Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 15

Yesu “Ya Kafa Shari’a ta Gaskiya Cikin Duniya”

Yesu “Ya Kafa Shari’a ta Gaskiya Cikin Duniya”

1, 2. A wane lokaci ne Yesu ya fusata, kuma me ya sa?

YESU ya fusata—da kyakkyawar hujja. Watakila ya yi maka wuya ka yi tunaninsa a wannan hanyar, domin mutum ne mai tawali’u. (Matta 21:5) Ya kasance da cikakken kame kai, domin fushinsa na adalci ne. * Amma menene ya sa wannan mutum mai son lumana ya fusata? Batun rashin adalci ne mai tsanani.

2 Yesu yana kaunar haikali da yake Urushalima a zuciyarsa. A dukan duniya shi ne kawai wuri mai tsarki da aka kebe ga bautar Ubansa na samaniya. Yahudawa daga kasashe da yawa suna tafiya mai nisa su je bauta a wurin. Har mutane na Al’ummai masu tsoron Allah, suna zuwa farfajiyar haikalin da aka kebe domin amfaninsu. Amma da farkon hidimarsa, Yesu ya shiga cikin filin haikalin ya ga abin da yake da ban kyama. Duba, wurin ya fi kama da kasuwa fiye da gidan bauta! Ya cika da dillalai da masu canja kudi. Amma, ina rashin adalci a nan? Ga wadannan mutane, haikalin Allah wuri ne kawai na cutar mutane—har ma a yi musu fashi. Ta yaya?—Yohanna 2:14.

3, 4. Wace damfara ce ta hadama take faruwa a gidan Jehovah, me Yesu ya yi ya gyara al’amura?

3 Shugabannan addini sun kafa doka cewa sai dai da wata irin saba za a biya harajin haikali. Baki dole su canja kudinsu domin su samu irin wannan saba. Saboda haka, masu canja kudin sun kafa teburansu har cikin haikali, suna karbar la’ada daga kowane ciniki da aka yi. Wanda ma ya fi riba shi ne sayar da dabbobi. Baki wadanda suke so su mika hadaya za su iya sayan dabba a cikin gari, amma ma’aikatan haikali za su iya kin hadayarsu cewa bai cancanta ba. Amma, abin hadaya da aka saya a nan cikin filin haikali tabbatacce ne za a karba. Tun da mutanen suna cikin hannunsu, wani lokaci ’yan kasuwan suna yin tsada. * Wannan ya wuce kasuwanci. Ya zama fashi!

‘Ku kawar da wadannan daga wurin nan!’

4 Yesu ba zai kyale irin wannan rashin adalci ba. Wannan gidan Ubansa ne! Ya yi bulala ta igiya ya kori garken shanu da na tumaki daga haikalin. Sai ya tsallake zuwa wajen ’yan canja kudi ya jirkice teburansu. Ka yi tunanin tsaba suna watsewa a kan daben sassakakken duwatsu! Ya dokaci dillalan tantabaru: “Ku kawarda wadannan daga wurin nan”! (Yohanna 2:15, 16) Kamar dai babu wanda yake da gaba gadi ya yi adawa da wannan mutumin mai karfin zuciya.

“Ka Ga Da, Ka Ga Uba”

5-7. (a) Ta yaya rayuwar Yesu kafin ya zama mutum ya rinjayi yin shari’arsa, kuma menene za mu koya ta wajen nazarin misalansa? (b) Ta yaya Kristi ya yi yaki da rashin adalci da ya shafi ikon mallaka na Jehovah da kuma sunansa?

5 Hakika, dillalan sun sake dawowa. Bayan kamar shekara uku, Yesu ya sake magance wannan matsalar ta rashin adalci, a wannan lokaci ya dauko kalmomin Jehovah yana la’anta wadanda suka mayar da gidan Ubansa “kogon mafasa.” (Matta 21:13; Irmiya 7:11) Hakika, sa’ad da Yesu ya ga damfara ta hadama na mutanen da kuma kazantar da haikalin Allah, ya ji kamar dai yadda Ubansa ya yi. Kuma ba abin mamaki ba ne! Domin cikin shekaru miliyoyi marasa iyaka, Uba na samaniya ya koyar da Yesu. Saboda haka, ya cika da shari’a irin na Jehovah. Ya zama rayayyen misali na furcin nan, “Ka ga da, ka ga uba.” Saboda haka, idan muna so mu fahimci halin Jehovah na shari’a, hanya mafi kyau ita ce mu yi bimbini bisa misalan Yesu Kristi.—Yohanna 14:9, 10.

