Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 Babi Na 28

‘Kai Kaɗai ne Mai Aminci’

‘Kai Kaɗai ne Mai Aminci’

1, 2. Me ya sa za mu ce Sarki Dauda ba baƙon rashin aminci ba ne?

SARKI Dauda ba baƙon rashin aminci ba ne. A wani lokaci, sarautarsa ta shaida tashin hankali, ta cika da ƙulle-ƙulle, mutanen al’ummarsa sun yi ƙulle-ƙulle a kansa. Bugu da ƙari, wasu cikin waɗanda muke tsammanin abokansa ne na kud da kud suka ci amanarsa. Ka yi la’akari da Michal, matar Dauda ta farko. Da farko tana “ƙaunar Dauda,” babu shakka tana taimakonsa a dukan fama da yake yi na sarauta. Amma daga baya, ta “kuwa raina shi a zuciyarta,” har ta ɗauke shi kamar mutane “ashararu.”—1 Samu’ila 18:20; 2 Samu’ila 6:16, 20.

2 Sai kuma mashawarcin Dauda, Ahithophel. Ana ɗaukar shawararsa da muhimmanci ƙwarai kamar magana ce daga Jehovah. (2 Samu’ila 16:23) Amma a ƙarshe, amininsa ya zama maci amana, ya saka hannu wajen shirya tawayen ga Dauda. Kuma wanene madugun waɗanda suka ƙulla wannan dabara? Absalom ne, ɗan cikin Dauda! Wannan maƙullin “ya [dinga] sace zukatan maza na Isra’ila,” yana aza kansa sarki na biyu. Tawayen Absalom ya yi ƙarfi da ya tilasta wa Sarki Dauda ya yi gudun ransa.—2 Samu’ila 15:1-6, 12-17.

3. Wane tabbaci Dauda yake da shi?

3 Babu wanda ya kasance ne da aminci ga Dauda? A cikin dukan masifarsa, Dauda ya sani da akwai wanda ya kasance da aminci. Waye? Babu wani sai Jehovah Allah. “Ga mai aminci za ka nuna kai mai aminci ne,” in ji Dauda game da Jehovah. (2 Samu’ila 22:26; NW ) Menene aminci, kuma ta yaya Jehovah ya ba da misali mafi girma na wannan hali?

 Menene Aminci?

4, 5. (a) Menene “aminci”? (b) Ta yaya aminci ya bambanta da yarda?

4 ‘Aminci’ yadda aka yi amfani da shi a Nassosin Ibrananci, mutunci ne da yake manne wa wani abu kuma ba ya barin abin har sai nufinsa ya cika game da abin. Ya ƙunshi fiye da yarda kawai. Alhali ma, mutum zai iya kasancewa abin yarda domin ya zama masa wajibi. Akasin haka, aminci ya kahu ne cikin ƙauna. * Bugu da ƙari, kalmar nan “aminci” za a iya amfani da ita ga abubuwa da ba su da rai. Alal misali, mai Zabura ya kira wata “amintaccen mai-shaida cikin sararin sama” domin bayyanarsa a kai a kai. (Zabura 89:37) Amma wata ba zai iya kasancewa da aminci kamar mutum ba. Me ya sa? Domin aminci nuna ƙauna ce—abin da abubuwa marasa rai ba za su iya yi ba.

An kira wata, mai shaida mai aminci, amma halittu masu fahimi ne kawai za su iya nuna irin aminci na Jehovah da gaske

5 A ma’anarta ta Nassi, aminci yana nuna ƙauna. Bayyanarsa ya nuna cewa da dangantaka tsakanin mai aminci da kuma wanda ake nuna wa aminci. Irin wannan  amincin ba mai lilo ba ne. Ba kamar taguwar teku ba ce da iskar canjin yanayi take busa ta. Akasarin haka, aminci ko kuma ƙauna ta aminci, yana da ƙarfi ya yi nasara bisa tangarɗa mai tsanani.

6. (a) Yaya ake rashin aminci a tsakanin ’yan Adam, kuma ta yaya aka nuna wannan a cikin Littafi Mai Tsarki? (b) Wace hanya ce mafi kyau na koyon abin da aminci yake nufi, kuma me ya sa?

