Koma ka ga abin da ke ciki

Sun Saka Alama Mai Kalar Algashi (Purple) a Rigunansu

Sun Saka Alama Mai Kalar Algashi (Purple) a Rigunansu

 Maud tana zama a Faransa kuma tana aiki a wata makaranta inda take taimaka wa yara nakasassu a lokacin da suke aji. A kwanan nan, an koya wa yara a wani aji game da Kisan Kāre Dangi da ꞌyan Nazi suka yi wa Yahudawa da kuma sansanonin aiki da suka kafa. Fursunoni da suke sansanin sun saka riguna masu alama. Kalar da kuma yadda aka yanka alamar ne suke nuna dalilin da ya sa aka saka mutumin a kurkuku.

 Saꞌad da malamin yake magana game da alama mai kalar Algashi da wasu fursunoni suka saka, ya ce: “Ina ganin an sa su a kurkuku domin su ꞌyan luwadi ne.” Bayan an tashi, Maud ta bayyana wa malamin cewa ꞌyan Nazi sun yi amfani da alama mai kalar Algashi don su bambanta Shaidun Jehobah. a Ta ce za ta kawo masa wasu abubuwa da aka rubuta a kan batun. Malamin ya yarda da abin da ta ce kuma ya gaya wa Maud ta bayyana wa daliban.

 Da ake tattauna batun a wani aji, wata malama dabam ta yi amfani da taswira da ke nuna alamomi dabam-dabam da fursunonin suka saka. A taswirar an nuna cewa alama mai kalar Algashi tana nuna Shaidun Jehobah. Bayan an tashi, Maud ta bayyana ma wannan malamar wasu abubuwa a kan batun. Malamar ta amince da bayaninta kuma ta shirya Maud ta bayyana wa daliban.

Maud tana rike da littattafai da bidiyon da ta yi amfani da su

 Maud ta shirya bayani na minti 15 da za ta yi a aji na farko, amma da lokacin ya kai, sai aka gaya mata cewa: “Kina iya yin bayani na awa guda.” Maud ta soma da nuna musu bidiyo game da yadda ꞌyan Nazi suka tsananta wa Shaidun Jehobah. Bayan da aka nuna yadda ꞌyan Nazi suka dauke yara 800 daga wurin iyayensu a bidiyon, Maud ta dakatar da bidiyon kuma ta karanta labaran yara uku cikinsu. Bayan sun gama kallon bidiyon, Maud ta kammala da karanta wata wasikar ban kwana da wani Mashaidi dan kasar Austria ya rubuta a shekara 1940. Matashin dan shekara 19 mai suna Gerhard Steinacher ya rubuta wa iyayensa wannan wasikar awoyi kadan kafin ꞌyan Nazi su kashe shi. b

 Maud ta yi wa aji na biyun irin wannan bayanin. Don yadda Maud ta kasance da karfin zuciya, dukan malaman sukan ambata Shaidun Jehobah saꞌad da suke koyar wa dalibansu game da fursunoni da ke sansanonin ꞌyan Nazi.

a A lokacin Yakin Duniya na Biyu, Shaidun Jehobah a Jamus da aka san su da suna Bibelforscher (wato Daliban Littafi Mai Tsarki), an saka su a kurkuku don sun ki su goyi bayan ꞌyan Nazi.

b An yanke wa Gerhard Steinacher hukuncin kisa don ya ki ya zama sojan Jamus. A wasikarsa na ban kwana, ya rubuta cewa: “Ni karamin yaro ne har ila. Ba zan iya jurewa ba sai da taimakon Allah, kuma fatana ke nan.” An kashe Gerhard washegari da safe. An rubuta a jikin kabarinsa cewa: “Ya mutu don yana so ya daukaka Allah.”