Koma ka ga abin da ke ciki

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Damar Zaban Abin da Za Mu yi? Allah ne mai ikon?

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Damar Zaban Abin da Za Mu yi? Allah ne mai ikon?

Amsar da Littafi Mai Tsarki ya ba da

Allah ya ba mu damar zaban abin da muke son mu yi maimakon Allah ya kaddara dukan abin da zai faru da mu. Ka bincika abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar.

  • Allah ya halicci mutane cikin kamaninsa. (Farawa 1:26) Mu ba kamar dabbobi ba ne da ilhami ke musu ja-gora amma muna kama da Mahaliccinmu da ke da kauna da kuma gaskiya. Mu ma muna iya zaban abin da za mu yi kamar Mahaliccinmu.

  • Zai iya yiwuwa mu san wasu abubuwan da za su iya faruwa da mu a nan gaba. Littafi Mai Tsarki ya karfafa mu mu “zaɓi rai” ta . . . ‘jin muryarsa,’ wato bin dokokinsa. (Kubawar Shari’a 30:19, 20) Wannan ba zai kasance da amfani ba da a ce ba a ba mu damar zaban abin da za mu yi ba. Allan bai tilasta mana ba amma ya ce: “Da ma ka yi sauraro ga dokokina! da hakanan ne da salamarka ta yi kamar kogi, adalcinka kuma kamar rakuman teku.”—Ishaya 48:18.

  • Allah ba ya kaddara samun nasara ko fadiwarmu ba. Idan muna son mu yi nasara dole ne mu yi aiki sosai. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Dukan abin da hannunka ya iske na yi, ka yi shi da karfinka.” (Mai-Wa’azi 9:10) Littafi Mai Tsarki ya kara da cewa: “Tunanin mai-himma zuwa yalwata kadai su ke nufa.”—Misalai 21:5.

Damar da Allah ya ba mu na tsai da shawara kyauta ce daga wurinsa. Kuma hakan yana sa mu kaunace shi da ‘dukan zuciyarmu’ da yake burinmu ne mu yi hakan.—Matta 22:37.

Allah ne mai iko da dukan abubuwa kuwa?

Littafi Mai Tsarki ya ce Allah shi ne Mai iko duka kuma ba wanda ya kai shi iko. (Ayuba 37:23; Ishaya 40:26) Amma, ba ya amfani da ikonsa kawai ya mallaki kome. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce Allah ya “daure” da Babila ta dā da ta yi gāba da mutanensa. (Ishaya 42:14) Hakazalika, a yau Allah ya kyale wadanda suke amfani da ikon da suke da shi wajen cutar wasu. Amma Allah ba zai yi shuru har abada ba.—Zabura 37:10, 11.