6 Dan Allah makadaici yana wajen sa’ad da Shaidan ya kira Jehovah Allah makaryaci, kuma ya tuhumi adalcin Sarautarsa. Wannan jafa’i ne na kai tsaye! Dan kuma ya ji Shaidan ya kalubalanta cewa babu wanda zai bauta wa Jehovah ba tare da son kai ba, cikin kauna. Wadannan tuhuma babu shakka sun bata wa Dan mai adalci rai. Babu shakka ya yi farin ciki da ya sani cewa shi yake da babban matsayi wajen gyara wannan al’amari! (2 Korinthiyawa 1:20) Ta yaya zai yi wannan?

7 Kamar yadda muka koya a Babi na 14, Yesu Kristi ya bayar da amsa ta karshe, cikakkiya ga tuhuma da take bata amincin halittun Jehovah. Yesu ya kafa tushen daukaka ikon mallaka na Jehovah kuma ya tsarkakke sunansa. Tun da shi ne Shugaba na Jehovah, Yesu zai kafa shari’a ta Allah a dukan sararin samaniya. (Ayukan Manzanni 5:31) Rayuwarsa a duniya haka nan ta nuna shari’a ta Allah. Jehovah ya ce game da shi: “Zan sa Ruhuna a bisansa, za shi furtadda shari’a ga Al’ummai.” (Matta 12:18) Ta yaya Yesu ya cika wadannan kalmomi?

Yesu Ya Bayyana ‘Abin da Shari’a Take Nufi’

8-10. (a) Ta yaya al’adar baka ta addinin Yahudawa ta daukaka kyama ga wadanda ba Yahudawa ba da kuma mata? (b) Ta yaya dokokin baka ta mai da dokar Asabarci na Jehovah ta zama kaya?

8 Yesu ya yi kaunar Dokar Jehovah kuma ya rayu daidai da ita. Amma shugabannin addini na zamaninsa sun jujjuya Dokar kuma ba su yi amfani da ita daidai ba. Yesu ya ce musu: “Kaitonku, ku marubuta da Farisawa, masu-riya! . . . kun kyale matsaloli mafiya girma na Attaurat, shari’a, da jinkai da bangaskiya.” (Matta 23:23) Wadannan malaman Dokar Allah ba sa bayyana ‘abin da shari’a take nufi.’ Maimakon haka, suna bata shari’a ta Allah. Ta yaya? Ka ga wasu misalai ’yan kadan.

9 Jehovah ya umurci mutanensa su ware daga al’umman arna da suka kewaye su. (1 Sarakuna 11:1, 2) Amma, wasu shugabannan addini masu wawan-bi suka karfafa mutanen su yi kyamar dukan wadanda ba Yahudawa ba. Mishnah yana dauke da wannan dokar: “Kada a bar sa a masaukin mutanen al’ummai tun da ana zaton suna jima’i da dabba.” Irin wannan kiyayya ga dukan wadanda ba Yahudawa ba rashin adalci ne kuma bai jitu da ma’anar Dokar Musa ba. (Leviticus 19:34) Wasu dokokin mutane sun kaskantar da mata. Dokar baka ta ce ya kamata mace ta bi mijinta a baya, kar ta yi tafiya kafada da kafada da shi ba. An gargade namiji kada ya yi magana da mace a cikin jama’a ko idan matarsa ce! Kamar bayi, ba a ba mata damar su ba da shaida a kotu ba. Da akwai wata addu’a ma da maza suke yi wa Allah godiya domin cewa su ba mata ba ne!

10 Shugabannan addini sun binne Dokar Allah a karkashin dokoki da umurnan mutane. Alal misali, dokar Asabarci, ta hana aiki ne ranar Asabarci, ta kebe wannan ranar domin bauta, wartsakewa ta ruhaniya, da kuma hutu. Farisawan sun sa dokar ta yi nauyi. Sun dauka wa kansu fassarar abin da “aiki” yake nufi. Sun ware abubuwa 39 cewa aiki ne, kamar su girbi ko kuma farauta. Wadannan suna jawo tambayoyi marasa iyaka. Idan mutum ya kashe kuma a ranar Asabarci, yana farauta ne? Idan ya cika hannu da hatsi domin ya ci yayin da yake tafiya, yana girbi ne? Idan ya warkar da wanda yake ciwo, yana aiki ne? Wadannan tambayoyin an amsa su da dokoki da yawa.

