Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 3

Kana Bukatar Ka San ko Waye ne Allah

Kana Bukatar Ka San ko Waye ne Allah

Don ka zama aminin Allah, kana bukatar ka koya game da shi. Aminanka sun san sunanka kuma suna kiranka da shi? Hakika, sun sani. Allah ma yana so ka san sunansa kuma ka yi amfani da shi. Sunan Allah Jehobah ne. (Zabura 83:18; Matta 6:9) Dole ka koyi kuma ka san abin da yake so da abin da ba ya so. Kana bukatar ka san su waye aminansa kuma su waye abokan gabansa. Sanin wani yakan ɗauki lokaci. Littafi Mai-Tsarki ya ce hikima ce a keɓe lokaci a koyi game da Jehobah.—Afisawa 5:15, 16.

Aminan Allah suna yin abin da yake faranta masa rai. Ka yi tunani game da aminanka. Idan kana yi musu abin da ba shi da kyau kuma kana yin abubuwan da ba sa so, za su ci gaba da zama aminanka? Babu shakka, ba za su ci gaba ba! Haka nan, idan kana so ka zama aminin Allah, kana bukatar ka yi abin da zai faranta masa rai.—Yohanna 4:24.

Ba dukan addinai ba ne suke sa mutum ya zama aminin Allah. Yesu wanda shi ne babban aminin Allah, ya yi maganar hanyoyi biyu. Ɗayar hanyar tana da faɗi kuma tana cike da mutane. Wannan hanyar tana kai wa zuwa ga halaka. Ɗayar hanyar kuma matsatsiya ce mutane ƙalilan ne suke bin ta. Wannan hanyar tana kai wa zuwa rai madawwami. Wannan yana nufin cewa idan kana so ka zama aminin Allah, dole ne ka koyi hanyar bauta masa da take daidai.—Matta 7:13, 14.