Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 5

Aminan Allah Za Su Zauna A Cikin Aljanna

Aminan Allah Za Su Zauna A Cikin Aljanna

Aljanna ba za ta zama kamar duniyar da muke zaune cikinta yanzu ba. Allah bai yi niyya cewa duniya za ta zama da damuwa ko baƙin ciki ko azaba ko kuma wahala ba. A nan gaba, Allah zai mayar da duniya ta zama aljanna. Yaya Aljanna za ta zama? Bari mu ga abin da Littafi Mai Tsarki ya ce:

Mutanen kirki. Aljanna za ta zama gidan aminan Allah. Za su yi abubuwa masu kyau wa juna. Za su bi tafarkin adalci na Allah a rayuwarsu.—Misalai 2:21.

Abinci da yawa. Ba za a yi yunwa a cikin aljanna ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Za a yi albarkar hatsi [ko, abinci] a ƙasa.”—Zabura 72:16.

Gidaje masu kyau da kuma aiki mai ƙayatarwa. A cikin aljanna, kowace iyali za su sami gidan kansu. Kowa zai yi aikin da zai kawo masa farin ciki na gaske.—Ishaya 65:21-23.

Zaman lafiya a dukan duniya. Mutane ba za su riƙa yaƙi ko kuma su mutu a yaƙi ba. Kalmar Allah ta ce: “[Allah] ya sa yaƙoƙi su ƙare.”—Zabura 46:8, 9.

Ƙoshin lafiya. Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari: “Wanda ya ke zaune a ciki [Aljanna] ba za ya ce, Ina ciwo ba.” (Ishaya 33:24) Ƙari ga haka, babu wanda zai zama gurgu ko makaho ko kurma ko bebe.—Ishaya 35:5, 6.

Ƙarshen azaba, baƙin ciki, da kuma mutuwa. Kalmar Allah ta ce: “Mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin zuciya, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari sun shuɗe.”—Ru’ya ta Yohanna 21:4.

Miyagun mutane ba za su kasance ba. Jehovah ya yi alkawari: “Za a datse miyagu daga cikin ƙasan, za a tumɓuke masu-cin amana kuma.”—Misalai 2:22.

Mutane za su ƙaunaci juna kuma za su daraja juna. Rashin gaskiya, zalunci, haɗama, da kuma ƙiyayya ba za su sake kasancewa ba. Mutane za su zama masu haɗin kai kuma za su yi rayuwa bisa ƙa’idodin Allah.—Ishaya 26:9.