yawan yara da za su haifa. (Karanta Luka 14:​28, 29.) Ma’auratan waɗanda yaransu sun yi girma sun san cewa renon yara yana cin kuɗi sosai kuma yana ɗaukan lokaci da kuma kuzari. Saboda haka, yana da muhimmanci su tattauna tambayoyin nan: ‘Shin mu biyu za mu riƙa aiki don mu biya bukatun iyalinmu? Mun san ainihin abubuwan da muke bukata kuwa? Idan dukanmu za mu yi aiki, wane ne zai kula da yaranmu? Misalin wane ne yaran za su riƙa bi?’ Sa’ad da ma’aurata suka tattauna tambayoyin nan, suna bin kalmomin da ke littafin Karin Magana 21:5.​Karanta.

Miji mai ƙaunar matarsa zai yi iya ƙoƙarinsa ya taimaka mata (Ka duba sakin layi na 8)

8. Waɗanne matsaloli ne ya kamata ma’aurata su san cewa za su fuskanta, kuma me mijin da ke ƙaunar matarsa zai yi?

8 Kula da yara yana ɗaukan lokaci da kuzari sosai. Saboda haka, idan ma’aurata suka haifi yara da yawa a cikin ƙanƙanin lokaci, zai yi musu wuya su biya bukatar kowane yaro. Wasu ma’aurata da suke da yara da yawa sun ce a wasu lokuta, ba sa sanin abin da za su ce ko kuma yi. Mahaifiyar takan gaji a kowane lokaci. Kuma hakan zai sa ba za ta sami ƙarfin yin nazari da addu’a da kuma wa’azi a kai a kai ba. Ƙari ga haka, zai yi mata wuya ta mai da hankali a taro kuma ta amfana. Saboda haka, miji mai ƙaunar matarsa zai yi iya ƙoƙarinsa don ya taimaka wa matarsa sa’ad da yaransu suke bukatar a kula da su a taro da kuma a gida. Alal misali, zai iya taimaka wa matarsa da yin aikace-aikacen gida. Zai yi aiki tuƙuru don ya tabbata cewa kowa a iyalin ya amfana daga Ibada ta Iyali. Ban da haka, zai riƙa fita wa’azi da iyalinsa a kai a kai.

KU KOYA WA YARA SU ƘAUNACI JEHOBAH

9-10. Mene ne ya kamata iyaye su yi don su taimaka wa yaransu?

9 Waɗanne abubuwa ne iyaye za su iya yi don su taimaka wa yaransu su ƙaunaci Jehobah? Ta yaya za su iya ƙare yaransu daga wannan muguwar duniya? Ka yi la’akari da wasu matakai da iyaye za su iya ɗauka.

10 Ku yi addu’a don Jehobah ya taimaka muku. Manoah da matarsa da suka zama iyayen Samson sun kafa mana misali mai kyau. Sa’ad da Manoah ya san cewa matarsa za ta haihu, ya roƙi Jehobah ya yi musu ja-goranci a yadda za su yi renon yaronsu.

11. Ta yaya iyaye za su bi misalin Manoah, kamar yadda yake a littafin Alƙalai 13:8?

11 Nihad da Alma daga ƙasar Bosnia da Herzegovina sun bi misalin Manoah. Sun ce: “Kamar Manoah, mun roƙi Jehobah ya koya mana yadda za mu zama iyayen kirki. Kuma Jehobah ya amsa addu’armu a hanyoyi dabam-dabam. Ya yi hakan ta Nassosi da littattafanmu da taron ikilisiya da kuma taron yanki.”​—Karanta Alƙalai 13:8.

12. Wane misali ne Yusufu da Maryamu suka kafa wa yaransu?

12 Ku nuna misali mai kyau. Ko da yake yana da muhimmanci ka koyar da yaranka, amma misalinka ne zai fi shafan su. Yusufu da Maryamu sun kafa wa Yesu da kuma sauran yaransu misali mai kyau. Yusufu ya yi aiki tuƙuru don ya biya bukatun iyalinsa. Ƙari ga haka, Yusufu ya ƙarfafa iyalinsa su so bauta wa Jehobah. (M. Sha. 4:​9, 10) Yusufu ya kai iyalinsa Urushalima “kowace shekara” don su kiyaye Idin Ƙetarewa ko da yake Doka ba ta bukaci magidanta su riƙa yin hakan ba. (Luk. 2:​41, 42) Wataƙila wasu magidanta a zamanin suna ganin yin irin wannan tafiya yana da wuya ainun ko ɓata lokaci ne ko kuma yana da tsada sosai. Duk da haka, Yusufu yana son yin ayyukan ibada kuma ya koya wa yaransa su riƙa yin haka. Ban da haka, Maryamu ta san Nassosi sosai. Ta kalaminta da ayyukanta, ta koya wa yaranta su so Kalmar Allah.

