Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Yadda Kiristoci Za Su Yi Nasara a Aurensu

Yadda Kiristoci Za Su Yi Nasara a Aurensu

‘Kowane ɗayanku shi yi ƙaunar matarsa kamar kansa; matan kuma ta ga kwarjinin mijinta.’—AFIS. 5:33.

WAƘOƘI: 87, 3

1. Ko da yake aure abin farin ciki ne, wane yanayi ne waɗanda suka yi aure za su fuskanta? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

SA’AD DA amarya da ango suka ga juna a ranar ɗaurin aurensu, suna yin murna sosai kamar su zuba ruwa a ƙasa su sha. A lokacin da suke fita zance, sun so juna sosai kuma yanzu suna shirye su yi aure kuma sun yi alkawari cewa za su kasance tare. Hakika, bayan sun yi aure, suna bukatar su yi wasu canje-canje don su kasance da haɗin kai a aurensu. Jehobah ne ya kafa aure kuma yana so ma’aurata su yi farin ciki kuma su yi nasara a aurensu. Shi ya sa kalmarsa take ɗauke da shawarwari game da aure. (Mis. 18:22) Amma kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya ce ma’aurata “za su sha wahala a cikin jiki” domin su ajizai ne. (1 Kor. 7:28) Ta yaya ma’aurata za su bi da waɗannan matsalolin? Kuma mene ne zai taimaka wa Kiristoci su yi nasara a aurensu?

2. Wace irin ƙauna ce ma’aurata za su yi wa juna?

2 Littafi Mai Tsarki ya bayyana muhimmancin ƙauna. Ya kamata ma’aurata su riƙa kula da juna kamar ƙwai, hakan shi ne (phi·liʹa a Helenanci). Eʹros tana nufin ƙaunar da take sa mata da miji su yi sha’awar juna. Stor·geʹ ƙauna ce tsakanin iyali kuma suna bukatar su kasance da wannan ƙaunar musamman idan suka haifi ’ya’ya. Amma (a·gaʹpe) wato ƙaunar da take cike da gaskiya da aminci, ita ce za ta sa ma’aurata su yi nasara. Shi ya sa manzo Bulus ya rubuta: “Kowane ɗayanku shi yi ƙaunar matatasa kamar kansa; matan kuma ta ga kwarjinin mijinta.”—Afis. 5:33.

ABIN DA YA KAMATA MA’AURATA SU YI

3. Wace irin ƙauna ce ya kamata ma’aurata su yi wa juna?

3 Bulus ya rubuta cewa: “Mazaje, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kristi kuma ya ƙaunaci ikilisiya, ya ba da kansa domin ta.” (Afis. 5:25) Mabiyan Yesu suna bukatar su ƙaunaci juna kamar yadda ya ƙaunace su. (Karanta Yohanna 13:34, 35; 15:12, 13.) Saboda haka, ma’aurata suna bukatar su so juna sosai da har za su iya sadaukar da ransu don juna. Amma saboda matsalar da suke fuskanta, ma’aurata suna iya cewa, “Allah ya kiyaye mu mutu domin juna.” Amma ku tuna cewa a·gaʹpe, ƙauna ce da ba ta son kai kuma tana “jimrewa da abu duka, tana gaskata abu duka, tana kafa bege ga abu duka, tana daurewa da abu duka.” Hakika, “ƙauna ba ta ƙarewa.” (1 Kor. 13:7, 8) Idan ma’aurata suka tuna da alkawarin da suka yi cewa za su ƙaunaci juna kuma su riƙe amana, hakan zai taimaka musu su yi aiki tare kuma su bi ƙa’idodin Jehobah don su warware duk wata matsalar da za su fuskanta.

4, 5. (a) Wane hakki ne miji yake da shi a cikin iyali? (b) Ta yaya ya kamata mace ta ɗauki shugabancin maigidanta? (c) Waɗanne canje-canje ne wasu ma’aurata suka su yi?

