Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Shaidun Jehobah

Hausa

Shin Allah Ya Kaddara Lokacin da Za Mu Mutu Ne?

Shin Allah Ya Kaddara Lokacin da Za Mu Mutu Ne?

Amsar da Littafi Mai Tsarki ya ba da

A’a, Allah bai kaddara mana lokacin da za mu mutu ba. Littafi Mai Tsarki bai goyi bayan yin imani da kaddara ba, a maimakon haka, ya ce “tsautsayi” ne ke jawo mutuwa.—Mai-Wa’azi 9:11, Littafi Mai Tsarki.

Littafi Mai Tsarki ya ce akwai “lokacin mutuwa”, ko ba haka ba?

Hakika, littafin Mai-Wa’azi 3:2 ya ce “akwai lokacin haihuwa, da lokacin mutuwa: lokacin yin dashe, da lokacin tumbuke abin da aka dasa.” Amma wannan nassin yana nuni ne ga juyin yanayin rayuwa da muke gani kullum. (Mai-Wa’azi 3:1-8) Allah bai kaddara lokacin da za mu mutu ba, kamar yadda ba ya tilasta wa manomi ya yi shuki a lokacin da bai ga dama ba. Saboda haka, wannan nassin yana tuna mana muhimmancin yi wa Mahaliccinmu hidima da dukan ranmu maimakon mu ba wa abubuwa marar muhimmanci fifiko.—Mai-Wa’azi 3:11; 12:1, 13.

Za mu iya yin rayuwa mai tsawo

Duk da matsalolin da muke da su, za mu iya yin rayuwa na dogon lokaci idan muka tsai da shawarwari masu kyau. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Koyarwar mai-hikima mabulbular rai ne, da za a rabu da tarkunan mutuwa.” (Misalai 13:14) Haka ma Musa ya gaya wa Isra’ilawa cewa za su iya yin rayuwa na ‘tsawon’ lokaci’ idan suka bi dokokin da Allah ya ba su. (Kubawar Shari’a 6:2) Akasin haka, za mu iya gajerta kwanakin rayuwarmu idan muka tsai da shawarwari da ba su dace ba.—Mai-Wa’azi 7:17.

Amma ba za mu iya guje wa mutuwa ba, ko da mun tsai da shawarwari masu kyau a rayuwa. (Romawa 5:12) Wannan yanayin zai canja, domin Allah ya yi mana alkawari a cikin Littafi Mai Tsarki cewa akwai lokacin da “mutuwa kuwa ba za ta kara kasancewa ba.”—Ru’ya ta Yohanna 21:4.