13. Ta yaya wasu ma’aurata suka bi misalin Yusufu da Maryamu?

13 Nihad da Alma da aka ambata ɗazu sun bi misalin Yusufu da Maryamu. Ta yaya hakan ya taimaka musu su reni ɗansu ya ƙaunaci Allah kuma ya bauta masa? Sun ce, “Ta wajen kafa wa ɗanmu misali mai kyau, mun nuna masa cewa ya dace ya riƙa bin ƙa’idodin Jehobah.” Nihad ya daɗa cewa, “Ka zama irin mutum da kake son ɗanka ya zama.”

14. Me ya sa ya dace iyaye su san abokan yaransu?

14 Ku taimaka wa yaranku su zaɓi abokan kirki. Ya kamata iyaye su san abokan yaransu da kuma abin da suke yi. Hakan ya ƙunshi sanin abokan yaranku a shafin sada zumunta na Intane da kuma a wayarsu. Waɗannan abokan za su iya shafan tunanin yaranku da kuma ayyukansu.​—1 Kor. 15:33.

15. Me iyaye za su iya koya daga misalin Jessie?

15 Mene ne iyaye za su yi idan ba su iya amfani da kwamfuta ko kuma na’urori ba? Jessie, wani mahaifi a ƙasar Filifin ya ce: “Ba mu iya amfani da na’urori sosai ba. Amma hakan bai hana mu koya wa yaranmu haɗarurrukan da ke tattare da yin amfani na’urori ba.” Jessie bai hana yaransa yin amfani da na’urori domin bai iya amfani da su ba. Ya ce: “Na ƙarfafa yarana su yi amfani da na’urorinsu don su koyi sabon yare da shirya taro da kuma karanta Littafi Mai Tsarki kullum.” Iyaye, kun karanta da kuma tattauna da yaranku batun aika saƙo da kuma hotuna ta shafin sada zumunta da ke sashen “Matasa” a jw.org® kuwa? Kun kalla da kuma tattauna bidiyoyin nan Waye Ke da Iko, Kai ko Na’urarka? da kuma Ka Zama Mai Hikima a Dandalin Zumunta na Intane? * Hakan zai taimaka muku yayin da kuke koya wa yaranku yadda za su yi amfani da na’urori yadda ya dace.​—K. Mag. 13:20.

16. Mene ne iyaye da yawa suka yi, kuma mene ne sakamakon?

16 Iyaye da yawa suna shirya ayyuka da za su sa yaransu su riƙa cuɗanya da mutanen da ke kafa misali mai kyau a hidimar Jehobah. Alal misali, wasu ma’aurata a ƙasar Kwaddebuwa masu suna N’Déni da Bomine sukan gayyaci mai kula da da’ira ya zauna a gidansu. N’Déni ya ce: “Hakan ya taimaka wa ɗanmu sosai. Ya soma hidimar majagaba kuma yanzu shi mataimakin mai kula da da’ira ne.” Shin za ku taimaka wa yaranku su riƙa yin irin wannan cuɗanya?

17-18. A wane lokaci ne ya kamata iyaye su soma koyar da yaransu?

17 Ku soma koyar da yaranku tun suna ƙanana. Ya fi kyau iyaye su soma koyar da yaransu tun suna ƙanana. (K. Mag. 22:6) Muna da misalin Timoti wanda ya yi tafiya da manzo Bulus sa’ad da ya yi girma. Afiniki mahaifiyar Timoti da kakarsa Loyis sun soma koyar da shi tun yana “ƙaramin yaro.”​—2 Tim. 1:5; 3:15.

18 Wasu ma’aurata kuma a ƙasar Kwaddebuwa masu suna Jean-Claude da Peace sun reni dukan yaransu shida su ƙaunaci Jehobah kuma su riƙa bauta masa. Mene ne ya taimaka musu? Sun bi misalin Afiniki da Loyis. Sun ce: “Da zarar mun haifi yaranmu, mun soma koya musu Kalmar Allah.”​—M. Sha. 6:​6, 7.

