Za Ka Iya Zama Aminin Allah!

Wannan bayanin zai taimaka maka ka ga yadda za ka iya yin hakan.

DARASI NA 1

Allah Yana Gayyatarka Ka Zama Amininsa

Mutane daga wurare dabam-dabam suna zama aminan Allah. Kai ma za ka iya zama amininsa.

DARASI NA 2

Allah Shi ne Amini Na Kwarai da Za Ka Taba Samu

Zai iya gaya maka yadda za ka sami farin ciki da kwanciyar hankali.

DARASI NA 3

Kana Bukatar Ka San ko Waye ne Allah

Hakan zai taimaka maka ka san abin da Allah yake so da wanda ya tsana.

DARASI NA 4

Yadda Za Ka Koya Game Da Allah

Ya sa ya yiwu mu san abubuwan da ya yi a dā da wadanda yake yi yanzu da kuma wadanda zai yi a nan gaba.

DARASI NA 5

Aminan Allah Za Su Zauna A Cikin Aljanna

Aljanna ba za ta zama kamar duniyar da muke ciki yanzu ba. Yaya za ta zama?

DARASI NA 6

Aljanna Ta Yi Kusa!

Wane tabbaci muke da shi?

DARASI NA 7

Gargadi Daga Abin da Ya Faru a Dā

Mene ne za mu iya koya daga labarin Nuhu da ke Littafi Mai Tsarki?

DARASI NA 8

Su Waye ne Abokan Gāban Allah?

Za ka iya gane mugayen nan kuma ka guje su.

DARASI NA 9

Su Waye Aminan Allah?

Kuma me suke so mutane su sani game da Jehobah?

DARASI NA 10

Yadda Za Ka Gane Addini na Gaskiya

Akwai abubuwa da yawa da za su iya taimaka maka ka gane addini na gaskiya.

DARASI NA 11

Ka Ki Addinin Karya!

Ta yaya za ka san addinin karya? Me ya sa addinin karya bai da kyau?

DARASI NA 12

Me Ke Faruwa Bayan Mutuwa?

Littafi Mai Tsarki ya ba mu amsar.

DARASI NA 14

Aminan Allah Suna Guje Ma Abin da Ba Shi da Kyau

Wadanne irin abubuwa ne Allah ba ya so?

DARASI NA 15

Aminan Allah Suna Yin Abin da Yake da Kyau

Wadanne abubuwa ne za mu yi don mu zama aminan Allah?

DARASI NA 16

Ka Nuna Cewa Kana Ƙaunar Allah

Idan kana so abokantakarku ta yi karfi wajibi ne ku rika magana, ka ji abin da amininka yake fada, shi ma ya ji abin da kake gaya masa kuma ku rika gaya wa wasu abin kirki game da aminanku. Haka yake da zama aminin Allah.

DARASI NA 17

Ka Zama Aboki na Kwarai Idan Kana So Ka Sami Abokai na Kwarai

Idan ka ci gaba da koyo game da Jehobah, kaunarka a gare shi za ta karu.

DARASI NA 18

Ka Zama Aminin Allah Har Abada!

Rai na har abada kyauta ce mai kyau da Allah zai ba wa aminansa.