Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 BABI NA 1

“Ga Shi, Wannan Allahnmu Ne”

“Ga Shi, Wannan Allahnmu Ne”

1, 2. (a) Wadanne tambayoyi za ka so ka yi wa Allah? (b) Menene Musa ya tambayi Allah?

ZA KA iya tunanin yin magana da Allah? Tunanin hakan kadai ma yana tsoratarwa—Mamallakin dukan halitta yana magana da kai! Kā yi jinkiri da farko, amma sai ka yi kokari ka amsa. Ya saurare ka, ya amsa, ya sa ka sake ka yi kowacce irin tambayar da ka ke so. Yanzu, me za ka tambaya?

2 A can dā, akwai wani mutumin da ya kasance cikin irin wannan yanayin. Sunansa Musa. Abin da ya zaba ya tambayi Allah zai ba ka mamaki. Bai yi tambaya ba game da kansa, ko kuma abin da zai same shi a nan gaba, ko kuma game da wahalar talikai. Maimakon haka, ya tambayi sunan Allah. Za ka ce wannan bai dace ba, domin Musa ya riga ya san sunan Allah. Tambayarsa lalle tana da ma’ana mai zurfi. Hakika, ita ce tambaya mafi muhimmanci da Musa ya yi. Amsar ta shafi dukanmu. Za ta iya taimakonka wajen bin muhimmiyar hanya ta kusantar Allah. Ta yaya? Bari mu bincika wannan tadi na musamman.

3, 4. Menene ya kai Musa yin tadi da Allah, kuma menene wannan tadin?

3 Musa dan shekara 80 ne lokacin. Ya yi shekara arba’in yana hijira daga mutanensa Isra’ilawa, wadanda bayi ne a kasar Masar. Wata rana, sa’ad da yake kiwon garken surukinsa, ya ga abin mamaki. Dan kurmi yana ci da wuta, amma bai kone ba. Yana ci kawai da wuta, yana walkiya kamar kwasfa a gefen dutse. Sai Musa ya ratse don ya duba. Watakila ya firgita sa’ad da ya ji murya ta yi masa magana a tsakiyar wutar! Ta wajen mala’ika, Allah da Musa suka yi tadi na dogon lokaci. Kamar yadda watakila ka sani, a nan Allah ya umurci Musa da yake jinkiri  saboda tsoro ya bar rayuwarsa ta salama ya koma kasar Masar ya ceci Isra’ilawa da suke bauta.—Fitowa 3:1-12.

4 A wannan lokacin, Musa da zai tambayi Allah ko da menene. Amma, ka lura da tambayar da ya zaba ya yi: “Ga shi, sa’anda na zo wurin ’ya’yan Isra’ila, na ce musu, Allah na ubanninku ya aike ni gareku, su kuma sun ce mini, Wāne sunansa? me zan ce musu?”—Fitowa 3:13.

5, 6. (a) Tambayar da Musa ya yi ta koya mana wace gaskiya ce mai sauki, mai muhimmanci? (b) Wane abu ne da ya kai a hukunta aka yi da sunan Allah? (c) Me ya sa yake da muhimmanci da Allah ya bayyana sunansa ga ’yan Adam?

5 Abu na fari da wannan tambayar ta koya mana shi ne cewa, Allah yana da suna. Bai kamata mu yi wasa da wannan gaskiya mai sauki ba. Duk da haka, da yawa suna yin haka. A fassarar Littafi Mai Tsarki da yawa, an cire sunan Allah, an sake shi da lakabi kamar su, “Ubangiji” da kuma “Allah.” Wannan shi ne abu mafi sa bakin ciki da ya kai a hukunta da aka yi don addini. Ban da haka ma, menene kake yi da farko sa’ad da ka sadu da wani? Ba sunansa kake tambaya ba? Haka yake idan ya zo ga sanin Allah. Ba wani ba ne da ba shi da suna wanda yake nesa, wanda ba za a taba saninsa ba, ko kuma a fahimce shi. Ko da yake ba a ganinsa, shi wani ne, yana da suna—Jehovah.