6 Irin wannan aminci yana da wuya a yau. Sau da yawa, abokanai na kusa ‘sukan halaka juna.’ Labarin mutane suna yasar da abokanan aurensu yana ƙaruwa. (Misalai 18:24; Malachi 2:14-16) Ayyukan cin amana sun zama ruwan dare, da za mu riƙa maimaita kalmomin annabi Mikah: ‘Mutum mai aminci ya shuɗe daga duniya.’ (Mikah 7:2) Ko da yake mutane suna kasawa wajen nuna ƙauna ta aminci, aminci mashahurin hali ne na Jehovah. Hanya mafi kyau na koyon ainihi abin da aminci yake nufi ita ce bincika yadda Jehovah ya nuna wannan ɓangare mai girma na ƙaunarsa.

Amincin Jehovah da Ba Wanda Ya Kai Shi

7, 8. Me ya sa za a iya cewa Jehovah ne kaɗai mai aminci?

7 Littafi Mai Tsarki ya ce game da Jehovah: “Kai kaɗai ne mai aminci.” (Ru’ya ta Yohanna 15:4, NW ) Ta yaya wannan zai yiwu? Mutane ma da mala’iku ba a wasu lokatai sun nuna aminci na ban mamaki ba? (Ayuba 1:1; Ru’ya ta Yohanna 4:8) Yesu Kristi kuma fa? Ba shi ne shugaba ‘mai aminci’ na Allah ba? (Zabura 16:10) To, me ya sa za a ce Jehovah ne kaɗai mai aminci?

8 Da farko, ka tuna cewa aminci ɓangare ne na ƙauna. Tun da “Allah ƙauna ne”—tun da shi ne ainihin tushen wannan halin—waye zai nuna aminci cikakke fiye da Jehovah? (1 Yohanna 4:8) Hakika, mala’iku da mutane za su iya nuna irin halinsa, amma Jehovah ne kawai yake da aminci fiye da kowa. “Mai-zamanin dā,” ya nuna aminci  da jimawa kafin kowace halitta, a duniya ko sama. (Daniel 7:9) Saboda haka, Jehovah ne tushen aminci. Ya nuna wannan hali a hanyar da babu wata halitta da za ta yi daidai da shi. Ga wasu misalai.

9. Ta yaya Jehovah yake da ‘aminci cikin ayyukansa’?

9 Jehovah ‘mai aminci ne cikin dukan ayyukansa.’ (Zabura 145:17) A wace hanya? Zabura ta 136 ta ba da amsa. A nan an ambaci wasu ayyukan ceto na Jehovah, har ma da ceto na ban mamaki na Isra’ilawa daga Jar Teku. Abin lura kuma, kowacce aya ta wannan Zabura ta ƙare da: ‘Ƙaunarsa [ko kuma, amincinsa] madawwamiya ce.’ Wannan zabura an haɗa ta cikin Tambayoyi don Bimbini da ke shafi na 289. Sa’ad da kake karatun waɗannan ayoyi, yadda Jehovah ya nuna alheri a hanyoyi dabam dabam ga mutanensa zai burge ka. Hakika, Jehovah ya nuna aminci ga bayinsa amintattu ta wajen saurarar kukarsu na neman taimako kuma ya taimaka musu a lokacin da ya dace. (Zabura 34:6) Aminci na ƙauna na Jehovah ga bayinsa ba ya jijjiga, muddin sun kasance da aminci a gare shi.

10. Ta yaya Jehovah ya nuna aminci game da mizanansa?

10 Bugu da ƙari, Jehovah yana nuna aminci ga bayinsa ta wajen nacewa ga mizanansa. Ba kamar wasu mutane ba ne da ba su da tafarki takamaimai, waɗanda tunani ne kawai yake yi musu ja-gora, Jehovah ba ya shawagi a wajen ra’ayinsa game da abin da yake nagari da abin da yake mugu. A cikin dukan shekaru aru-aru, ra’ayinsa game da sihiri, bautar gumaka, da kisa ba su canja ba. “Har tsufarku kuma, ni ne shi,” haka ya faɗa ta bakin annabinsa Ishaya. (Ishaya 46:4) Saboda haka, mun tabbata cewa za mu amfana daga bin tafarkin ɗabi’a da yake cikin Kalmar Allah.—Ishaya 48:17-19.

