Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 2

Allah Shi ne Amini Na Kwarai da Za Ka Taba Samu

Allah Shi ne Amini Na Kwarai da Za Ka Taba Samu

Zama aminin Allah zai sa ka sami albarka da ba ya misaltuwa. Allah zai koya maka yadda za ka sami farin ciki da kwanciyar rai; zai fitar da kai daga imani da yawa da ba daidai ba, da kuma al’adu masu yin lahani. Zai ji addu’o’inka. Zai taimake ka ka more kwanciyar hankali da kuma aminci. (Zabura 71:5; 73:28) Allah zai ba ka goyon baya a lokutan wahala. (Zabura 18:18) Kuma Allah zai ba ka kyautarsa ta rai na har abada.—Romawa 6:23.

Yayin da kake kusantar Allah, za ka kusaci aminan Allah. Za su zama aminanka su ma. Da gaske, za su zama maka kamar ’yan’uwa maza da mata. Za su yi farin cikin koya maka game da Allah, za su taimake ka kuma za su ƙarfafa ka.

Ba daidai muke da Allah ba. Yayin da kake ƙoƙari ka zama aminin Allah, dole ka tuna wani abu da yake da muhimmanci sosai. Zama aminin Allah ba abota tsakanin waɗanda suke daidai ba ne. Ya fi mu girma sosai, ya fi mu hikima, ya fi mu kuma iko sosai. Shi ne Sarkinmu da ya dace. Saboda haka, idan muna so mu zama aminansa, dole ne mu saurare shi kuma mu yi abin da ya gaya mana mu yi. Wannan zai yi mana amfani kullum.—Ishaya 48:18.