Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 BABI NA 25

“Jinƙai Mai-Taushi na Allahnmu”

“Jinƙai Mai-Taushi na Allahnmu”

1, 2. (a) Yaya uwa take amsa kukar jaririnta? (b) Wane motsin rai ne yake da ƙarfi fiye da juyayi na uwa?

DA TSAKAR dare, jariri ya yi kuka. Nan da nan, uwar ta farka. Ba ta barci kamar yadda ta saba—tun da ta haife jaririnta. Ta koyi ta bambance kuka iri-iri na jaririnta. Saboda haka, sau da yawa za ta iya faɗar ko jaririnta yana bukatar abinci, lallami, ko kuma a kasance tare da shi. Amma ko menene dalilin kukar jaririn uwar za ta amsa. Zuciyarta ba za ta ƙyale ta ta ƙyale bukatar jaririnta ba.

2 Juyayin da uwa take yi wa ɗan cikinta yana tsakanin motsin rai mai taushi da ’yan Adam suka sani. Amma da akwai, motsin rai da ya fi wannan ƙarfi—jinƙai mai taushi na Allahnmu, Jehovah. Binciken wannan hali na ƙauna zai taimaka mana mu kusaci Jehovah. To, bari mu tattauna abin da juyayi yake nufi da kuma yadda Allah yake nuna shi.

Menene Juyayi?

3. Mecece ma’anar aikatau na Ibrananci da aka fassara “yin jinƙai” ko kuma “ji tausayi”?

3 A cikin Littafi Mai Tsarki, juyayi da jinƙai suna da nasaba ta kusa kusa. Wasu kalmomin Ibrananci da na Helenanci sun ba da ma’anar juyayi mai taushi. Alal misali, ka yi la’akari da aikatau na Ibrananci ra·chamʹ, wanda sau da yawa aka fassara shi “yin jinƙai” ko kuma “ji tausayi.” Wani littafin neman bayani ya yi bayani cewa aikatau ra·chamʹ “yana nuna juyayi mai zurfi kuma mai taushi, kamar wanda yake zuwa idan aka fuskanci kasawa ko kuma wahalar waɗanda muke  ƙauna ko kuma waɗanda suke bukatar taimakonmu.” Wannan kalmar Ibrananci, da Jehovah ya yi amfani da ita wa kansa, tana da nasaba da kalmar “mahaifa” kuma za a iya ce da ita “juyayi na uwa.” *Fitowa 33:19; Irmiya 33:26.

“Ya yiwu mace ta manta da . . . ɗan cikinta?”

4, 5. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da motsin rai da uwa take yi ga jaririnta ya koya mana game da jinƙan Jehovah?

4 Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da wannan motsin rai da uwa take da shi ga jaririnta ya koya mana game da ma’anar jinƙai na Jehovah. A Ishaya 49:15, mun karanta: “Ya yiwu mace ta manta da ɗanta mai-shan mama, har da ba za ta yi juyayin [ra·chamʹ] ɗan cikinta ba? i, ya yiwu waɗannan su manta, amma ni ba ni manta da ke ba.” Wannan kwatanci mai taɓa rai ya nuna zurfin juyayi na Jehovah ga mutanensa. Ta yaya?

5 Yana da wuya a yi tunanin cewa uwa za ta manta ta ciyar da jaririnta kuma ta kula da shi. Ban da haka ma, jariri ba shi da na kansa; dare da rana jariri yana bukatar ƙaunar uwar da kuma hankalinta. Abin takaici, ƙyaliya ta uwaye ba sabon abu ba ne, musamman ma a wannan “miyagun zamanu” da ta cika da rashin “ƙauna irin na tabi’a.” (2 Timothawus 3:1, 3) “Amma,” Jehovah ya ce, “ni ba ni manta da ke ba.” Jinƙai mai taushi da Jehovah yake da shi ga bayinsa ba ya ƙarewa. Ya fi motsin rai mafi taushi da za mu iya tunaninsa—juyayi da uwa take yi na jaririnta. Saboda haka ba abin mamaki ba ne da mai ba da sharhi ya ce game da Ishaya 49:15: “Wannan yana ɗaya daga cikin nuna ƙauna mafi ƙarfi, idan ma ba mafi ƙarfi ba ke nan na Allah a cikin Tsohon Alkawari.”