6 Bugu da kari, sa’ad da Allah ya bayyana sunansa, wani abin mamaki da sha’awa yana shirin aukuwa. Yana gayyatar mu ne mu zo mu san shi. Yana so mu zabi abin da ya fi kyau a rayuwa—mu kusace shi. Amma Jehovah ya yi fiye da gaya mana sunansa kawai. Ya kuma koya mana abin da sunan yake nufi.

Ma’anar Sunan Allah

7. (a) Mene ne ma’anar ainihin sunan Allah? (b) Menene Musa yake so ya sani da gaske sa’ad da ya tambayi Allah Sunansa?

7 Jehovah ya zabi sunansa da kansa, kuma sunan yana  cike da ma’ana. “Jehovah” yana nufin “Ya Kan Sa Ya Kasance.” Shi ne mafi girma a sama da duniya, shi ne ya halicce kome kuma yana cika dukan manufarsa. Wannan ma kawai ya isa ya sa mu daraja shi kuma mu ji tsoronsa. Amma muhimmancin sunansa ya bayyana shi ne kawai a matsayin mahalicci? Musa babu shakka ya so ya samu karin bayani. Ka ga, ya san cewa Jehovah ne Mahalicci, kuma ya san sunan Allah. Sunan Allah ba sabo ba ne.

8, 9. (a) Ta yaya Jehovah ya amsa tambayar Musa, kuma menene ba daidai ba game da yadda ake yawan fassara amsarsa? (b) Menene ma’anar furcin nan “zan kasance abin da zan kasance”?

8 Da yake ba da amsa, Jehovah ya bayyana wani sashen halinsa mai ban al’ajabi, wanda ya shafi ma’anar sunansa. Ya gaya wa Musa: “Zan kasance abin da zan kasance.” (Fitowa 3:14, NW ) Fassara da yawa na Littafi Mai Tsarki a wajen nan sun ce: “Ni ina yadda Ni ke.” Amma fassarar mai kyau ta nuna cewa ba wai Allah yana tabbatar da wanzuwarsa kawai ba ne. Maimakon haka, yana koya wa Musa ne—da kuma dukanmu—cewa “Zai kasance,” ko kuma ya zama, duk wani abin da ake bukata don Ya cika alkawuransa. J. B. Rotherham ya furta wannan ayar haka: “Zan zama dukan abin da nake so.” Wani gwani a Ibrananci na Littafi Mai Tsarki ya yi bayani a kan wannan furucin: “Ko yaya yanayin ko kuma bukatar . . . , Allah zai ‘zama’ maganin wannan bukatar.”

9 Me wannan yake nufi ga Isra’ilawa? Kowacce irin tangarda da za su fuskanta, ko yaya wahalar da za su iske kansu ciki ta zama, Jehovah zai zama dukan abin da ake bukata domin ya cece su daga bauta kuma ya kai su Kasar Alkawari. Babu shakka wannan sunan ya sa sun dogara ga Allah. Zai sa hakanan a gare mu a yau. (Zabura 9:10) Me ya sa?

10, 11. Ta yaya sunan Jehovah ya sa mu yi tunaninsa cewa Uba ne nagari da za a iya tunaninsa? Ka ba da misali.

10 Alal misali: Iyaye sun san yadda za su rika gyara wajen  kula da ’ya’yansu. A rana guda, uwa za ta zama nas, mai girki, malama, mai ba da horo, alkali, da sauransu. Mutane da yawa suna jin ayyuka masu yawa da ake bukata daga wurinsu ya fi karfinsu. Sun lura da dogara kwarai da ’ya’yansu suke yi gare su, ba sa shakkar cewa Baba ko Mama, za su lallashe su, su sulhunta su, su gyara abin wasa da ya lalace, kuma su amsa kowacce irin tambayar da ta fito daga zuciyarsu mai yawan tambayoyi. Wasu iyaye suna jin ba su cancanci irin dogarar da ’ya’yansu suke yi gare su ba a wasu lokatai su ji kunya, domin kasawarsu. Suna ji kamar ba su isa ba sam su yi wadannan ayyuka.

