Koma ka ga abin da ke ciki

Kuna Ganin Cewa Ku Kaɗai Ne Za Ku Sami Ceto?

Kuna Ganin Cewa Ku Kaɗai Ne Za Ku Sami Ceto?

 A’a. Miliyoyin mutane da suka rayu ƙarnuka da suka shige da ba Shaidun Jehobah ba ne za su sami zarafin samun ceto. Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa a sabuwar duniya da Allah ya yi alkawari, “za a yi tashin matattu, na masu-adalci da na marasa-adalci.” (Ayyukan Manzanni 24:15) Ƙari ga haka, mutane da yawa da ke rayuwa yanzu za su iya soma bauta wa Allah, su ma za su iya samun ceto. Amma dai, ba aikinmu ba ne mu shar’anta wanda zai tsira da wanda ba zai tsira ba. Wannan aikin Yesu ne.—Yohanna 5:22, 27.