11, 12. Ta yaya Yesu ya nuna adawarsa ga al’adun Farisawa wanda ba daga Nassosi ba?

11 A irin wannan yanayi ta yaya Yesu zai taimaki mutane su fahimci abin da shari’a take nufi? A koyarwarsa da kuma hanyar rayuwarsa ya karfafa wajen yin adawa da wadannan shugabannan addini. Da farko ka ga wasu cikin koyarwarsa. Ya la’anci dubban dokokinsu na mutane, yana cewa: “Kuna maida maganar Allah wofi ke nan saboda takalidinku wanda kuka bayar.”—Markus 7:13.

12 Yesu ya koyar cikin iko cewa Farisawan sun bata game da dokar Asabarcin—cewa, ba su fahimci gaba dayan ma’anar dokar ba. Almasihu, ya yi bayani, shi ne “ubangijin asabarci,” saboda haka yana da damar ya warkar da mutane a ranar Asabarci. (Matta 12:8) Domin ya nanata batun, ya yi warkarwa ta mu’ujiza a fili a ranar Asabarci. (Luka 6:7-10) Irin wannan warkarwa nuna abin da zai yi ne a dukan duniya a lokacin Sarautarsa ta Shekara Dubu. Alif din za ta zama ranar Asabarci ce mai girma, lokacin da dukan mutane masu aminci a karshe za su huta daga karnuka na wahala cikin zunubi da mutuwa.

13. Wace doka ce ta kahu a sakamakon hidimar Kristi na duniya, kuma ta yaya ta bambanta da wadda take gaba da ita?

13 Yesu kuma ya bayyana sarai abin da shari’a take nufi da sabuwar doka ta kahu, ‘dokar Kristi,’ bayan ya kammala hidimarsa ta duniya. (Galatiyawa 6:2) Ba kamar ta gaba da ita ba, Dokar Musa, wannan sabuwar doka galibi tana dangane ne, ba bisa jerin rubutaccen dokoki ba, amma bisa mizanai. Ko da yake ta kunshi wasu dokoki kai tsaye. Daya daga cikin wadannan Yesu ya kira, “sabuwar doka.” Yesu ya koyar da mabiyansa su yi kaunar juna kamar yadda ya yi kaunarsu. (Yohanna 13:34, 35) Hakika, kauna ta sadaukar da kai za ta zama halin dukan wadanda suke rayuwa bisa ‘dokar Kristi.’

Rayayyen Misali na Shari’a

14, 15. Ta yaya Yesu ya nuna cewa ya fahimci iyakacin ikonsa, kuma me ya sa wannan yake da ban karfafa?

14 Yesu ya yi fiye da koyarwa game da kauna. Ya rayu daidai da ‘dokar Kristi.’ An gani a tafarkin rayuwarsa. Ka ga hanyoyi uku da misalin Yesu ya bayyana sarai abin da shari’a take nufi.

15 Na farko, Yesu ya mai da hankali ya guji yin rashin adalci. Watakila ka lura cewa yawancin rashin adalci yana faruwa ne sa’ad da mutane ajizai suka zama masu taurin kai kuma suka zarce iyakar ikonsu. Yesu bai yi haka ba. A wani lokaci, wani mutum ya tunkari Yesu, kuma ya ce: “Malam, ka ce ma dan’uwana shi raba gadō da ni.” Me Yesu ya amsa? “Mutum, wanene ya sanya ni alkali ko mai-raba musu a bisanku?” (Luka 12:13, 14) Wannan ba abin mamaki ba ne? Fahimin Yesu, hukuncinsa, da kuma iyakar iko da Allah ya ba shi ya fi na kowane mutum a duniya; duk da haka, ya ki ya saka baki cikin wannan al’amari, tun da ba a ba shi ainihin ikon ya yi haka ba. Yesu ya san da iyakarsa ta wannan hanyar, har a cikin karnuka na rayuwarsa kafin ya zama mutum. (Yahuda 9) Hali ne mai kyau na Yesu, cikin tawali’u ya dogara ga Jehovah ya tsara abin da yake adalci.

