Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Me Ya Sa Jehobah Ya Kafa Aure?

Me Ya Sa Jehobah Ya Kafa Aure?

‘Ubangiji Allah kuma ya ce, ba kyau mutum shi kasance shi ɗaya; sai in yi masa mataimaki mai-dacewa da shi.’—FAR. 2:18.

WAƘOƘI: 36, 11

1, 2. (a) Wane ne ya kafa aure? (b) Mene ne Adamu da Hauwa’u ya kamata su sani game da aure? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

AURE abu ne mai muhimmanci a rayuwarmu. Shi ya sa sanin dalilin da ya sa Jehobah ya ƙafa aure zai iya sa mu kasance da ra’ayin da ya dace game da aure, kuma hakan zai taimaka mana mu more albarkar da aure yake kawowa. Bayan Allah ya halicci Adamu, ya kawo masa dukan dabbobi don ya sa musu suna, amma shi Adamu ba shi da “mataimaki mai-dacewa da shi.” Allah ya sa Adamu ya yi barci mai zurfi, sai ya ɗauki ɗaya daga cikin haƙarƙarinsa ya halicci mace da shi, kuma ya kawo ta wurin Adamu. (Karanta Farawa 2:20-24.) Hakika wannan ya nuna mana cewa Jehobah ne ya kafa aure.

2 Yesu da kansa ya ba da tabbaci cewa Jehobah ne ya ce: “Saboda wannan namiji za ya bar ubansa da uwatasa shi manne wa matatasa, su biyu kuwa za su zama nama ɗaya.” (Mat. 19:4, 5) Jehobah ya yi amfani da haƙarƙarin Adamu kuma ya halicce macen, hakan ya nuna musu cewa suna bukatar su kasance da dangantaka ta kud da kud. Jehobah  ba ya so mata da miji su kashe aurensu ko kuma maza su auri mata da yawa.

AURE YA CIKA NUFIN JEHOBAH

3. Mene ne ainihin dalilin da ya sa Jehobah ya kafa aure?

3 Adamu ya yi farin cikin samun matarsa wanda daga baya ya kira ta Hauwa’u. A matsayinta na wadda ta ‘dace’ da shi, da za ta zama ‘mataimakiyarsa,’ kuma za su ci gaba da rayuwa cikin farin ciki a matsayinsu na mata da miji. (Far. 2:18) Ainihin dalilin da ya sa Jehobah ya kafa aure shi ne don duniya ta cika da mutane. (Far. 1:28) Ko da yake suna ƙaunar iyayensu, yaran za su yi aure don su ma su sami nasu iyalin. Ƙari ga haka, ’yan Adam za su cika duniya kuma su sa ta zama aljanna.

4. Mene ne ya faru da aure na farko?

4 Auren Adamu da Hauwa’u ya taɓarɓare domin sun yi wa Jehobah rashin biyayya. “Tsohon macijin” nan Shaiɗan Iblis, ya ruɗi Hauwa’u kuma ta yarda cewa idan ta ci daga “itacen sanin nagarta da mugunta” za ta san abin da yake da kyau da marar kyau. Ba ta nemi shawarar mijinta ba a matsayinsa na shugaban iyalin kafin ta ci ’ya’ya itacen. Ƙari ga haka, maimakon Adamu ya yi biyayya ga Allah, sai ya saurari matarsa kuma ya ci ’ya’yan itacen tare da ita.—R. Yoh. 12:9; Far. 2:9, 16, 17; 3:1-6.

5. Me za mu iya koya daga misalin Adamu da Hauwa’u?

5 Sa’ad da Jehobah ya tambaye su dalilin da ya sa suka yi rashin biyayya, Adamu ya ɗora wa matarsa laifi kuma ya ce: “Macen da ka ba ni domin ta zauna tare da ni, ita ta ba ni daga itacen, ni kuwa na ci.” Hauwa’u kuma ta ɗora wa macijin laifi cewa shi ne ya ruɗe ta. (Far. 3:12, 13) Adamu da matarsa ba su ba da ƙwararan hujjar yin rashin biyayya ba. Saboda haka, Jehobah ya hukunta su. Hakika, misalinsu gargaɗi ne a gare mu. Idan ma’aurata suna so su yi nasara a aurensu, wajibi ne kowannensu ya yi biyayya ga Jehobah.

