Samun Amincewar Allah Tabbaci Ne Cewa Za Mu Tsira A Karshe?

Samun Amincewar Allah Tabbaci Ne Cewa Za Mu Tsira A Karshe?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 A’a, Littafi Mai Tsarki bai ce idan Allah ya amince da mu yau, hakan tabbaci ne cewa za mu sami tsira a karshe ba. Idan mutum ya yi imani da Yesu yau kuma ya kulla dangantaka mai kyau da Allah, zai iya bata wannan dangantakar a nan gaba idan bai mai da hankali ba. Littafi Mai Tsarki ya ce wajibi ne mu “dāge” da gaske idan muna so mu ci gaba da yin imani da Yesu. (Yahuda 3, 5) Shi ya sa aka gaya wa Kiristoci da suka riga suka kulla dangantaka da Allah a karni na farko cewa: “Ku yi aikin cetonku da tsoro da rawan jiki.”—Filibiyawa 2:12.

Ayoyin da suka nuna cewa wannan ra’ayin bai jitu da koyarwar Littafi Mai Tsarki ba

  •   A cikin Littafi Mai Tsarki an yi magana game da zunubai masu tsanani da za su iya hana mu shiga Mulkin Allah. (1 Korintiyawa 6:9-11; Galatiyawa 5:19-21) Da a ce yana yiwuwa a sami ceto bayan Allah ya amince da mutum da farko, da ba a ba da wannan kashedin ba. Hakika, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa wanda ya sami ceto zai iya komawa ya aikata zunubi mai tsanani. Alal misali, Ibraniyawa 10:26 ta ce: “In kuwa mun ci gaba da yin zunubi da gangan, bayan mun yi na’am da sanin gaskiya, to, ba fa sauran wata hadaya domin kawar da zunubai.”—Ibraniyawa 6:4-6; 2 Bitrus 2:20-22, Littafi Mai Tsarki.

  •   Yesu ya ba da wani misalin da ya nuna cewa yana da muhimmanci mu ci gaba da yin imani da shi. A cikin misalin, ya kamanta kansa da itacen inabi, sa’an nan mabiyansa kuma da rassan itacen. Da farko, wadansu daga cikinsu za su nuna ta wurin ayyukansu ko kuma halinsu cewa sun yi imani da shi, amma daga baya za su daina yin imani da shi kuma hakan zai sa ya sāre su daga jikin itacen don kada su ‘zama reshe.’ (Yohanna 15:1-6) Manzo Bulus ma ya yi amfani da irin wannan misalin a lokacin da ya ce za a “datse” Kiristoci da suka daina yin imani da Yesu.—Romawa 11:17-22.

  •   An umurci Kiristoci su “yi tsaro.” (Matta 24:42; 25:13) Wadanda suka bar dangantakarsu da Allah ta yi tsami ta wajen yin “ayyukan duhu” wato, yin abubuwa da Allah ya haramta ko kuma ta kin yin abubuwan da Yesu ya umurce su su yi, ba za su sami ceto ba.—Romawa 13:11-13; Ru’ya ta Yohanna 3:1-3.

  •   Ayoyi da yawa a cikin Littafi Mai Tsarki sun nuna cewa wajibi ne mutum ya jimre har karshe kafin ya sami ceto. (Matta 24:13; Ibraniyawa 10:36; 12:2, 3; Ru’ya ta Yohanna 2:10) Kiristoci a karni na farko sun yi farin ciki sosai sa’ad da suka ji cewa sauran ’yan’uwansu suna jimrewa. (1 Tasalonikawa 1:2, 3; 3 Yohanna 3, 4) Kana ganin Littafi Mai Tsarki zai nanata batun jimrewa idan a karshe za a ceci wadanda ba su jimre ba?

  •   Sai da Manzo Bulus yana dab da mutuwa ne kafin ya tabbata cewa zai sami ceto. (2 Timotawus 4:6-8) Amma a lokacin da ya soma bauta wa Allah, ya san cewa idan ya bi sha’awar zuciyarsa ba zai sami ceto a karshe ba. Shi ya sa ya ce: “Ina horon jikina, na mai da shi bawana, domin kada bayan da na yi wa wadansu wa’azi, ni kaina a hana ni samun ladan cin nasara.”​—1 Korintiyawa 9:27, Littafi Mai Tsarki Juyi Mai Fitar da Ma’ana; Filibiyawa 3:12-14.