6. Yaya mutane ajizai da yawa suke ɗaukan tausayi mai taushi, amma menene Jehovah ya tabbatar mana?

 6 Jinƙai mai taushi alamar kumamanci ne? Mutane ajizai da yawa suna da wannan ra’ayin. Alal misali, ɗan falsafa na Romawa Seneca, wanda tsarar Yesu ne kuma fitaccen masani ne a Roma, ya yi tunani cewa “tausayi kasawa ne na zuciya.” Seneca maɗaukaki ne na Kamau, Kamau falsafa ce da take nanata kamewa da ba ta da motsin rai. Mutum mai hikima zai iya taimakon waɗanda suke wahala, in ji Seneca, amma kada ya ƙyale kansa ya ji tausayi, domin irin wannan motsin rai zai hana shi kwanciyar rai. Irin wannan rayuwa ta maƙo ba ta ba da zarafin yin juyayi ba. Amma ba haka Jehovah yake ba ko kaɗan! A cikin Kalmarsa, Jehovah ya tabbatar mana cewa shi “ke cike da tausayi, mai-jinƙai ne kuma.” (Yaƙub 5:11) Kamar yadda za mu gani, jinƙai ba kumamanci ba ne amma hali ne mai ƙarfi, mai muhimmanci. Bari mu gani yadda Jehovah yake yinsa, kamar iyaye masu ƙauna.

Sa’ad da Jehovah Ya Yi wa Wata Al’umma Jinƙai

7, 8. A wace hanya ce Isra’ilawa suka wahala a ƙasar Masar ta dā, kuma yaya Jehovah ya amsa wahalarsu?

7 Juyayin Jehovah ya bayyana sarai a hanyar da ya bi da al’ummar Isra’ila. A ƙarshen ƙarni na 16 K.Z., miliyoyin Isra’ilawa suna bauta a ƙasar Masar, inda aka ci zalinsu ƙwarai. Masarawa “suka baƙanta musu rai kuma da bauta mai-wuya, aikin kwaɓi da tubula.” (Fitowa 1:11, 14) A cikin wahalarsu Isra’ilawan suka yi kuka ga Jehovah domin taimako. Yaya Allah mai jinƙai mai taushi ya amsa?

8 Ta taɓa zuciyar Jehovah. Ya ce: “Hakika na ga ƙuncin mutanena waɗanda ke cikin Masar, na kuwa ji kukarsu  saboda shugabanninsu na gandu; gama na san baƙinzuciyarsu.” (Fitowa 3:7) Ba zai yiwu ba Jehovah ya ga wahalar mutanensa ko kuma ya ji kukarsu bai yi juyayinsu ba. Kamar yadda muka gani a Babi na 24 na wannan littafin, Jehovah Allah mai tausayi ne. Kuma tausayi—iya fahimtar wahalar wasu ne—ɗan’uwan juyayi ne. Amma Jehovah bai yi juyayin mutanensa kawai ba; ya motsa ya aikata dominsu. Ishaya 63:9 ta ce: “Cikin ƙaunarsa da cikin tausayinsa ya fanshe su.” Da “hannu mai-ƙarfi,” Jehovah ya ceci Isra’ilawa daga ƙasar Masar. (Kubawar Shari’a 4:34) Daga baya, ya yi musu tanadin abinci cikin mu’ujiza kuma ya kai su cikin ƙasarsu mai ni’ima.

9, 10. (a) Me ya sa Jehovah ya ceci Isra’ilawa a kai a kai bayan sun zauna a Ƙasar Alkawari? (b) A zamanin Jephthah, Jehovah ya ceci Isra’ilawa daga wane zalunci, kuma menene ya motsa shi ya yi haka?