6. Ka bayyana littafin Farawa 3:15.

6 Duk da cewa Shaiɗan ya ruɗi Adamu da Hauwa’u a lambun Adnin, Jehobah ya sa ’yan Adam su kasance da bege a annabci na farko da ya yi a cikin Littafi Mai Tsarki. (Karanta Farawa 3:15.) ‘Zuriyar’ matar zai murƙushe Shaiɗan wanda ya yi tawaye da Allah. Ta hakan Jehobah ya nuna wa ’yan Adam cewa yana da dangantaka na musamman da mala’ikunsa masu yawa da suke masa hidima a sama. Nassosi sun bayyana cewa daga cikin ƙungiyarsa mai kama da mata a gare shi, Jehobah zai turo wanda zai “ƙuje” Iblis. Ƙari ga haka, wannan zuriyar zai sa ’yan Adam masu biyayya su more rayuwa da iyayenmu na farko suka ɓatar, wato yin rayuwa har abada a duniya kamar yadda Jehobah ya nufa a dā.—Yoh. 3:16.

7. (a) Ta yaya tawayen da Adamu da Hauwa’u suka yi ya shafi zaman aure? (b) Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce ma’aurata su riƙa yi?

7 Tawayen da Adamu da Hauwa’u suka yi ya shafi aurensu da kuma na ’ya’yansu. Alal misali, Hauwa’u da kuma mata gabaki ɗaya za su yi naƙuda sosai a lokacin haihuwa. Ban da haka, mata za su so mazansu sosai amma maza za su mallaki matansu, wasu ma za su riƙa wulaƙanta matansu kamar yadda muke gani a yau. (Far. 3:16) Littafi Mai Tsarki ya ce wajibi ne magidanta su yi shugabanci a hanya  mai kyau. Ƙari ga haka, mata suna bukatar su yi biyayya ga shugabancin mazajensu. (Afis. 5:33) Idan ma’aurata suna da haɗin kai, za su iya kawar da duk wata matsalar da za ta taso a tsakaninsu.

DAGA ZAMANIN ADAMU ZUWA LOKACIN RIGYAWA

8. Daga lokacin Adamu zuwa lokacin Rigyawa, yaya mutane suke aure?

8 Adamu da Hauwa’u sun haifi ’ya’ya kafin su mutu saboda zunubinsu. (Far. 5:4) Kayinu ɗansu na fari ya auri ɗaya daga cikin ’yan’uwansa mata. Lamek wanda zuriyar Kayinu ne, shi ne mutum na farko da aka ce ya auri mata biyu. (Far. 4:17, 19) Daga lokacin Adamu zuwa zamanin Nuhu, mutane ƙalilan ne aka ambata cewa suna bauta wa Jehobah. Habila da Anuhu da kuma Nuhu da iyalinsa suna cikinsu. Littafi Mai Tsarki ya ce, a zamanin Nuhu “’ya’yan Allah suka ga ’yan mata na mutane kyawawa ne; suka ɗauko wa kansu mata dukan waɗanda suka zaɓa.” Wannan saduwar da mala’ikun suka yi da matan ’yan adam ta haifar da yara ƙattai masu mugun ƙarfi. Saboda haka, “muguntar mutum ta yi yawa cikin duniya, kuma kowacce shawara ta tunanin zuciyarsa mugunta ce kaɗai kullayaumi.”—Far. 6:1-5.

9. Mene ne Jehobah ya yi wa mugayen mutane a zamanin Nuhu, kuma wane darasi ne muka koya daga hakan?

9 A zamanin Nuhu Jehobah ya kawo Rigyawa da ta hallaka mugayen mutane. A wannan lokacin mutane sun shagala da ayyukansu na yau da kullum, har da yin aure kuma hakan ya sa ba su ɗauki abin da Nuhu “mai-shelan adalci” yake cewa game da Rigyawa da muhimmanci ba. (2 Bit. 2:5) Yesu ya ce zamaninmu zai zama kamar na Nuhu. (Karanta Matta 24:37-39.) A yau, mutane da yawa ba sa so su saurari bisharar Mulkin Allah da ake yi a dukan duniya kafin a halaka wannan mugunwar zamani. Wane darasi ne hakan ya koya mana? Bai kamata mu bar wasu abubuwa kamar aure da kuma rainon yara su kasance da muhimmanci a rayuwarmu har su sa mu manta cewa ranar Jehobah tana gabatowa.

DAGA LOKACIN RIGYAWA ZUWA ZAMANIN YESU

10. (a) A al’adu da yawa, yaya mutane suke ɗaukan ayyukan lalata? (b) Ta yaya Ibrahim da Saratu suka kafa misali mai kyau a aurensu?

