Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 66

Mu Rika Yada Bishara

Mu Rika Yada Bishara

(Ru’ya ta Yohanna 14:​6, 7)

 1. 1. A lokacin da Adamu da Hauwa’u

  Sun ƙarya dokokin Allah Maɗaukaki,

  Jehobah ya yi shiri don ya cece mu.

  Don ƙauna da tausayinsa ga ʼyan Adam,

  Ya naɗa Ɗansa Yesu ya sarauce mu,

  A Mulkinsa da ya kafa

  a cikin sama.

  Yesu da shafaffu za su yi mulkin nan,

  Jehobah zai albarkaci sarautarsu.

 2. 2. An yi annabci za a yi wa’azin nan.

  Mu yi shi da ƙwazo sosai ga mutane.

  Mala’ikun Jehobah na tare da mu,

  Muna yin shelar Mulkin Allah Jehobah.

  Jehobah ya danƙa mana babban gata,

  Mu girmama Allah, mu

  ɗaukaka shi sosai.

  Shaidun Jehobah shi ne ake kiran mu

  Don muna wa’azin bishara da ƙwazo.

(Ka kuma duba Mar. 4:11; A. M. 5:31; 1 Kor. 2:​1, 7.)