Koma ka ga abin da ke ciki

Me Ya Sa Ake Kisan Kare Dangi? Me Ya Sa Allah Ya Kyale Hakan Ya Faru?

Me Ya Sa Ake Kisan Kare Dangi? Me Ya Sa Allah Ya Kyale Hakan Ya Faru?

 Yawancin mutanen da suke yin wadannan tambayoyin sun taba yin hasarar ’yan’uwansu da kuma abubuwa da yawa shi ya suke bukatar ƙarfafa ba samun amsoshin tambayoyin kawai ba. Wasu suna ganin cewa Kisan Kare Dangi mugunta ne sosai, saboda haka, sun shakkar cewa akwai Allah.

Rashin fahimtar gaskiya game da Allah da kuma Kisan Kare Dangi

 Kāge: Laifi ne mu tambayi dalilin da ya sa Allah ya kyale Kisan Kare Dangi.

 Gaskiya: Mutane masu bangaskiya sosai ma sun taba tambayar dalilin da ya sa Allah ya kyale mugunta. Alal misali, annabi Habakkuk ya tambayi Allah: “Me ya sa ka sa ni in ga mugunta, In kuma dubi wahala? Halaka da zalunci suna a gabana. Jayayya da gardama sun tashi.” (Habakkuk 1:3, Littafi Mai Tsarki) Allah bai tsauta wa Habakkuk ba, maimakon haka, ya sa a rubuta tambayoyin a cikin Littafi Mai Tsarki domin dukanmu mu karanta.

 Kāge: Allah bai damu da wahalar da mutane suke sha ba.

 Gaskiya: Allah ba ya son wahala da mugunta da mutane suke sha. (Misalai 6:16-19) Da Allah ya ga mugunta ta yi yawa a zamanin Nuhu, hakan “ya bata masa zuciya kwarai.” (Farawa 6:5, 6) Babu shakka, shi ya sa Kisan Kāre Dangi ba ya faranta wa Allah zuciya.—Malachi 3:6.

 Kāge: Allah yana amfani da Kisan Kāre Dangi don ya hori Yahudawa.

 Gaskiya: Hakika, Allah ya kyale Romawa na karni na farko su halaka Urushalima. (Matta 23:37–24:2) Amma, tun daga lokacin Allah ba ya horon wasu al’umma ya bar wasu ko kuma ya dauki wasu da muhimmanci fiye da wasu. A wurin Allah, “ba wani bambanci tsakanin Bayahude da Ba’al’umme.”—Romawa 10:12, Littafi Mai Tsarki.

 Kāge: In da a ce akwai Allah mai kauna da iko, da ya sa an daina Kisan Kare Dangi.

 Gaskiya: Ko da yake Allah ba ya haddasa wahala, amma a wani lokaci yana kyale mutane su sha wahala na dan lokaci.—Yakub 1:13; 5:11.

Me ya sa Allah ya kyale Kisan Kare Dangi?

 Dalili daya ne ya sa Allah ya kyale Kisan Kare Dangi da kuma shan wahala. Yana son ya gyara wani batun da ya taso a dā. Littafi Mai Tsarki ya ce, ba Allah ba ne yake mulkin wannan duniya, amma Iblis ne. (Luka 4:1, 2, 6; Yohanna 12:31) Ko da yake talifin da aka hada da wannan batun ya ba da cikakken bayanin da ya sa Allah ya kyale shan wahala, akwai wasu tabbaci guda biyu daga Littafi Mai Tsarki da za su taimake mu mu fahimci dalilin da ya sa Allah ya kyale Kisan Kare Dangi.

  1.   Su wa suka sa ake fama da Kisan Kare Dangi?

     Ko da yake Allah ya gaya wa iyayenmu na farko abin da ya kamata su yi, bai sa su dole su yi masa biyayya ba. Sun zaba wa kansu abin da suka gani kamar shi ne yin nagarta da mugunta. Kuma wannan banzan shawarar da suka yi da kuma wadanda mutane da yawa suka yi a dā ne yake sa ’yan Adam suke shan wahala sosai. (Farawa 2:17; 3:6; Romawa 5:12) Hakan ya yi daidai da abin da littafin nan Statement of Principles of Conservative Judaism ya fadi cewa: “Yawancin matsalolin da ’yan Adam suke fuskanta a yau sakamakon rashin yin amfani da damar da muke da shi na yin shawara da kyau ne.” Allah bai daina ba mu damar tsai da shawara ba, maimakon haka, ya bar mu mu tsai da shawara da kanmu ba tare da ja-gorarsa ba.

  2.   Allah zai gyara abubuwan da Kisan Kare Dangi ya batar. Allah ya yi alkawari cewa zai ta da mutanen da suka mutu har da wadanda suka mutu a sakamakon Kisan Kare Dangi. Zai ta’azantar da mutanen da ’yan’uwansu suka rasu a sakamakon wannan bala’in. (Ishaya 65:17; Ayyukan Manzanni 24:15) Kaunar da Allah yake wa ’yan Adam ya tabbatar mana da cewa Allah zai cika wannan alkawarin da ya yi.—Yohanna 3:16.

 Mutane da yawa da Kisan Kare Dangi ya shafa sun kasance da bangaskiya kuma sun yi rayuwa mai ma’ana don sun fahimci dalilin da ya sa Allah ya kyale mugunta da kuma yadda zai kawo karshenta.