11 Jehovah ma Uba ne mai kauna. Duk da haka, ba tare da karya kamiltattun mizanansa ba, babu abin da ba zai iya zama ba domin ya kula da ’ya’yansa na duniya a hanya mafi kyau. Saboda haka sunansa, Jehovah, ya sa mu yi tunaninsa cewa Uba ne nagari da za a yi tunaninsa. (Yakub 1:17) Musa da dukan sauran amintattun Isra’ilawa ba da jimawa ba suka fahimci cewa Jehovah yana aikata abubuwa cikin jituwa da sunansa. Suka yi kallo da mamaki lokacin da Jehovah ya sa kansa ya zama Kwamandan Sojoji da ba a nasara bisansa, Shugaban abubuwan halitta, Mai Ba da Doka da babu kamarsa, Alkali, Mai Sifanta Gini, Mai Tanadin abinci da ruwa, Mai Adana tufafi da kuma takalma—da sauransu.

12. Ta yaya halin Fir’auna game da Jehovah ya bambanta da na Musa?

12 Saboda haka Allah ya bayyana sunansa, kuma ya bayyana abubuwa masu ban al’ajabi game da Wanda ke amsa sunan, kuma ya nuna cewa abubuwan da ya ce game da kansa gaskiya ne. Babu shakka, Allah yana so mu san shi. Me muka ce? Musa yana so ya san Allah. Wannan muradi mai karfi ya yi wa rayuwar Musa ja-gora kuma ya kai shi ga kusantar Ubanmu na samaniya  sosai. (Litafin Lissafi 12:6-8; Ibraniyawa 11:27) Abin nadama, kadan ne kawai cikin tsarar Musa suke da irin wannan muradin. Sa’ad da Musa ya gaya wa Fir’auna sunan Jehovah, wannan sarkin Masar mai girman kai, ya ce: “Wanene Jehovah?” (Fitowa 5:2, NW ) Fir’auna ba ya son ya samu karin sani game da Jehovah. Maimako, ya sallami Allah na Isra’ila cikin ba’a cewa ba shi da muhimmanci ko kuma amfani. Irin wannan hali gama-gari ne a yau. Yana makanta mutane ga daya cikin muhimmiyar gaskiyar cewa—Jehovah shi ne Ubangiji Sarki Mai Girma.

Jehovah Ubangiji Sarki Mai Girma

13, 14. (a) Me ya sa ake ba Jehovah lakabi da yawa a cikin Littafi Mai Tsarki, kuma ina wasu cikinsu? ( Ka duba akwati a shafi na 14.) (b) Me ya sa Jehovah ne kadai ya kai a ce da shi “Allah, Madaukaki”?

13 Jehovah yana gyara kwarai, da ya sa yana da lakabi da yawa da suka dace cikin Nassi. Wadannan lakabin ba sa gasa da sunansa; maimakon haka, suna koya mana ne karin abin da sunansa yake nufi. Alal misali, an kira shi “Allah, Madaukaki.” (Zabura 57:2) Wannan lakabi na daukaka, da ya bayyana sau da yawa a cikin Littafi Mai Tsarki ya gaya mana matsayin Jehovah. Shi kadai yake da ikon ya Mallaki dukan halitta. Ka bincika abin da ya sa.

14 Jehovah makadaici ne yadda yake Mahalicci. Ru’ya ta Yohanna 4:11 ta ce: “Kai ne mai-isa ka karbi daukaka da daraja da iko, ya Ubangijinmu da Allahnmu: gama kai ka halicci dukan abu, saboda nufinka kuma suka kasance, saboda nufinka aka halicce shi.” Wadannan kalmomin masu daukaka ba za su kasance ga wani dabam ba. Kowanne abu a sararin samaniya Jehovah ne ya halicce shi! Babu shakka, Jehovah ya cancanci daraja, iko, da kuma daukaka da ke ga Ubangiji Sarki Mai Girma kuma Mahaliccin dukan abu.

15. Me ya sa aka kira Jehovah “Sarki na zamanu”?

 15 Wani lakabin da Jehovah ne kawai yake da shi “Sarki na zamanu” ne. (1 Timothawus 1:17; Ru’ya ta Yohanna 15:3) Menene wannan yake nufi? Yana da wuya hankalinmu mai iyaka ya fahimta, amma Jehovah madawwami ne a duka gefe biyu—gaba da baya. Zabura 90:2 ta ce: “Tun fil’azal kai ne Allah har abada.” Saboda haka, Jehovah ba shi da mafari; ya kasance koyaushe. An kira shi yadda ya dace Wanda Yake “Tun Fil’azal”—domin yana wanzuwa tun daga dawwama kafin wani ko wani abu ya wanzu! (Daniel 7:9, 13, 22) Wanene zai iya tuhumar cancantarsa na Ubangiji Sarki Mai Girma?

