21-27 ga Yuli
KARIN MAGANA 23
Waƙa ta 97 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)
1. Shawarwari Masu Kyau Game da Shan Giya
(minti 10)
Idan ka zaɓa ka sha giya, kada ka sha har ka bugu (K. Ma 23:20, 21; w04 12/1 shafi na 28 sakin layi na 5-6)
Ka tuna cewa yawan shan giya na jawo mummunar sakamako (K. Ma 23:29, 30, 33-35; it-1-E 656)
Kada ka bar ruwan inabi ya jarrabce ka (K. Ma 23:31, 32)
2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
(minti 10)
-
K. Ma 23:21—Mene ne bambancin yawan cin abinci da kuma mummunar kiɓa? (w04-E 11/1 31 sakin layi na 2)
-
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?
3. Karatun Littafi Mai Tsarki
(minti 4) K. Ma 23:1-24 (th darasi na 5)
4. Fara Magana da Mutane
(minti 2) WAꞌAZI A INDA JAMAꞌA SUKE. (lmd darasi na 3 batu na 5)
5. Komawa Ziyara
(minti 5) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Ka nuna wa mutumin yadda muke nazari da mutane. (lmd darasi na 9 batu na 5)
6. Almajirtarwa
(minti 5) Ka ƙarfafa ɗalibinka ya shawo kan wani hali marar kyau da yake da shi. (lmd darasi na 12 batu na 4)
Waƙa ta 35
7. Shin Zai Dace In Ba da Giya a Bikina ko Kada In Bayar?
(minti 8) Tattaunawa.
Idan mutum yana bikin aure ko liyafa, zai dace ya ba da giya ne? Wannan zaɓi ne da mai bikin zai yanke da kansa, amma ƙaꞌidodin Jehobah ne za su taimaka masa ya yanke shawara mai kyau game da batun.
Ku kalli BIDIYON Zai Dace In Ba da Giya a Bikina? Sai ka tambayi masu sauraro:
-
Ta yaya ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki na gaba za su taimaki mai bikin ya san ko zai dace ya ba da giya ko aꞌa?
-
Yoh 2:9—Yesu ya canja ruwa ya zama ruwan inabi a wani bikin aure.
-
1Ko 6:10—“Masu buguwa . . . ba waninsu da zai shiga Mulkin Allah.”
-
1Ko 10:31, 32—Saꞌad da “kuke ci, ko kuke sha ku yi kome saboda ɗaukakar Allah. Kada ku zama dalilin yin zunubi.”
-
-
Waɗanne yanayoyi ne kuma za mu yi tunani a kai?
-
Don mu yanke shawara mai kyau, me ya sa zai dace mu yi amfani da hankalinmu da tunaninmu don mu fahimci ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki kuma mu bi?—Ro 12:1; M. Wa 7:16-18
8. Bukatun Ikilisiya
(minti 7)
9. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya
(minti 30) lfb darasi na 2, gabatarwar sashe na 2, da kuma darasi na 3