19. Mene ne koya wa yaranku Kalmar Allah ya ƙunsa?

19 Mene ne ‘koya’ wa yaranku Kalmar Jehobah yake nufi? A littafin Maimaitawar Shari’a 6:​7, kalmar nan ‘koyar’ a Ibrananci tana nufin “ka koyar kuma ka sa mutum ya fahimci abin da kake koya masa ta wurin maimaita shi a kai a kai.” Don iyaye su yi hakan, suna bukatar su riƙa kasancewa da yaransu a kai a kai. A wasu lokuta, iyaye suna maimaita wa yaransu wani batu, kuma hakan na iya gajiyar da iyayen. Amma, ya kamata iyaye su yi amfani da wannan zarafi don su taimaka wa yaransu su fahimci Kalmar Allah kuma su yi amfani da ita.

Iyaye suna bukatar su tsai da shawara a kan yadda za su reni kowanne cikin yaransu (Ka duba sakin layi na 20) *

20. Ka bayyana yadda Zabura 127:4 za ta iya taimaka wajen renon yara.

20 Ku san yaranku sosai. Zabura ta 127 ta kwatanta yara da kibiyoyi. (Karanta Zabura 127:4.) Ana yin kibiyoyi da kayayyaki dabam-dabam, kuma girman kibiyoyin ya bambanta. Hakazalika, halin kowane yaro ya bambanta. Saboda haka, iyaye suna bukatar su san yadda za su koyar da kowanne cikin yaransu. Wasu ma’aurata a ƙasar Isra’ila a yau da suka yi nasara wajen renon yaransu biyu su bauta wa Jehobah sun faɗi abin da ya taimaka musu. Sun ce: “Ba mu yi nazari da su biyu tare ba.” Hakika, kowane magidanci zai yanke shawara a kan fasalin da zai fi dacewa da yaransa.

JEHOBAH ZAI TAIMAKA MAKA

21. Ta yaya Jehobah yake taimaka wa iyaye?

21 A wasu lokuta, yana yi wa iyaye wuya sosai su koyar da yaransu, amma yara amana ne daga wurin Jehobah. Yana shirye ya taimaka wa iyaye kuma ya saurari addu’o’insu. Ƙari ga haka, yana amsa addu’o’insu sa’ad da suka yi amfani da Littafi Mai Tsarki da littattafanmu don su koyar da su. Ban da haka, misali da kuma shawarar wasu iyaye da suka manyanta a ikilisiya na taimaka wa iyaye.

22. Waɗanne abubuwa mafi kyau ne iyaye za su iya ba yaransu?

22 Wasu mutane sun ce renon yaro guda yana ɗaukan shekara 20, amma gaskiyar ita ce, iyaye ba sa gama renon yaransu. Kyauta mafi kyau da za ku ba yaranku shi ne ƙauna da lokacinku da kuma koya musu Littafi Mai Tsarki. Yadda kowane yaro zai ɗauki koyarwar zai bambanta. Amma yara da yawa waɗanda iyaye da suke ƙaunar Jehobah ne suka rene su suna godiya, kuma suna ji yadda wata ’yar’uwa mai suna Joanna Mae a ƙasar Asiya take ji. Ta ce: “Idan na tuna yadda iyayena suka rene ni, ina godiya don yadda suka horar da ni kuma suka koya mini in ƙaunaci Jehobah. Sun sa in yi rayuwa mai ma’ana.” (K. Mag. 23:​24, 25) Kiristoci da yawa suna jin hakan.

WAƘA TA 59 Mu Yabi Jehobah

^ sakin layi na 5 Ya kamata ma’aurata su haifi yara kuwa? Idan suna son yara, guda nawa ne ya kamata su haifa? Kuma ta yaya za su koya wa yaransu su ƙaunaci Jehobah kuma su bauta masa? A wannan talifin, an tattauna misalan wasu a zamaninmu da kuma ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da za su iya taimaka mana mu amsa waɗannan tambayoyin.

^ sakin layi na 15 Ka kuma duba talifin nan “Ka Guji Haɗarin da Ke Dandalin Sada Zumunta na Intane” a Littafin Taro na Yuni 2018.

^ sakin layi na 60 BAYANI A KAN HOTO: Wasu ma’aurata suna tattauna ko za su haifi yara, suna tattauna farin ciki da hakan yake kawowa da kuma aikin da ke ciki.

^ sakin layi na 64 BAYANI A KAN HOTO: Waɗannan ma’auratan ba sa yin nazari da yaransu tare domin shekarunsu da iyawarsu ya bambanta.