Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Nemi Abin da Ya Fi Zinariya Tamani

Ka Nemi Abin da Ya Fi Zinariya Tamani

Shin ka taɓa samun zinariya? Mutane da yawa ba su taɓa ba. Duk da haka, da akwai miliyoyin mutanen da suka sami abin da ya fi zinariya tamani. Wannan abin ita ce hikimar da Allah yake bayarwa kuma “ba za a saye ta da zinariya tsantsa ba.”—Ayu. 28:12, 15.

ƊALIBAN Littafi Mai Tsarki suna kama da mahaƙar ma’adanai. Waɗannan ɗaliban suna bukatar su yi iya ƙoƙarinsu wajen bincika Littafi Mai Tsarki don su kasance da hikimar da babu irinta. Saboda haka, bari mu yi la’akari da hanyoyi uku da ake yin amfani da su don samun zinariya da kuma abin da za mu koya daga hakan.

SHIN KA SAMU ABU MAI TAMANI KAMAR ZINARIYA?

A ce kana tafiya a bakin teku, sai ka ga wani ƙaramin dutse yana walƙiya. Ka tsaya kuma ka kalli dutsen, sai ka ga cewa zinariya ce. Hakan ya sa ka farin ciki sosai. Ɗan ƙaramin dutse ne amma ba a cika samunsa kamar yadda ake samun lu’ulu’u. Babu shakka, za ka sake duba ko’ina ko za ka ga wata zinariyar.

Wataƙila, ka tuna ranar da wani Mashaidin Jehobah ya zo gidanka kuma ya tattauna Littafi Mai Tsarki da kai. Mai yiwuwa ka tuna lokacin da ka fara koyan wani abu daga Littafi Mai Tsarki, wataƙila sa’ad da ka ga sunan Allah, wato Jehobah a cikin Littafi Mai Tsarki. (Zab. 83:18) Ƙari ga haka, ka koyi cewa za ka iya zama abokin Jehobah. (Yaƙ. 2:23) Nan da nan sai ka fahimci cewa ka sami wani abin da ya fi zinariya tamani! Kuma tun daga lokacin, kana marmarin ƙara koyan abubuwa game da Allah.

KA CI GABA DA NEMA!

Ana iya samun burbuɗin zinariya da yawa a ƙorama da kuma teku. A cikin ’yan watanni a irin waɗannan wuraren, mahaƙar ma’adinai masu aiki tuƙuru suna iya samun dutsen da ke cike da zinariya wanda za a iya samun dubban daloli idan aka sayar da su.

Sa’ad da ka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah, kana iya ji kamar mai neman zinariya da ya samu zinariya da yawa masu tamani. Mai yiwuwa ka sami ƙarin ilimi sa’ad da kake bimbini a kan ayoyin Littafi Mai Tsarki, kuma hakan ya sa ka koyi abubuwa da yawa game da Jehobah. Yayin da kake bincike a kan ayoyin Littafi Mai Tsarki, ka koyi yadda za ka iya kusantar Jehobah da kuma yadda za ka ci gaba da kasancewa cikin ƙaunarsa. Ƙari ga haka, ya sa ka kasance da begen samun rai na har abada.—Yaƙ. 4:8; Yahu. 20, 21.

Shin kana iya ƙoƙarinka wajen koyan abubuwa game da Littafi Mai Tsarki kamar yadda mai neman ma’adanai yake yi wajen neman zinariya?

 Kamar yadda mai neman ma’adanai yake neman zinariya mai tamani, wataƙila kai ma ka yi iya ƙoƙarinka wajen koyan abubuwa game da Jehobah. Bayan ka koyi waɗannan abubuwan, mai yiwuwa hakan ya motsa ka ka keɓe ranka ga Jehobah kuma ka yi baftisma.—Mat. 28:19, 20.

KA CI GABA DA BINCIKE!

Mai haƙa ma’adanai yana iya ganin ’yar ƙaramar zinariya a cikin duwatsu. Amma saboda ƙaramar zinariyar da ke cikin dutsen, zai iya farfasa duwatsun don ya samu zinariyar. Idan ka duba duwatsun za ka ɗauka cewa babu zinariya a ciki. Amma haƙar za ta cim ma ruwa domin a ƙarshe, ana samun zinariya.

Hakazalika, mutum yana bukatar ya ci gaba da yin bincike bayan ya san muhimman koyarwa game da Kristi. (Ibran. 6:1, 2) Kana bukatar ka yi iya ƙoƙarinka wajen koyan sababbin abubuwa kuma ka koyi darussa masu muhimmanci daga nazarin Littafi Mai Tsarki da kake yi. Saboda haka, me za ka yi don ka ci gaba da amfana daga nazarin Littafi Mai Tsarki, ko da ka daɗe kana yin hakan?

Ka ci gaba da son koyan abubuwa. Ka mai da hankali ga bayanai masu muhimmanci. Ka ci gaba da yin bincike sosai don hakan zai taimaka maka ka samu hikimar Allah da ja-gorarsa. (Rom. 11:33) Ka yi amfani da abubuwan bincike da kuke da su a yarenku don ka san Littafi Mai Tsarki sosai. Ka nemi ja-gorar da kake bukata da kuma amsoshin tambayoyinka game da Littafi Mai Tsarki. Ka tambayi wasu game da Nassosi da talifofin da ya taimaka masu ko kuma ya ƙarfafa su. Ka gaya wa mutane game da abubuwan da ka koya sa’ad da kake nazarin Littafi Mai Tsarki.

Hakika, burinka ba kawai ka ƙara ilimi a kan Littafi Mai Tsarki ba ne. Manzo Bulus ya ce, “ilimi” yakan sa mutum ya soma girman kai. (1 Kor. 8:1) Saboda haka, ka kasance da tawali’u da kuma bangaskiya sosai. Yin ibada ta iyali a kai a kai da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki za su taimaka maka ka yi rayuwar da ta jitu da ƙa’idodin Allah. Ƙari ga haka, za su motsa ka ka nuna kana ƙaunar mutane. Mafi muhimmanci shi ne, za ka yi farin ciki cewa ka sami abin da ya fi zinariya tamani.—Mis. 3:13, 14.