11. Ka ba da misali da zai nuna cewa Jehovah yana da aminci ga alkawarinsa.

11 Jehovah kuma ya nuna aminci ta wajen kasancewa  da yarda ga kalmarsa ta alkawari. Idan ya faɗi abu, an yi an gama. Saboda haka Jehovah ya ce: “Maganata, wadda ta ke fitowa daga cikin bakina . . . ba za ta koma wurina wofi ba, amma za ta cika abin da na nufa, za ta yi albarka kuma a cikin saƙona.” (Ishaya 55:11) Ta wajen cika kalmarsa, Jehovah ya nuna aminci ga mutanensa. Ba ya ƙyale su su riƙa tsammanin abin da bai yi niyyar kawowa ba. Jehovah ba ya kasawa, shi ya sa bawansa Joshua ya ce game da shi: “Cikin dukan alherin da Ubangiji ya yi zancensa ga gidan Isra’ila babu wani abin da ya sare; dukan abu ya tabbata.” (Joshua 21:45) Saboda haka, mu tabbata cewa ba za mu taɓa nadama ba domin wata kasawa daga Jehovah ya cika alkawarinsa.—Ishaya 49:23; Romawa 5:5.

12, 13. A waɗanne hanyoyi ne ƙauna ta alheri ta Jehovah ‘madawwamiya ce’?

12 Kamar yadda muka lura da farko, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ƙaunar Jehovah ‘madawwamiya ce.’ (Zabura 136:1) Ta yaya wannan ya kasance haka? A wata hanya, gafarta zunubi ta Jehovah ta dindindin ce. Kamar yadda aka tattauna a Babi na 26, Jehovah ba ya tunawa da kuskure da ya shige wanda ya yi wa mutum gafara. Tun “da shi ke dukan mutane sun yi zunubi, sun kasa kuma ga darajar Allah,” kowannenmu ya yi godiya cewa ƙaunar Jehovah madawwamiya ce.—Romawa 3:23.

13 Ƙauna ta alherin Jehovah madawwamiya ce a wata hanya kuma. Kalmarsa ta ce adali “za ya zama kamar itacen da aka dasa a magudanan ruwaye, wanda yana bada ’ya’yansa a cikin kwanakinsa; ganyensa ba ya yi yaushi ba; kuma cikin iyakar abin da ya ke yi za shi yi albarka.” (Zabura 1:3) Ka yi tunanin itacen da ganyensa ba ya yin yaushi! Haka yake, idan muka yi farin ciki ƙwarai cikin Kalmar Allah, za mu rayu na dogon lokaci, cikin salama, da kuma gamsuwa. Albarka da Jehovah zai ba wa bayinsa  masu aminci masu dawwama ne. Hakika, a cikin sabuwar duniya da Jehovah zai kawo, mutane masu biyayya za su more alherinsa har abada.—Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4.

Jehovah “Ba Ya Yarda Tsarkakansa Ba”

14. Ta yaya Jehovah yake nuna godiya ga amincin bayinsa?

14 Jehovah ya nuna amincinsa a kai a kai. Tun da Jehovah ba ya jijjiga, aminci da yake nuna wa bayinsa masu aminci ba ya taɓa ragewa. Mai Zabura ya rubuta: “Dā yaro ni ke, yanzu kuwa na tsufa: amma ban taɓa gani an yar da mai-adalci ba, ko kuwa zuriyarsa suna roƙon abincinsu. Gama Ubangiji yana son shari’a, kuma ba ya yarda tsarkakansa ba.” (Zabura 37:25, 28) Hakika, tun da Mahalicci ne, Jehovah ya cancanci bautarmu. (Ru’ya ta Yohanna 4:11) Kuma domin shi mai aminci ne, Jehovah yana ɗaukar ayyukansu na aminci da tamani.—Malachi 3:16, 17.