9 Juyayin Jehovah bai tsaya a nan ba. Sa’ad da suka zauna a Ƙasar Alkawari, a kai a kai Isra’ilawa suke komawa ga rashin aminci kuma suka wahala domin haka. Amma sa’ad da mutanen suka komo hankalinsu sai suka yi kuka wa Jehovah. A kai a kai yake ta cetonsu. Me ya sa? “Domin yana jin juyayin mutanensa.”—2 Labarbaru 36:15; Alƙalawa 2:11-16.

10 Ka lura da abin da ya faru a zamanin Jephthah. Tun da Isra’ilawan sun koma ga bautar allolin ƙarya, Jehovah ya ƙyale Ammoniyawa suka ci zalinsu na shekara 18. A ƙarshe Isra’ilawan suka tuba. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana: “Suka rabu da baƙin allolin da ke tare da su, suka bauta ma Ubangiji: ransa kuwa ya ɓaci saboda azabar Isra’ila.” * (Alƙalawa 10:6-16) Muddin  da mutanensa suka nuna tuba ta gaskiya, Jehovah ba zai jimre ba kuma ya ga suna wahala. Sai Allah mai juyayi mai taushi ya ba wa Jephthah iko ya ceci Isra’ilawa daga hannun abokan gabansu.—Alƙalawa 11:30-33.

11. Daga sha’ani da Jehovah ya yi da Isra’ilawa, me muka koya game da juyayi?

11 Menene sha’anin Jehovah da al’ummar Isra’ila ta koya mana game da jinƙai mai taushi? Abu ɗaya shi ne, muna gani cewa ba kawai tausayi ba ne na sanin wahalar da wasu mutane suke fuskanta. Ka tuna da misalin uwa wadda juyayi ya motsa ta ta amsa kukar jaririnta. Hakazalika, Jehovah yana jin kukar mutanensa. Jinƙansa mai taushi yana motsa shi ya sauƙaƙa musu wahalarsu. Ƙari ga haka, yadda Jehovah ya bi da Isra’ilawan ya koya mana cewa juyayi ba kumamanci ba ne, domin wannan hali mai taushi ya sa ya mazakuta domin mutanensa. Amma Jehovah ga rukunin bayinsa ne kawai yake yin juyayi?

Juyayin Jehovah ga Mutane

12. Ta yaya Dokar ta nuna juyayin Jehovah ga mutane?

12 Doka da Allah ya bai wa al’ummar Isra’ila ta nuna juyayinsa ga mutane. Alal misali, ka yi la’akari da damuwarsa da matalauta. Jehovah ya sani cewa yanayi da ba a zata ba zai zo da zai jefa Ba’isra’ile cikin talauci. Yaya za a bi da matalauta? Jehovah ya umurci Isra’ilawa: “Ba za ka taurare masa zuciyarka ba, ba kuwa za ka rumtse hannunka ga ɗan’uwanka matsiyaci ba. Hakika za ka ba shi, ba kuwa da jin ciwo a zuciyarka ba lokacin da ka ke ba shi: gama saboda wannan abu Ubangiji Allahnka za ya albarkace ka cikin dukan aikinka.” (Kubawar Shari’a 15:7, 10) Jehovah ya ƙara ba da doka cewa Isra’ilawa  kada su girbe bakin gonarsu gabaki ɗaya ko kuma su yi kala. Irin wannan kalar domin matsiyata ne. (Leviticus 23:22; Ruth 2:2-7) Sa’ad da al’ummar ta bi wannan dokar game da matalauci a tsakaninsu, mabukata a Isra’ila ba sa roƙon abinci. Wannan ba nuna juyayi ba ne mai taushi na Jehovah?

13, 14. (a) Ta yaya Dauda ya tabbatar mana cewa Jehovah yana damuwa da kowannenmu sosai? (b) Ta yaya za a kwatanta cewa Jehovah yana kusa da waɗanda suka ‘karaya a zuciya’ ko a “ruhu”?