4 Manzo Bulus ya bayyana hakkin da ma’aurata suke da shi. Ya ce: “Mataye, ku yi zaman biyayya da maza naku, kamar ga Ubangiji. Gama miji kan mata yake, kamar yadda Kristi kuma kan ikilisiya ne.” (Afis. 5:22, 23) Hakan ba ya nufin cewa miji ya fi matarsa daraja. Maimakon haka, zai taimaka wa matar ta cika hakkin da Allah ta ba ta sa’ad da ya ce: “Ba ya yi kyau ba mutum shi kasance shi ɗaya; sai in yi masa mataimaki mai-dacewa da shi.” (Far. 2:18) Kamar yadda Kristi a matsayinsa na shugaban “ikilisiya” ya ƙaunaci mabiyansa, haka ma ya kamata Kiristoci mazaje su bi da matansu cikin ƙauna. Idan miji ya ƙaunaci matarsa, zai yi wa matar sauƙi ta daraja shi kuma ta taimaka masa. Ƙari ga haka, za ta yi hakan da farin ciki.

5 Wata ’yar’uwa mai suna Cathy [1] wadda ta auri Fred ta ce: “Sa’ad da nake budurwa, ba na dogara ga kowa kuma ina kula da kaina. Amma da na yi aure, ina bukatar na yi wasu canje-canje kuma in riƙa dogara ga maigidana. Hakan ba shi da sauƙi amma yin abubuwa yadda Jehobah yake so, ya sa mun kusaci juna sosai.” Fred ya ce: “Bayan na yi aure, tsai da shawara bai da sauƙi, domin ina bukatar in yi la’akari da ra’ayina da na matata a kan wani batu. Amma na nemi taimakon Jehobah kuma ina saurarar shawarar da matata take bayarwa. Hakan ya sa yanke shawara yana yi mini sauƙi kuma yana sa in ji cewa ni da matata mun dace da juna sosai!”

6. Ta yaya ƙauna za ta taimaka wa ma’aurata sa’ad da suke fuskantar matsala?

6 Domin aure ya kasance da ƙarfi sosai, ma’aurata suna bukatar su riƙa “haƙuri da juna” da kuma “gafarta ma juna.” Hakika, dukansu sukan yi kuskure. Amma idan hakan ya faru, suna iya koyan darasi daga kuskuren da suka yi kuma su gafarta wa juna. Ƙari ga haka, suna bukatar su nuna ƙaunar da ba ta son kai domin ita ce “magamin kamalta.” (Kol. 3:13, 14) Ban da haka, “ƙauna tana da yawan haƙuri, tana da nasiha . . . ba ta yin nukura.” (1 Kor. 13:4, 5) Idan akwai matsala, ma’aurata suna bukatar su magance matsalar da wuri kuma kada su bar rana ta faɗi suna fushi da juna. (Afis. 4:26, 27) Ba shi da sauƙi mutum ya ce “Yi haƙuri don abin da na yi.” Amma faɗin hakan yana nuna cewa mutumin mai tawali’u ne da kuma gabagaɗi. Ƙari ga haka, yana taimakawa wajen magance matsaloli kuma yana sa ma’aurata su kusaci juna sosai.

KA TARAIRAYI MATARKA KAMAR ƘWAI

7, 8. (a) Wace shawara ce Littafi Mai Tsarki ya bayar game da yin jima’i a aure? (b) Me ya sa ma’aurata suke bukatar su riƙa tarairayar juna?

7 Littafi Mai Tsarki ya ba da shawarar da za ta taimaka wa ma’aurata su kasance da ra’ayin da ya dace game da yin jima’i. (Karanta 1 Korintiyawa 7:3-5.) Yana da muhimmanci ma’aurata su riƙa lura da yadda suke ji a jikinsu kuma su biya bukatar juna. Idan miji ba ya tarairayar matarsa kamar ƙwai, zai yi mata wuya ta ji daɗin yin jima’i. An umurci mazaje su bi da matansu “bisa ga sani.” (1 Bit. 3:7) Saboda haka, bai kamata a tilasta yin jima’i ba. Ko da yake namiji yakan riga mace soma jin sha’awa, amma ya kamata su biyun su kasance a wannan yanayin.

8 Ko da yake Littafi Mai Tsarki bai ba da takamamiyar doka game da irin wasa ta yin sha’awar juna da ma’aurata za su riƙa yi ba, amma ya ambata yadda wasu suka nuna soyayya. (W. Waƙ. 1:2; 2:6) Ya kamata ma’aurata su riƙa tarairayar juna sosai.

