Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 97

Kalmar Allah Za Ta Sa Mu Rayu

Ka Zabi Sauti
Kalmar Allah Za Ta Sa Mu Rayu
DUBA

(Matta 4:4)

 1. 1. Kalmar Allah na ba da rai

  Mai inganci sosai.

  Kalmar tana da tamani,

  Fiye da abinci.

  Muna cin amfanin Kalmar,

  Yau da kuma gobe.

  (AMSHI)

  Wajibi ne mu karanta

  Kalmar Allah sosai.

  Karanta Kalmar za ta sa

  Mu amfana sosai.

 2. 2. Kalmar Allah na sa mu san

  Labaran mutane,

  Mutane amintattu fa,

  Masu gaba gaɗi.

  Karanta duk labarinsu

  Yana ƙarfafa mu.

  (AMSHI)

  Wajibi ne mu karanta

  Kalmar Allah sosai.

  Karanta Kalmar za ta sa

  Mu amfana sosai.

 3.  3. DKoyaushe in mun karanta

  Kalmar Maɗaukaki,

  Tana ƙarfafa mu sosai,

  Tana sa mu jimre.

  In mun daraja Kalmarsa,

  Za mu sami bege.

  (AMSHI)

  Wajibi ne mu karanta

  Kalmar Allah sosai.

  Karanta Kalmar za ta sa

  Mu amfana sosai.

(Ka kuma duba Josh. 1:8; Rom. 15:4.)