16, 17. (a) Ta yaya Yesu ya nuna shari’a wajen wa’azin bisharar Mulkin Allah? (b) Ta yaya Yesu ya nuna cewa shari’arsa tana da jinkai?

16 Na biyu, Yesu ya nuna shari’a a hanyar da ya yi wa’azin bisharar Mulkin Allah. Bai nuna son zuciya ba. Maimakon haka, ya yi kokari ya isa wurin dukan ire-iren mutane, ko mai arziki ko matalauci. Akasin haka, Farisawan sun sallami matalauta, da kalma ta nuna kyama ʽam-ha·ʼaʹrets, ko “ ’yan iska.” Yesu da gaba gadi ya gyara wannan rashin adalci. Sa’ad da ya koya wa mutane bishara—ko kuma ma, idan ya ci abinci da mutanen, ko ciyar da su, ya warkar da su, ko kuma ya tashe su a matattu—ya daukaka shari’ar Allahn da yake so a kai ga ‘dukan ire-iren mutane.’ *1 Timothawus 2:4.

17 Na uku, shari’ar Yesu tana da jinkai kwarai. Ya yi kokari ya taimake masu zunubi. (Matta 9:11-13) Ya taimaki mutane da ba su da karfin kāre kansu. Alal misali, Yesu bai hada da shugabannan addini ba wajen daukaka rashin yarda da dukan mutane na Al’ummai ba. Cikin jinkai, ya taimaki kuma ya koyar da wasu cikin wadannan, ko da yake ainihi an aiko shi ga Yahudawa ne. Ya yarda ya tafiyar da warkarwa na sojan Roma, yana cewa: “Ko cikin Isra’ila ban iske bangaskiya da girma haka ba.”—Matta 8:5-13.

18, 19. (a) A wadanne hanyoyi ne Yesu ya daukaka darajar mata? (b) Ta yaya misalin Yesu ya taimaka mana muka ga nasaba da ke tsakanin gaba gadi da shari’a?

18 Hakazalika, Yesu bai yarda da yadda ake daukan mata ba. Maimakon haka, da gaba gadi ya yi abin da yake daidai. Matan Samariyawa an gaskata ba su da tsarki kamar matan mutane na Al’ummai. Duk da haka, Yesu bai yi wata wata ba wajen yi wa matar Basamariyar wa’azi a rijiyar Sukar. Hakika, ga wannan matar ne ma Yesu da farko ya bayyana kansa shi ne Almasihu da aka yi alkawarinsa. (Yohanna 4:6, 25, 26) Farisawan sun ce bai kamata a koya wa mata Dokar Allah ba, amma Yesu ya yi amfani da lokaci da kuzari wajen koyar da mata. (Luka 10:38-42) Kuma ko da yake al’ada ta gaskata cewa mata ba za a iya dogara cewa za su ba da tabbatacciyar shaida ba, Yesu ya daukaka mata da yawa da gatar kasancewa na farko su gan shi bayan ya tashi daga matattu. Har ya gaya musu su je su gaya wa almajiransa maza game da wannan aukuwa mai muhimmanci!—Matta 28:1-10.

19 Hakika, Yesu ya bayyana sarai abin da shari’a take nufi. A yawancin lokatai, ya yi hakan cikin hadari ga kansa. Misalin Yesu ya taimake mu mu ga cewa daukaka shari’a ta gaskiya tana bukatar gaba gadi. Daidai fa, aka kira shi “Zaki wanda shi ke na asalin kabilar Yahuda.” (Ru’ya ta Yohanna 5:5) Ka tuna cewa zaki alama ne na shari’a, mai gaba gadi. A nan gaba kadan, Yesu zai kawo shari’a mafi girma. A cikar ta gabaki daya zai kafa “shari’a ta gaskiya cikin duniya.”—Ishaya 42:4.

Sarki Almasihu Ya ‘Kafa Shari’a a Duniya’

20, 21. A zamaninmu, ta yaya Sarki Almasihu ya daukaka shari’a a dukan duniya da kuma a cikin ikilisiyar Kirista?