10 A zamanin Nuhu, mutane sun auri mata da yawa, amma Nuhu da ’ya’yansa uku ba su yi hakan ba. Yin zina ya zama gama gari, har ya zama al’adar wasu addinai. Ibrahim da Saratu sun yi biyayya ga Allah kuma suka ƙaura suka koma Kan’ana, amma mutanen ƙasar ba sa daraja aure don ayyukansu na lalata. Ƙari ga haka, Jehobah ya halaka Saduma da Gwamrata domin tsananin lalata na mutanen biranen. Amma Ibrahim ya shugabanci iyalinsa a hanyar da ta dace, kuma Saratu ta kafa misali mai kyau ta wajen yi wa mijinta biyayya. (Karanta 1 Bitrus 3:3-6.) Ibrahim ya tabbata cewa ɗansa Ishaku ya auri wadda take bauta wa Jehobah. Haka ma Ishaku ya yi wa ɗansa Yakubu, kuma ’ya’yan Yakubu sun zama kakannin ƙabilu 12 na Isra’ila.

11. Ta yaya Dokar da aka ba da ta hannun Musa ta kāre Isra’ilawa?

11 Daga baya, Jehobah ya yi wa al’ummar Isra’ila alkawari. Dokar da aka ba da ta hannun Musa ta taimaka wajen kāre maza da matansu a ibadarsu ga Jehobah. Alal misali, an kafa  dokoki game da aure, har da auren mace fiye da ɗaya, kuma dokar ta hana Isra’ilawa daga auren waɗanda ba sa bauta wa Jehobah. (Karanta Kubawar Shari’a 7:3, 4.) Dattawa suna taimaka wa ma’aurata idan suna fuskantar matsala a aurensu. Ƙari ga haka, da akwai dokokin da aka kafa game da cin amana da kishi da kuma zargi. Ko da yake an amince da kashe aure amma an kafa dokokin da za su kāre miji ko matar. Mutum zai iya sakin matarsa idan ta yi “wani abin da ba daidai ba.” (K. Sha. 24:1) Ba a bayyana mene ne “abin da ba daidai ba” da zai sa mutum ya saki matarsa, amma mun san cewa ba ƙananan kurakurai ba ne.—Lev. 19:18.

KADA MA’AURATA SU CI AMANAR JUNA

12, 13. (a) Mene ne wasu magidanta suke yi wa matansu a zamanin Malakai? (b) Mene ne zai faru idan wani ɗan’uwa ya gudu da matar wani?

12 A zamanin annabi Malakai, magidanta da yawa na Yahudawa sun saki matansu a kan hujjojin da ba su dace ba. Irin waɗannan mazajen suna sakin matansu wataƙila don su auri ’yammata ko kuma waɗanda ba sa bauta wa Jehobah. Sa’ad da Yesu yake duniya, Yahudawa suna sakin matansu “a kan kowane dalili.” (Mat. 19:3, Littafi Mai Tsarki) Jehobah Allah ya ƙi jinin irin wannan kashe auren.—Karanta Malakai 2:13-16.

13 A yau, mutanen Jehobah ba sa amincewa da cin amana a aure. Amma idan wani ɗan’uwa da ya yi baftisma ya gudu da matar wani, kuma ya aure ta bayan ya saki matarsa ta dā kuma fa? Za a yi masa yankan zumunci idan bai tuba ba, don a tsarkake ikilisiyar. (1 Kor. 5:11-13) Ƙari ga haka, yana bukatar ya ‘yi aikin da zai nuna ya tuba’ kafin a dawo da shi. (Luk. 3:8, LMT; 2 Kor. 2:5-10) Ko da yake ba a faɗi yawan lokacin da zai wuce kafin a dawo da mutumin da aka yi masa yankan zumunci ba, zai iya ɗaukan shekara guda ko fiye da hakan kafin mai zunubin ya nuna cewa ya tuba da gaske. Ko da an dawo da mutumin, wajibi ne ya nuna ko ya tuba da gaske “a gaban kursiyin shari’a na Allah.”—Rom. 14:10-12; ka duba Hasumiyar Tsaro na 15 ga Nuwamba, 1979, shafuffuka na 31-32.

YADDA KIRISTOCI SUKE AURE

14. Mene ne Dokar da aka ba da ta hannun Musa ta cim ma?

14 Dokar da aka ba da ta hannun Musa ta yi wa Isra’ilawa ja-gora fiye da shekaru 1,500. Kuma ta taimaka wa mutanen Allah su bi ƙa’idodin Allah don su magance matsalolin da za su iya tasowa a iyali. Ƙari ga haka, ta yi musu ja-gora har zuwan Almasihu. (Gal. 3:23, 24) Sa’ad da Yesu ya mutu, an daina bin Dokar da aka ba da ta hannun Musa kuma Allah ya ƙafa wani sabon tsari. (Ibran. 8:6) Hakan ya sa Kiristoci ba sa bin wasu abubuwan da Dokar da aka ba da ta hannun Musa ta amince da su.

15. (a) Wace ƙa’ida ce ake bi a ikilisiyar Kirista a batun aure? (b) Waɗanne abubuwa ne ya kamata ma’aurata su yi la’akari da shi idan suna so su kashe aurensu?