13 A yau ma, Allahnmu mai ƙauna yana damuwa ƙwarai game da mu. Za mu iya tabbata cewa yana sane da duk wata wahala da muke sha. Mai Zabura Dauda ya rubuta: “Idanun Ubangiji suna fuskanta wajen masu-adalci; kunnuwansa kuma a buɗe su ke ga jin ƙararsu. Ubangiji yana kusa da masu-karyayyar zuciya, yana ceton irin waɗanda su ke da ruhu mai-tuba.” (Zabura 34:15, 18) Game da waɗanda aka kwatanta da waɗannan kalmomi, wani mai sharhi na Littafi Mai Tsarki ya lura cewa: “Masu karyayyen zukata ne da baƙin ciki a ruhu, wato, sun natsu saboda zunubi, ba su da daraja a idanunsu, kuma ba su da tabbaci na tamaninsu.” Irin waɗannan za su ji cewa Jehovah yana da nesa kuma ba su da wani muhimmanci da zai damu da su. Amma ba haka ba ne. Kalmomin Dauda sun tabbatar mana da cewa Jehovah ba ya yasar da waɗanda “ba su da daraja a idanunsu.” Allahnmu mai juyayi ya sani cewa a irin wannan lokaci, suna bukatarsa fiye da dā, kuma yana kusa.

14 Ka yi la’akari da wannan labarin. Wata uwa a Amirka ta hanzarta ɗanta ɗan shekara biyu zuwa asibiti da yake da tari mai tsanani. Bayan an gwada yaron, likitocin suka gaya wa uwar dole ne su riƙe yaron na kwana ɗaya a asibiti. A ina uwar ta kwana? A kan kujera a  asibitin kusa da gadon ɗanta! Ɗanta ƙarami yana ciwo, kuma dole ne ta kasance kusa da shi. Hakika za mu yi tsammanin fiye da haka ma daga Ubanmu na samaniya mai ƙauna! Tun da ma, an halicce mu a cikin surarsa. (Farawa 1:26) Kalmomi masu taɓa zuciya na Zabura 34:18 sun gaya mana cewa sa’ad da muka ‘karaya a zuciya’ ko kuma a “ruhu”—kullum yana shirye ya yi taimako.

15. A waɗanne hanyoyi ne Jehovah yake taimakonmu?

15 To, ta yaya Jehovah yake taimakonmu? Ba dole ba ne ya cire tushen wahalarmu. Amma Jehovah ya yi tanadi mai yawa domin waɗanda suke kuka gare shi. Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki ta ba da shawara mai kyau da za ta yi amfani. A cikin ikilisiya, Jehovah ya yi tanadin masu kula ƙwararru a ruhaniya, waɗanda suke ƙoƙari su nuna irin juyayinsa wajen taimakon ’yan’uwa masu bi. (Yaƙub 5:14, 15) Da yake “mai-jin addu’a” ne, yana ba da “ruhu mai-tsarki ga waɗanda su ke roƙonsa.” (Zabura 65:2; Luka 11:13) Wannan ruhun zai iya cika mu da “mafificin girman iko” domin mu jimre har sai Mulkin Allah ya cire dukan wahala. (2 Korinthiyawa 4:7) Ba ma godiya ne ga dukan waɗannan tanadodi? Kada mu manta cewa nuna juyayi ne mai taushi na Jehovah.

16. Wanne ne misalin jinƙai mafi girma na Jehovah, kuma ta yaya ya shafe mu?

16 Hakika, misalin juyayi mafi girma na Jehovah shi ne ba da Wanda yake ƙauna ƙwarai fansa dominmu. Hadaya ce ta ƙauna daga Jehovah, kuma ta buɗe hanya domin cetonmu. Ka tuna cewa wannan tanadi na fansa ya shafe mu. Da kyakkyawan dalili, Zechariah, uban Yohanna mai Baftisma, ya annabta cewa wannan tanadin ya ɗaukaka “jinƙai mai-taushi na Allahnmu.”—Luka 1:78.

 Sa’ad da Jehovah Ya Ƙi Yin Juyayi

17-19. (a) Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa tausayin Jehovah ba wai ba shi da iyaka ba ne? (b) Menene ya sa juyayin Jehovah ya kai ƙarshensa?