20 Tun da ya zama Sarki Almasihu a shekara ta 1914, Yesu ya daukaka shari’a a duniya. Ta yaya? Ya goyi bayan cikar annabcinsa da ke Matta 24:14. Mabiyan Yesu a duniya sun koyar da mutanen dukan kasashe gaskiya game da Mulkin Jehovah. Kamar Yesu, sun yi wa’azi ba tare da son zuciya ba kuma cikin adalci, suna kokarin su ba kowa—yara da manya, attajiri da matalauci, maza da mata—zarafi su san Jehovah, Allah na shari’a ta gaskiya.

21 Yesu kuma yana daukaka shari’a a cikin ikilisiya ta Kirista, wanda shi ne Shugabanta. Kamar yadda aka annabta, ya yi tanadin “kyauta ga mutane,” dattawa Kiristoci masu aminci wadanda suke ja-gora a cikin ikilisiya. (Afisawa 4:8-12) Wajen kiwon wannan garke mai tamani na Allah, irin wadannan mutane suna bin misalin Yesu Kristi wajen daukaka shari’a. Suna tunawa kullum cewa Yesu yana son a bi da tumakinsa cikin adalci—ko yaya matsayinsu, rinjaya, ko kuma arziki.

22. Yaya Jehovah yake ji game da rashin adalci mai yawa a duniya ta yau, kuma menene ya nada Dansa ya yi game da shi?

22 A nan gaba kadan, Yesu zai kafa shari’a a duniya a babbar hanya. Rashin adalci ya yi yawa cikin wannan lalatacciyar duniya. Kowane yaro da ya mutu domin yunwa ya fada ne cikin hannun rashin adalci da ba ta da hujja, musamman idan muka yi tunani game da kudi da kuma lokaci da ake batarwa wajen yin makaman yaki da kuma nishadi na son kai na maneman nishadi. Miliyoyin mutuwa marar iyaka kowacce shekara suna daya ne cikin rashin adalci mai yawa, duka kuma suna ta da fushin Jehovah na adalci. Ya nada Dansa ya yi yaki na adalci da dukan wannan mugun zamani ya kawo karshen dukan rashin adalci dindindin.—Ru’ya ta Yohanna 16:14, 16; 19:11-15.

23. Bayan Armageddon, ta yaya Kristi zai daukaka shari’a cikin dukan fil’azal?

23 Amma dai, shari’ar Jehovah ta kunshi fiye da kawai halaka miyagu. Ya kuma nada Dansa ya yi sarauta shi ‘Dan sarkin Salama.’ Bayan yakin Armageddon, sarautar Yesu za ta kafa salama a dukan duniya, kuma zai yi sarauta “ta wurin . . . adalci.” (Ishaya 9:6, 7) Sai Yesu ya yi farin ciki wajen kawar da dukan rashin adalci da ya kawo bala’i da wahala a duniya. A cikin dukan fil’azal, zai daukaka cikakkiyar shari’a ta Jehovah da aminci. Saboda haka, yana da muhimmanci mu yi kokari mu yi koyi da shari’ar Jehovah a yanzu. Bari mu ga yadda za mu yi haka.

^ sakin layi na 1 Wajen nuna fushi na adalci, Yesu kama yake da Jehovah, wanda yake “fushi” da dukan mugunta. (Nahum 1:2) Alal misali, bayan Jehovah ya gaya wa mutanensa masu taurin kai cewa sun mai da gidansa “kogon mafasa,” ya ce: “Za a zubar da fushina da hasalata a bisa wurin nan.”—Irmiya 7:11, 20.

^ sakin layi na 3 In ji Mishnah, an taba zanga-zanga wasu shekaru daga baya domin tsadar tantabaru a haikalin. Aka rage kudin tantabarun nan da nan da kashi 99 kan dari! Wa suke amfana daga wannan kasuwanci mai riba? Wasu ’yan tarihi suka ce kasuwar haikalin, gidan Babban Firist Annas suke da ita, yana ba da yawancin arziki wa iyalin firist din.—Yohanna 18:13.

^ sakin layi na 16 Farisawan sun yi imani da cewa matalauta, wadanda ba su yi zurfi a Doka ba, “la’anannu ne.” (Yohanna 7:49) Sun ce kada mutum ya koyar da su ko ya yi kasuwanci da su ko kuma ma ya ci abinci da su ko kuma ya yi addu’a tare da su. Mutum ya kyale ’yarsa ta auri dayansu ya fi ya ba da ita ga mugun dabba. Sun yi tunanin cewa tashin matattu ban da wadannan matalauta.