15. Ka yi bayani game da yadda sha’anin Jehovah da al’ummar Isra’ila ya nuna Amincinsa.

15 Cikin alherinsa, Jehovah a kai a kai yake taimaka wa mutanensa sa’ad da suke cikin wahala. Mai Zabura ya gaya mana: “Shi mai-kiyayadda rayukan tsarkakansa ne; Yana fishe su daga hannun masu-mugunta.” (Zabura 97:10) Ka yi la’akari da sha’aninsa da al’ummar Isra’ila. Bayan ya cece su cikin mu’ujiza daga Jar Teku, Isra’ilawa suka yi shela cikin waƙa ga Jehovah: “Kai cikin [ƙaunarka ta alherin ko kuma, ƙauna ta aminci] ka biyar da mutane waɗanda ka fanshe su.” (Fitowa 15:13, hasiya ta NW ) Ceto daga Jar Teku hakika aiki ne na ƙauna cikin aminci daga Jehovah. Musa ya gaya wa Isra’ilawan: “Ba domin kun fi dukan al’umma yawa ba Ubangiji ya ƙallafa ƙaunatasa a gareku, ya zaɓe ku; gama ku mafi ƙaramta ne daga cikin dukan al’ummai: amma domin Ubangiji yana ƙaunarku yana kuwa da nufin ya tsayadda rantsuwa wadda ya  rantse ma ubanninku, domin wannan Ubangiji ya fishe ku da hannu mai-ƙarfi, ya fanshe ku daga gidan bauta, daga hannun Fir’auna sarkin Masar.”—Kubawar Shari’a 7:7, 8.

16, 17. (a) Wane irin nuna rashin godiya ne Isra’ilawa suka yi, duk da haka yaya Jehovah ya ji tausayinsu? (b) Ta yaya Isra’ilawa suka nuna cewa “babu magani” da zai yi musu, kuma wane misalin gargaɗi wannan ya ba mu?

16 Hakika, al’ummar Isra’ila ta kasa nuna godiya ga alherin Jehovah, domin bayan ya cece su “suka dinga yin zunubi ga [Jehovah], suna tayar ma Maɗaukaki.” (Zabura 78:17) Cikin ƙarnuka, sun yi tawaye a kai a kai, suna barin Jehovah kuma suna juyawa ga wasu allolin ƙarya da ayyukan arna da suke ƙazantarwa. Duk da haka, Jehovah bai karya alkawarinsa ba. Maimakon haka ta wajen annabi Irmiya Jehovah ya kira mutanensa: “Ki juyo, ya ke Isra’ila maɓaraiciya, . . . ba ni dubanki da fushi: gama mai-[aminci] ne ni.” (Irmiya 3:12) Kamar yadda aka lura a Babi na 25, yawancin Isra’ila ba su motsa ba. Hakika, “suka yi ma manzannin Allah ba’a, suka rena maganatasa, suka yi ma annabawansa zunɗa.” Menene sakamakon haka? A ƙarshe, “fushin Ubangiji ya tashi bisa kan mutanensa, har babu magani.”—2 Labarbaru 36:15, 16.

17 Menene muka koya daga wannan? Amincin Jehovah ba makaho ba ne kuma ba a ruɗunsa. Hakika, Jehovah ‘mai yalwar alheri’ ne kuma yana farin ciki ya yi jinƙai idan da dalilin yin sa. Amma menene yake faruwa sa’ad da mai laifi ya nuna shi ya wuci gyara? A irin wannan yanayin, Jehovah yana manne wa mizanansa na adalci kuma ya yi horo. An gaya wa Musa, Jehovah “ba shi kuɓutadda mai-laifi ko kaɗan.”—Fitowa 34:6, 7.

18, 19. (a) Ta yaya ne hukunta miyagu da Jehovah zai yi ma aikin aminci ne? (b) A wace hanya ce Jehovah zai nuna amincinsa ga bayinsa da aka tsananta musu har zuwa mutuwa?

18 Hukunta miyagu na Allah ma aikin aminci ne. Ta  yaya? Nuni ɗaya an same shi daga littafin Ru’ya ta Yohanna a umurnin da Jehovah ya ba mala’iku bakwai: “Ku tafi, ku zubarda bakwaiɗin kasake na hasalar Allah cikin duniya.” Sa’ad da mala’ika na uku ya zubar da nasa kasko “cikin teku” sai ya zama jini. Sai mala’ikan ya gaya wa Jehovah: “Mai-[aminci] ne kai, wanda kake yanzu, ka kasance a dā kuma, kai Mai-tsarki, domin ka hukunta hakanan: gama su suka zubarda jinin tsarkaka da annabawa, jini kuma ka ba su su sha: wannan ya dace da su.”—Tafiyar tsutsa tamu ce; Ru’ya ta Yohanna 16:1-6.