16, 17. (a) Me ya sa ba za mu iya ganin Jehovah ba, kuma me ya sa wannan bai kamata ya ba mu mamaki ba? (b) A wace hanya ce Jehovah ya kasance fiye da wani abin da za mu iya gani ko kuma mu taba?

16 Duk da haka, wasu suna tuhumar wannan cancantar, kamar yadda Fir’auna ya yi. Kadan daga cikin damuwar shi ne mutane ajizai sun dogara sosai bisa abin da suke iya gani da idanunsu. Ba za mu iya ganin Ubangiji Sarki Mai Girma ba. Shi ruhu ne, ba ya ganuwa ga idanun mutane. (Yohanna 4:24) Ban da haka ma, idan mutum jini da nama ya tsaya a gaban Jehovah Allah, ai sai mutuwa ke nan. Jehovah kansa ya gaya wa Musa: “Ba ka da iko ka ga fuskata: gama mutum ba shi ganina shi rayu.”—Fitowa 33:20; Yohanna 1:18.

17 Wannan bai kamata ya ba mu mamaki ba. Musa ya ga daukakar Jehovah kadan, ta wajen mala’ika da yake wakilanci. Menene sakamakon wannan? Fuskar Musa ta yi “kyalli” na wani lokaci bayan haka. Isra’ilawa sun tsoraci su dubi fuskar Musa kai tsaye. (Fitowa 33:21-23; 34:5-7, 29, 30) Saboda haka, babu shakka, cewa babu mutumin da zai iya ganin Ubangiji Sarki Mai Girma kansa a dukan daukakarsa! Wannan yana nufi ne cewa bai kasance kamar abin da za mu iya gani kuma mu taba ba? A’a, mun yarda da wanzuwar abubuwa da yawa da ba ma iya gani— alal misali iska, taguwar rediyo, da kuma tunani. Bugu da kari, Jehovah yana nan dindindin, shigewar lokaci ba ta shafansa, har biliyoyin shekaru babu iyaka! A wannan hanya, ya fi kome da za mu iya gani ko kuma mu taba, domin duniyar da muke gani tana tsufa kuma ta rube. (Matta 6:19) Ya kamata ne mu yi tunaninsa kamar, wani abu ko iko ne kawai da babu alama ko kuma Aukuwar Farko marar ma’ana? Bari mu gani.

Allah Mai Mutuntaka

18. Wane wahayi aka ba wa Ezekiel, kuma menene fuskoki hudu na “masu-rai” da suke kusa da Jehovah yake alamtawa?

18 Ko da yake ba za mu iya ganin Allah ba, da akwai wajeje masu ban sha’awa cikin Littafi Mai Tsarki da suka ba mu damar leka cikin sama kanta. Sura ta farko ta Ezekiel misali ne guda. An ba wa Ezekiel wahayin kungiyar Jehovah ta sama, wadda ya gani kamar karusar haske mai yawa. Musamman wadanda suka burge shi sune kwatancin manyan ruhohi da suka kewaye Jehovah. (Ezekiel 1:4-10) Wadannan “masu-rai” suna da nasaba da Jehovah, kuma sifarsu ta bayyana mana wani abu mai muhimmanci game da Allah da suke yi wa bauta. Kowanne yana da fuskoki hudu—ta bijimi, ta zaki, ta gaggafa, da kuma ta mutum. Wadannan babu shakka suna alamta halaye ne hudu na musamman na mutuntakar Jehovah.—Ru’ya ta Yohanna 4:6-8, 10.

