Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Littafi Mai Tsarki ya ce ana bukatar aƙalla shaidu biyu kafin a yanke wa wani hukunci. (L. Ƙid. 35:30; M. Sha. 17:6; 19:15; Mat. 18:16; 1 Tim. 5:19) Amma a dokar da Allah ya ba Isra’ilawa, ya ce idan wani ya yi wa macen da an riga an yi alkawarin aure da ita fyaɗe, macen ba ta da laifi amma mutumin yana da shi. Me ya sa ba ta da laifi amma mutumin yana da laifi duk da cewa babu wani da ya shaida aukuwar lamarin?

A batun da aka ambata a Maimaitawar Shari’a 22:​25-27, mutumin ya riga ya yi laifin, ba ƙoƙarin sani ko ya yi laifi ake nema a yi ba. Dokar ta mai da hankali a kan nuna cewa macen ba ta da laifi. Ka yi la’akari da abin da ayoyin suke magana a kai.

A Maimaitawar Shari’a 22:​23, 24, an yi magana game da mutumin da ya yi lalata a “cikin gari” da matar da aka yi alkawarin aure da ita. Abin da ya yi ya nuna cewa ya yi zina domin an riga an yi alkawarin aure da matar. Matar kuma fa? “Ba ta yi kukan neman taimako ba.” Da a ce ta yi kuka, da mutane sun ji kuma sun taimake ta. Hakan ya sa dukansu biyu suna da laifi kuma za a hukunta su don zinar da suka yi.

Bayan haka, dokar ta yi magana game da wani yanayi dabam: “Idan a daji ne mutum ya sadu da macen da an riga an ɗaura alkawarin aure da ita, ya kuma kama ta ya kwana da ita ƙarfi da yaji, to, wannan mutumin kaɗai zai mutu. Ba za ku yi wa macen nan kome ba. Macen nan ba ta yi wani laifin da ya isa mutuwa ba, gama wannan magana tana kamar wanda ya fāda wa maƙwabcinsa ya kashe shi. Tun da yake ya same ta a daji, wataƙila macen ta yi kukan neman taimako, amma babu wanda zai cece ta.”​—M. Sha. 22:​25-27.

A irin wannan yanayin, alƙalan za su amince cewa macen ba ta da laifi. Me ya sa? Za su yarda cewa “wataƙila macen ta yi kukan neman taimako, amma babu wanda zai cece ta.” Don haka, ba ta yi zina ba. Amma za a tuhumi mutumin da laifin fyaɗe da kuma zina domin ya kwana “ƙarfi da yaji” da matar da aka yi alkawarin aure da ita.

Wannan dokar ta mai da hankali ne ga nuna cewa macen ba ta da laifi. Duk da haka, dokar ta nuna cewa mutumin ya yi fyaɗe da kuma zina. Za mu iya kasancewa da tabbaci cewa alƙalan za su “yi bincike” da “tambaya sosai” kafin su yanke hukuncin da ta jitu da ƙa’idar da Allah ya ba su kuma ya maimaita sau da yawa.​—M. Sha. 13:14; 17:4; Fit. 20:14.