Koma ka ga abin da ke ciki

Fahimtar Littafi Mai Tsarki—Me Muke Bukata?

Fahimtar Littafi Mai Tsarki—Me Muke Bukata?

Amsar da Littafi Mai Tsarki ya ba da

 Littafi Mai Tsarki ya bayyana abin da kake bukata don ka fahimce shi. Ko yaya iliminka yake, maganar Allah da ke cikin Littafi Mai Tsarki “ba ta fi ƙarfinka ba” kuma “ba ta kuwa da nisa.”—Kubawar Shari’a 30:11.

Yadda za mu fahimci Littafi Mai Tsarki

  1.   Ka kasance da Halin Kirki. Ka amince cewa Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ce. Ka kasance da tawali’u, domin Allah ba ya son masu fahariya. (1 Tasalonikawa 2:13; Yakub 4:6) Amma fa, kada ka gaskata da abin da ka karanta kawai, Allah yana son ka yi amfani da ‘azancinka,’ wato yin tunani sosai.—Romawa 12:1, 2.

  2.   Ka yi addu’a don ka sami hikima. Littafin Misalai 3:5 ta ce: “Kada ka jingina ga naka fahimi.” Maimakon haka, ka ci gaba da ‘rokon Allah’ don ya ba ka hikimar fahimtar Littafi Mai Tsarki.—Yakub 1:5.

  3.   Ka yi nazari a kai a kai. Za ka amfana sosai idan ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai maimakon jifa-jifa.—Joshua 1:8.

  4.   Ka yi nazari a kan wani batu.

     Nazarta batu, wato bincika wani abin da Littafi Mai Tsarki ya ce, hanya ce mai kyau na koyan abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa. Ka soma da “darussa na farko” sai kuma ka “ci gaba da koyan abubuwa masu zurfi.” (Ibraniyawa 6:1, 2, Juyin Easy-to-Read) Za ka ga cewa nassosi suna jituwa da kuma bayana juna, har ma da wurare masu “wuyan ganewa.”—2 Bitrus 3:16.

  5.   Ka nemi taimako daga wasu. Littafi Mai Tsarki ya karfafa mu mu nemi taimako wajen wasu don mu fahimci Littafi Mai Tsarki. (Ayyukan Manzanni 8:30, 31) Shaidun Jehobah suna da tsarin koyar da Littafi Mai Tsarki kyauta. Kamar Kiristoci na farko, suna amfani da Nassosi don su taimaka wa mutane su fahimci ainihin abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa.—Ayyukan Manzanni 17:2, 3.

Abubuwan da ba ka bukata

  1.   Basira ko ilimi sosai. Manzannin Yesu 12 sun fahimci Nassosi kuma sun koya wa wasu, ko da yake ana daukan manzannin cewa “marasa karatu ne.”—Ayyukan Manzanni 4:13.

  2.   Za ka iya koyan abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa kyauta. Yesu ya gaya wa almajiransa: “Kyauta kuka karba, sai ku bayar kyauta.”—Matta 10:8.