19. Wane hali ne (a) fuskar bijimi take alamtawa? (b) ta zaki fa? (c) ta gaggafa fa? (d) ta mutum fa?

19 A cikin Littafi Mai Tsarki, bijimi sau da yawa yana nufin karfi, kuma hakan ya dace, domin dabbar tana da karfi sosai. Zaki kuma, sau da yawa yana zaman shari’a, domin shari’a ta gaskiya tana bukatar gaba gadi, hali da aka san zaki da shi. Gaggafa an san ta domin idanunta, tana ganin har dan abu mitsitsi a nesa. Saboda haka fuskar gaggafa tana alamar hikimar hangar nesa na Allah. Fuskar mutum  kuma fa? Mutum da aka halitta a kamanin Allah, ya kadaita wajen nuna hali na Allah mafi girma—kauna. (Farawa 1:26) Wadannan sashen mutuntakar Jehovah—karfi, shari’a, hikima, da kuma kauna—an nanata su sau da yawa a cikin Nassosi da za a iya kiransu halayen Allah na musamman.

20. Ya kamata mu damu ne cewa mutuntakar Jehovah za ta canja, kuma me ya sa ka fadi haka?

20 Ya kamata mu damu ne cewa Allah watakila ya canja cikin shekaru dubbai tun lokacin da aka kwatanta shi cikin Littafi Mai Tsarki? A’a, mutuntakar Allah ba ta canjawa. Ya gaya mana: “Gama ni Ubangiji ba mai-sakewa ba ne.” (Malachi 3:6) Maimakon ya rika canjawa kawai bisa ga motsin zuci, Jehovah ya tabbatar da kansa Uba ne cikakke ta hanyar da yake bi da kowanne yanayi. Yana nuna fasalolin mutuntakarsa da ta dace. Daya daga cikin halayensa hudu, wadda ta fi ita ce kauna. Tana bayyana a dukan abin da Allah yake yi. Yana nuna karfinsa, shari’arsa, da kuma hikimarsa cikin kauna. Hakika, Littafi Mai Tsarki ya fadi wani abu mai girma game da Allah da kuma wannan halin. Ya ce: “Allah kauna ne.” (1 Yohanna 4:8)  Ka lura cewa bai ce Allah yana da kauna ba ko kuma Allah yana kauna. Maimakon haka, ya ce Allah kauna ne. Kauna ita ce asali, ita take motsa shi ya yi dukan abin da yake yi.

“Ga Shi, Wannan Allahnmu Ne”

21. Yaya za mu ji sa’ad da muka kara fahimi game da halayen Jehovah?

21 Ka taba ganin dan yaro yana nuna wa abokansa ubansa da farin ciki da kuma alfahari, “Ga babana”? Masu bauta wa Jehovah suna da dalilan jin haka game da Jehovah. Littafi Mai Tsarki ya annabta lokaci da amintattun mutane za su yi ihu: “Ga shi, wannan Allahnmu ne.” (Ishaya 25:8, 9) Da zarar ka kara fahimi game da halayen Jehovah, hakanan za ka ji kana da Uba mafi kyau da za a iya tunaninsa.

22, 23. Yaya Littafi Mai Tsarki ya kwatanta Ubanmu na samaniya, kuma ta yaya muka sani cewa yana so mu kusace shi?

22 Wannan Uba ba mara juyayi ba ne, ko kuma yana da nesa—duk da abin da wasu masu addini masu zafin hali da kuma ’yan falsafa suka koyar. Ba za mu so mu matso kusa da Allah marar juyayi ba, kuma Littafi Mai Tsarki ya ce Ubanmu na samaniya ba haka yake ba. Amma ya kira shi “Allah mai-albarka.” (1 Timothawus 1:11) Yana yin fushi kuma yana yin farin ciki. Yana “bata masa zuciya” idan halittunsa masu hankali suka taka ka’idodi da ya kafa domin amfaninsu. (Farawa 6:6; Zabura 78:41) Amma sa’ad da muka yi abu da hikima cikin jituwa da Kalmarsa, muna ‘faranta zuciyarsa.’—Misalai 27:11.

23 Ubanmu yana so mu kusace shi. Kalmarsa ta karfafa mu mu ‘nemi Allah, ko halama ma a lallaba mu same shi, ko da shi ke ba shi da nisa da kowanne dayanmu ba.’ (Ayukan Manzanni 17:27) Amma, yaya kuwa, zai yiwu ga ’yan Adam su kusaci Ubangiji Sarki Mai Girma na dukan halitta?