9. Me ya sa bai dace mu yi sha’awar wadda ba abokiyar aurenmu ba?

9 Idan muna ƙaunar Allah sosai da kuma maƙwabtanmu, hakan zai hana mu barin wani abu ya ɓata aurenmu. Wasu sun ɓata aurensu ta wajen kallon hotunan batsa. Ya kamata mu guji kallon hotunan batsa da kuma lalata. Bai kamata mu riƙa yin kwarkwasa da wanda ba mijinmu ko matarmu ba. Ya kamata mu tuna cewa Jehobah ya san tunaninmu da kuma ayyukanmu. Sanin hakan zai taimaka mana mu guji yin duk wani abin da zai ɓata masa rai kuma mu kasance da aminci ga abokan aurenmu.—Karanta Matta 5:27, 28; Ibraniyawa 4:13.

SA’AD DA MA’AURATA SUKE FUSKANTAR MATSALA

10, 11. (a) Me ya sa ake yawan kashe aure a yau? (b) Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da rabuwa? (c) Mene ne zai hana ma’aurata rabuwa da juna?

10 Idan ma’aurata suka kasa magance matsalolin da suke fuskanta, suna iya yin tunani cewa rabuwa ko kuma kashe aure shi ne kawai mafita. A wasu ƙasashe, yawanci ma’aurata suna kashe aurensu. Hakan ba ya yawan faruwa a cikin ikilisiyar Kirista amma mutanen Allah da yawa suna fuskantar matsaloli a aurensu.

11 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada matan ta rabu da mijinta idan kuwa ta rigaya ta bar shi, ta zauna haka nan ba miji, ko kuwa ta sulhunta da mijinta; mijin kuma kada ya rabu da matarsa.” (1 Kor. 7:10, 11) Kada ku ɗauki rabuwa kamar ƙaramin al’amari. Ko da yake wasu ma’aurata suna iya ganin cewa idan suka rabu, hakan zai magance matsalar da suke fuskanta amma yin hakan yana da haɗari sosai. Yesu ya ce namiji zai bar iyayensa kuma ya manne wa matarsa. Bayan haka, sai ya ce: “Abin da Allah ya gama fa, kada mutum shi raba.” (Mat. 19:3-6; Far. 2:24) Hakan yana nufin cewa bai kamata ma’aurata su raba abin da Allah ya haɗa ba. Jehobah ba ya so ma’aurata su rabu da juna. (1 Kor. 7:39) Muna bukatar mu tuna cewa dukanmu za mu gaya wa Jehobah dalilin da ya sa muka yi wasu abubuwa. Idan muka tuna da hakan, za mu yi saurin magance duk wata matsalar da muke fuskanta kafin matsalar ta zama da tsanani.

12. Mene ne zai iya sa ma’aurata su yi tunanin rabuwa da juna?

12 Me ya sa wasu ma’aurata suke fuskantar matsala a aurensu? Domin ba su sami abin da suke zato a auren ba. Hakan yana sa su baƙin ciki kuma su riƙa fushi da kansu da kuma abokin aurensu. A yawancin lokaci, yadda aka reni mutane ya bambanta sosai kuma hakan yana iya jawo matsala. Wani abin da yake kawo matsala kuma shi ne batun kuɗi da yadda za a bi da surukai da kuma yadda za a tarbiyyartar da yara. Amma ya kamata Kiristoci su bar Allah ya ja-gorance su wajen magance irin waɗannan matsaloli.

13. Waɗanne dalilai ne za su iya sa ma’aurata su rabu?

13 A wani lokaci, zai dace ma’aurata su rabu da juna. Wasu sun rabu da mazansu don mijin ya ƙi biyan bukatun iyalin da gangan. Wasu matan sun rabu da mazansu don suna cin zalinsu ko kuma sun hana su bauta wa Jehobah. Zai dace Kiristocin da suke fuskantar matsala a aurensu su nemi taimakon dattawa. Waɗannan ’yan’uwan za su iya taimaka wa ma’aurata su bi shawarar da Littafi Mai Tsarki ya bayar game da aure. Ya kamata mu roƙi Jehobah ya ba mu ruhunsa kuma ya taimaka mana mu bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki sa’ad da muke fuskantar matsala a aurenmu. Ƙari ga haka, mu roƙe shi taimaka mana mu nuna halaye masu kyau.—Gal. 5:22, 23. [2]

14. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da waɗanda abokan aurensu ba sa bauta wa Jehobah?