15 Sa’ad da wasu Farisawa suka yi wa Yesu tambaya game da kashe aure, ya ce ko da yake Dokar da aka ba da ta hannun Musa ta ƙyale su su riƙa kashe aure amma “ba haka yake a farko ba.” (Mat. 19:6-8) Amsar da Yesu ya ba da ta nuna cewa lokaci ya yi da Kiristoci za su sake soma bin dokar da Allah ya  ba da a lambun Adnin. (1 Tim. 3:2, 12) Ya kamata ma’aurata su manne wa juna kuma su sa ƙaunar Allah da kuma juna ta ƙarfafa aurensu. Zina ce kawai za ta sa ma’aurata su kashe aurensu kuma hakan zai ba wanda aka ci amanarsa ’yancin sake yin aure. (Mat. 19:9) Hakika, mutum zai iya gafarta wa wadda ta yi zina amma ta tuba, kamar yadda annabi Hosiya ya gafarta wa matarsa Gomer sa’ad da ta yi zina. Hakazalika, Jehobah ya gafarta wa Isra’ilawa da suka tuba bayan sun bauta wa wasu allolin ƙarya. (Hos. 3:1-5) Ƙari ga haka, idan wani ya san cewa matarsa ta yi zina kuma ya soma jima’i da ita, hakan ya nuna cewa ya gafarta mata kuma ba zai sake ta ba.

16. Mene ne Yesu ya ce game da waɗanda suka amince ba za su yi aure ba?

16 Bayan Yesu ya ce zina ce kawai za ta sa ma’aurata su kashe aurensu, sai ya ambata waɗanda suka amince ba za su yi aure ba. Kuma ya daɗa cewa wanda ya san zai iya yin hakan, ya yi. (Mat. 19:10-12) Mutane da yawa sun ƙi yin aure domin ba sa son wani abin da zai raba hankalinsu a bautar su ga Jehobah. Ya kamata a yaba musu sosai.

17. Mene ne zai taimaka wa mutum ya tsai da shawara ko zai yi aure?

17 Mutum ne da kansa zai yanke shawara ko zai yi aure ko ba zai yi ba. Duk da cewa manzo Bulus ya ba da shawara cewa mutum zai iya zama ba tare da ya yi aure ba, ya ce: “Amma, saboda fasikanci, bari kowanne mutum shi kasance da matar kansa, kowacce mace kuma da mijin kanta.” Kuma ya ƙara cewa: “Idan ba su da daurewa, su yi aure; gama da [“sha’awa ta sha kan mutum,” NW] gwamma a yi aure.” Hakika, yin aure zai taimaka wa mutum ya guji barin sha’awarsa ta sa shi yin wasa da al’aura don ta da sha’awa ko kuma ya yi lalata ba. Ƙari ga haka, ya kamata waɗanda suke so su yi aure su yi la’akari da shekarunsu, shi ya sa Bulus ya ce: ‘Idan kowane mutum yana tsammani yana yin abin da bai dace ga [“budurcinsa,” NW], idan ya riga ya wuce lokaci, idan hali ya nufa haka, ya yi abin da yake so; bai yi zunubi ba; bari ya yi aure.’ (1 Kor. 7:2, 9, 36; 1 Tim. 4:1-3) Amma kada mutum ya bar sha’awar yin jima’i da matasa suke fuskanta ya sa shi yin aure domin a lokacin wataƙila bai manyanta sosai da zai ɗauki hakkin yin aure ba.

18, 19. (a) A cikin ikilisiyar Kirista, su wane ne ya dace su auri juna? (b) Mene ne za a tattauna a talifi na gaba?

18 Waɗanda suka keɓe kansu ga Jehobah kuma suna ƙaunarsa da dukan zuciyarsu ne ya dace su auri juna. Ƙari ga haka, kafin su yi aure ya kamata su ƙaunaci juna sosai. Hakika, za su sami albarka idan suka yi aure “cikin Ubangiji” kaɗai. (1 Kor. 7:39) Da zarar sun yi aure, za su yi nasara a aurensu idan suka bi shawarar da Littafi Mai Tsarki ya ba da game da aure.

19 A talifi na gaba, za a tattauna wasu abubuwa daga Nassi da za su taimaka wa ma’aurata su bi da ƙalubalen da ke tattare da zaman aure a wannan “kwanaki na ƙarshe” wadda maza da mata da yawa suke da halayen da ke jawo matsala a aure. (2 Tim. 3:1-5) A cikin Littafi Mai Tsarki, Jehobah ya ba mu shawarwarin da za su taimaka mana mu yi nasara kuma mu yi farin ciki a aurenmu. Hakan zai taimaka mana mu ci gaba da bin hanyar da za ta kai mu ga samun rai na har abada.—Mat. 7:13, 14.