Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 40

Waye ne Allahnka?

Ka Zabi Sauti
Waye ne Allahnka?

(Romawa 14:⁠8)

 1. 1. Wa za ka bauta wa?

  Wa za ka wa biyayya?

  Wanda kake yi wa biyayya

  Ne Allahnka da ka zaɓa.

  Ba a iya bauta

  Wa Alloli biyu ba.

  Don haka, kai za ka zaɓi Allahn

  Da za ka wa biyayya.

 2. 2. Wa za ka bauta wa?

  Wa za ka wa biyayya?

  Jehobah Allah ne ko Shaiɗan?

  Ka zaɓi Allahnka yanzu.

  Shin za ka bauta wa

  Sarakunan duniya?

  Ko dai Jehobah za ka bauta wa

  Kuma ka yi nufinsa?

 3. 3. Waye zan bauta wa?

  Jehobah ne Allahna.

  Allah na sama zan bauta wa,

  Zan bi dukan dokokinsa.

  Yana so na sosai.

  Shi kaɗai zan bauta wa.

  Zan bauta masa duk rayuwata.

  Zan girmama sunansa.

(Ka kuma duba Josh. 24:15; Zab. 116:​14, 18; 2 Tim. 2:19.)