Jehovah cikin aminci zai tuna da waɗanda suka kasance da aminci har mutuwa kuma ya tashe su

19 Ka lura cewa a tsakiyar idar da saƙon hukunci, mala’ikan ya kira Jehovah ‘Mai Aminci.’ Me ya sa? Ta wajen halaka miyagu, Jehovah yana nuna aminci ga bayinsa, da yawa cikinsu an tsananta musu har mutuwa. Cikin aminci, Jehovah ya ajiye waɗannan a raye cikin tunaninsa. Yana so ya ga waɗannan masu aminci da suka mutu, Littafi Mai Tsarki ya tabbatar da cewa nufinsa ne ya sāka musu da tashin matattu. (Ayuba 14:14, 15) Jehovah bai manta da bayinsa masu aminci ba kawai domin ba su da rai. Akasarin haka, “suna rayuwa gareshi.” (Luka 20: 37, 38) Nufin Jehovah ya dawo da waɗanda suka mutu zuwa rai waɗanda yake tunawa da su tabbaci ne mai ƙarfi na amincinsa.

Bernard Luimes (a sama) da Wolfgang Kusserow (a tsakiya) ’yan Nazi ne suka kashe su

Wani rukunin ’yan siyasa sun tsare Moses Nyamussua kada a kashe shi

Ƙauna ta Aminci ta Jehovah ta Buɗe Hanyar Ceto

20. Su waye ne “tukwane na jinƙai,” kuma ta yaya Jehovah ya nuna musu aminci?

20 A cikin dukan tarihi, Jehovah ya nuna aminci mai ban mamaki ga mutane masu aminci. Hakika, a shekaru dubbai, Jehovah ya yi “haƙuri mai-yawa ya jimre da tukwane na fushi shiryayyu ga halaka.” Me ya sa? “Domin kuma ya sanarda wadatar ɗaukakarsa bisa tukwane na jinƙai, waɗanda ya rigaya ya shirya su zuwa ɗaukaka.” (Romawa 9:22, 23) Waɗannan “tukwane na jinƙai” masu zukatan kirki ne waɗanda ruhu mai tsarki ya shafa su su  zama magāda tare da Kristi na Mulkinsa. (Matta 19:28) Ta wajen buɗe hanyar ceto ga waɗannan tukwane na jinƙai, Jehovah ya kasance da aminci ga Ibrahim, wanda ya yi wa alkawarin nan: “Cikin zuriyarka kuma dukan al’umman duniya za su sami albarka; domin ka yi biyayya da maganata.”—Farawa 22:18.

Domin amincin Jehovah, dukan bayinsa masu aminci suna da tabbataccen bege na nan gaba

21. (a) Ta yaya Jehovah ya nuna aminci ga “taro mai-girma” waɗanda suke da begen tsira daga “ƙunci mai-tsanani”? (b) Menene amincin Jehovah ya motsa ka ka yi?

21 Jehovah ya nuna aminci ga “taro mai-girma” waɗanda suke da begen tsira daga “ƙunci mai-tsanani” da kuma rayuwa har abada cikin aljanna a duniya. (Ru’ya ta Yohanna 7:9, 10, 14) Ko da yake bayinsa ajizai ne, Jehovah cikin aminci ya ba su zarafin rayuwa har abada cikin aljanna a duniya. Ta yaya ya yi haka? Ta wajen fansa—nuna aminci ne mafi girma. (Yohanna 3:16; Romawa 5:8) Amincin Jehovah yana jawo waɗanda, a zuciyarsu, suna bukatar adalci. (Irmiya 31:3) Ba ka ji ka fi kusa da Jehovah domin aminci mai ƙarfi da ya nuna da kuma wanda zai nuna? Tun da muradinmu ne mu kusaci Allah, mu yi na’am ga ƙaunarsa ta wajen ƙarfafa aniyarmu mu bauta masa cikin aminci.

^ sakin layi na 4 Daɗinsa shi ne, kalmar nan da aka fassara “aminci” a 2 Samu’ila 22:26, NW, an fassara ta “alheri” ko kuma ‘ƙauna ta aminci’ a wani waje.