Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 65

Mu Rika Samun Ci Gaba!

Ka Zabi Sauti
Mu Rika Samun Ci Gaba!
DUBA

(Ibraniyawa 6:1)

 1. 1. Mu duƙufa samun ci gaba kullum!

  Mu bar kowa ya ga halayenmu masu kyau.

  Mu yi himma a yaɗa bisharar nan,

  Allah za ya kāre mu.

  Dukanmu muna da aikin yi,

  Aikin Yesu Ubangijinmu.

  Mu roƙi Jehobah ya taimake mu,

  Don mu riƙa nagarta.

 2. 2. Duk mu ƙoƙarta mu riƙa wa’azi!

  Mu sanar da saƙon da zai sa a sami rai,

  Kuma zai sa a riƙa yabon Allah,

  Su yabe shi da ƙwazo.

  Maƙiya za su tsorata mu,

  Amma kada mu ji tsoron su.

  Mu riƙa shelar Mulkin nan da ƙwazo,

  Mu yi hakan koyaushe.

 3.  3. Duk mu ƙoƙarta mu riƙa biyayya,

  Mu riƙa inganta

  wa’azinmu koyaushe.

  Za mu bi ja-gorancin ruhun Allah

  Da duk zuciyarmu fa.

  Mu ƙaunaci dukan ɗalibai,

  Don su so Kalmar Allah sosai.

  Su riƙa samun ci gaba koyaushe,

  Haskensu ya haskaka.

(Ka kuma duba Filib. 1:27; 3:16; Ibran. 10:39.)