Koma ka ga abin da ke ciki

Mece ce Kalmar nan Ceto Take Nufi?

Mece ce Kalmar nan Ceto Take Nufi?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 A wasu lokatai, marubutan Littafi Mai Tsarki suna yin amfani da wadannan kalmomi “tsira” da “ceto” don su nuna cewa an ceci mutum daga hadari ko kuma halaka. (Fitowa 14:13, 14; Ayyukan Manzanni 27:20) Amma, sau da yawa wadannan kalmomin suna nufin samun ceto daga zunubi. (Matta 1:21) Tun da yake zunubi ne yake kawo mutuwa, mutanen da aka cece su daga zunubi suna da begen yin rayuwa har abada.—Yohanna 3:16, 17. a

Mene ne zai sa mutum ya sami ceto?

 Idan kana son ka samu ceto, wajibi ne ka gaskata da Yesu kuma ka nuna hakan ta wajen yin biyayya ga dokokinsa.—Ayyukan Manzanni 4:10, 12; Romawa 10:9, 10; Ibraniyawa 5:9.

 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa wajibi ne ka yi wasu ayyuka ko kuma ka rika yin biyayya don ka nuna cewa kana da bangaskiya. (Yakub 2:24, 26) Amma, hakan ba ya nufin cewa za ka sami ceto. Ceto “kyauta ce” da Allah yake bayarwa don shi mai alheri ne.—Afisawa 2:8, 9.

Shin mutum zai iya rasa samun ceto?

 Kwarai kuwa. Mutumin da aka ceci daga nitsewa zai iya fadawa kuma cikin ruwa. Hakazalika, mutumin da aka ceci daga zunubi zai iya rasa samun ceto idan bai ci gaba da kasancewa da bangaskiya ba. Saboda haka, Littafi Mai Tsarki ya umurci Kiristoci da suka samu ceto su “yi yaki domin imani.” (Yahuda 3) Kari ga haka, ya gargade wadanda suka samu ceto cewa: Su ‘yi aikin cetonsu da tsoro da rawan jiki.’—Filibiyawa 2:12.

Wane ne Mai ceto—Allah ko Yesu?

 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Allah ne ainihin mai ceto ta wajen kiransa “Mai-ceto.” (1 Sama’ila 10:19; Ishaya 43:11; Titus 2:10; Yahuda 25) Kari ga haka, Allah ya yi amfani da mutane dabam-dabam don ya ceci al’ummar Isra’ila na dā, kuma Littafi Mai Tsarki ya kira su “masu-ceto.” (Nehemiya 9:27; Alkalawa 3:9, 15; 2 Sarakuna 13:5) b Hakazalika, Littafi Mai Tsarki ya kira Yesu “Mai-ceto” tun da yake Allah ya yi tanadin ceto ta wurin hadayar fansa da Yesu Kristi ya ba da.—Ayyukan Manzanni 5:31; Titus 1:4. c

Shin za a ceci dukan mutane ne?

 A’a, ba za a ceci wasu mutane ba. (2 Tasalonikawa 1:9) Sa’ad da aka tambayi Yesu cewa: “Wadanda za su tsira ba su da yawa ba ne?” Yesu ya amsa kuma ya ce, “Ku yi kokari ku shiga ta matsatsiyar kofa: gama ina ce maku, mutane da yawa za su so su shiga, ba za su iya ba.”​—Luka 13:23, 24.

Ra’ayoyin da ba daidai ba game da samun ceto

 Karya: Littafin 1 Korintiyawa 15:22 ya ce: “Cikin Kristi duka za su rayu.” Saboda haka, za a ceci dukan mutane.

 Gaskiya: Wannan ayar tana magana ne game da tashin matattu. (1 Korintiyawa 15:12, 13, 20, 21, 35) Saboda haka, wannan ayar da ta ce “cikin Kristi duka za su rayu,” tana nufin cewa dukan wadanda za a ta da daga mutuwa za su sami albarka ta wurin Yesu Kristi.​—Yohanna 11:25.

 Karya: Littafin Titus 2:11 ya ce Allah zai kawo “ceto ga dukan mutane,” saboda haka, kowa ne zai sami ceto.

 Gaskiya: Kalmar Girkanci da aka fassara zuwa “dukan” a wannan ayar tana nufin “kowane iri.” d Saboda haka, ainihin abin da littafin Titus 2:11 yake nufin shi ne, Allah zai kawo ceto ga iri-irin mutane, kuma sun kunshi mutane daga “dukan kabilai da al’ummai da harsuna.”​—Ru’ya ta Yohanna 7:9, 10.

 Karya: Littafin 2 Bitrus 3:9 ya ce Allah “ba ya so kowa ya halaka,” saboda haka, za a ceci dukan mutane.

 Gaskiya: Allah yana son ya ceci mutane amma ba ya tilasta musu su amince da tanadin da ya yi don samun ceto. A ‘ranar shari’arsa,’ zai “halakar mutane masu-fajirci.”​—2 Bitrus 3:7.

a Littafi Mai Tsarki ya ambata cewa an ceci mutum duk da cewa lokacin da za a ceci shi ko ita daga zunubi da kuma mutuwa zai faru ne a nan gaba.​—Afisawa 2:5; Romawa 13:11.

b A cikin wadannan ayoyin da aka ambata, wasu mafassara sun yi amfani da kalmar nan “zakara” da “jarumi” da “shugaba” ko kuma su ce “wani” maimakon “mai ceto.” Amma a cikin Nassosin Ibrananci na asali, an yi amfani da kalmar nan mai ceto sa’ad da ake magana game da ’yan Adam masu ceto da Jehobah Allah a matsayin mai ceto.​—Zabura 7:10.

c An dauko wannan sunan Yesu daga sunan Ibrananci Yehoh·shuʹaʽ, wanda yake nufin “Jehobah Ne Mai Ceto.”

d Ka duba kamus nan Vine’s Complete Expository Dictionary of Old and New Testament Words. An sake ambata kalmar Girkanci nan a littafin Matta 5:​11, sa’ad da Yesu ya ce mutane za su fadi “kowacce irin” munanan abubuwa game da mabiyansa.​—International Standard Version.