14 Littafi Mai Tsarki ya ce yana da kyau ma’aurata su kasance tare ko da wani a cikinsu ba ya bauta wa Jehobah. Kuma ya ba da dalilai masu kyau da ya sa za su ci gaba da kasancewa tare. (Karanta 1 Korintiyawa 7:12-14.) An ‘tsarkake’ wanda ba ya bauta wa Jehobah domin matarsa tana bauta wa Jehobah. Duk ’ya’yan da suka haifa suna da “tsarki” a gaban Jehobah kuma za su iya more dangantaka da Jehobah. Bulus ya ce: “Ke mata, ina kin sani, ko za ki ceci mijinki? Kai fa miji, ina ka sani, ko za ka ceci matarka?” (1 Kor. 7:16) Da akwai Kiristoci da yawa da suka taimaka wa matansu ko mazansu su soma bauta wa Jehobah.

15, 16. (a) Wace shawara ce Littafi Mai Tsarki ya ba wa matan da mazajensu ba sa bauta wa Jehobah? (b) Mene ne matan da mijinta ba ya bauta wa Jehobah za ta yi idan yana so su rabu?

15 Manzo Bitrus ya ce mata su riƙa yi wa mazajensu ladabi da biyayya “domin ko da akwai waɗansu da ba su yin biyayya da magana, su rinjayu ban da magana saboda halayen matansu; suna lura da halayenku masu-tsabta tare da tsoro.” Maimakon ta riƙa magana game da imaninta koyaushe, matar aure tana iya sa mijinta ya soma bauta wa Jehobah idan tana da ladabi da kuma sauƙin kai. Hakan shi ne “abin da ke da tamani mai-girma a gaban Allah.”—1 Bit. 3:1-4.

16 Amma idan mijin yana so su rabu fa? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Idan marar bangaskiyan zai rabu, bar shi ya rabu; ɗan’uwa ko ’yar’uwa ba su cikin bauta in haka nan ne: Amma Allah ya kirawo mu cikin salama.” (1 Kor. 7:15) Idan wanda ba ya bauta wa Jehobah yana so ya rabu da matarsa, ba wajibi ba ne a tilasta masa ya ci gaba da zama da ita ba. Amma hakan ba ya nufin cewa za ta iya sake yin aure. Wataƙila rabuwar da suka yi zai sa su kasance da kwanciyar hankali. Matar tana iya kasancewa da bege cewa mijinta zai dawo kuma su ci gaba da zama tare, wataƙila ma ya soma bauta wa Jehobah.

ABIN DA YA FI MUHIMMANCI A AURE

Ma’aurata za su yi farin ciki sosai idan suka fi mai da hankali ga ibadarsu ga Jehobah (Ka duba shafi na 17)

17. Mene ne ya kamata ma’aurata su fi mai da wa hankali?

17 Muna rayuwa a “kwanaki na ƙarshe.” Saboda haka, muna fuskantar “miyagun zamanu.” (2 Tim. 3:1-5) Duk da haka, idan muka ƙulla dangantaka ta kud da kud da Jehobah, hakan zai taimaka mana mu guji yin abubuwan da mutanen duniya suke yi. Bulus ya ce: “An gajertar da kwanaki, domin nan gaba waɗanda suke da mata su yi kamar ba su da su, . . . waɗanda suke moron duniya, kamar ba sa cika moriyarta.” (1 Kor. 7:29-31) Bulus ba ya nufin cewa kada ma’aurata su kula da juna. Amma yana nufin cewa ya kamata bautar Jehobah ta kasance abu mafi muhimmanci a rayuwarsu musamman a wannan kwanaki na ƙarshe.—Mat. 6:33.

18. Me ya sa ma’aurata za su iya kasancewa da farin ciki kuma su yi nasara a aurensu?

18 Muna rayuwa a miyagun zamani kuma ma’aurata da yawa suna kashe aurensu. Duk da haka, za mu iya kasancewa da farin ciki kuma mu yi nasara a aurenmu. Hakika, idan ma’aurata suka ci gaba da yin tarayya da mutanen Allah, suka bi shawarar Littafi Mai Tsarki kuma suka bar ruhun Jehobah ya ja-gorance su, hakan zai hana su raba “abin da Allah ya gama” ba.—Mar. 10:9.

^ [1] (sakin layin na 5) An canja wasu sunaye.

^ [2] (sakin layi na 13) Ka duba ratayen nan “Ra’ayin Littafi Mai Tsarki Game da Kisan Aure da Kuma Rabuwa,” a cikin littafin nan “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah,” shafuffuka na 219 zuwa 221.