17 Za mu yi tunani ne cewa juyayin Jehovah ba shi da iyaka? Akasarin haka, Littafi Mai Tsarki ya nuna haka a batun wasu mutane da suka yi gāba da hanyoyinsa na adalci, Jehovah ya ƙi yin juyayi yadda ya dace. (Ibraniyawa 10:28) Domin mu ga abin da ya sa ya yi haka, ka tuna misalin al’ummar Isra’ila.

18 Ko da yake Jehovah ya ceci Isra’ilawa a kai a kai daga abokan gābansu, juyayinsa daga bisani ya kai ƙarshensa. Waɗannan mutane masu taurin kai suna bauta wa gumaka, har suna kawo gumakansu abin ƙyama cikin haikalin Jehovah! (Ezekiel 5:11; 8:17, 18) Bugu da ƙari, an gaya mana: “Suka yi ma manzannin Allah ba’a, suka rena maganatasa, suka yi ma annabawansa zunɗa, har fushin Ubangiji ya tashi bisa kan mutanensa, har babu magani.” (2 Labarbaru 36:16) Isra’ilawan suka kai lokacin da babu wani dalili mai kyau na juyayi, kuma suka sa Jehovah ya yi fushi na adalci. Menene sakamakon haka?

19 Jehovah ba zai yi juyayin mutanensa ba kuma. Ya furta: “Ba ni jin tausayi, ba ni keɓewa, ba ni yin juyayi ba, har da zan bar halaka su.” (Irmiya 13:14) Saboda haka, aka halaka Urushalima da kuma haikalinta, kuma aka kwashi Isra’ilawa zuwa bauta a Babila. Bala’i ne sa’ad da mutane masu zunubi suka yi tawaye har sai da suka kai ƙarshen juyayin Allah!—Makoki 2:21.

20, 21. (a) Menene zai faru idan juyayi na Allah ya kai ƙarshensa a zamaninmu? (b) Wane tanadi ne na juyayi na Jehovah za mu tattauna a babi na gaba?

20 Yau kuma fa? Jehovah bai sake ba. Cikin juyayi,  ya umurci Shaidunsa su yi wa’azin ‘bishara ta mulki’ a dukan duniya. (Matta 24:14) Sa’ad da mutane masu zuciyar kirki suka yi na’am, Jehovah yana taimakonsu su fahimci saƙon Mulki. (Ayukan Manzanni 16:14) Amma wannan aikin ba zai ci gaba har abada ba. Ba zai kasance juyayi ba Jehovah ya ƙyale wannan muguwar duniya da dukan masifunta da wahaloli, ta ci gaba dindindin. Sa’ad da juyayinsa ya kai ƙarshensa, Jehovah zai zo ya zartar da hukunci a kan wannan zamanin. Har a lokacin ma zai aikata cikin juyayi—juyayi bisa “sunansa mai-tsarki” da kuma bayinsa masu ba da kai. (Ezekiel 36:20-23) Jehovah zai share mugunta ya kawo nagarta a sabuwar duniya. Game da miyagu, Jehovah ya ce: “Idona ba za ya keɓe ba, ba kuwa zan ji tausayi ba, amma zan jawo ma kansu alhakin aikinsu.”—Ezekiel 9:10.

21 Har sai wannan lokaci, Jehovah yana yin juyayi ga mutane, har da waɗanda suke fuskantar halaka. Mutane masu zunubi waɗanda suka tuba da gaske za su amfana daga tanadi mai girma ɗaya na juyayi na Jehovah—gafara. A babi na gaba, za mu tattauna misalai masu kyau na Littafi Mai Tsarki da suka nuna cikakken gafartawa ta Jehovah.

^ sakin layi na 3 Amma, a Zabura 103:13, aikatau na Ibrananci ra·chamʹ yana nufin jinƙai, ko kuma juyayi, da uba yake yi wa ’ya’yansa.

^ sakin layi na 10 Furcin nan “ransa kuwa ya ɓaci” a zahiri yana nufin “ruhunsa ya gajarta; haƙurinsa ya ƙare.” The New English Bible ya ce: “Ya kasa jimrewa ya ga wahalar Isra’ila.” Tanakh—A New Translation of the Holy Scriptures ya fassara shi: “Ya kasa jimre wa azabar Isra’ila.”