Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 64

Mu Rika Yin Wa’azi da Farin Ciki

Ka Zabi Sauti
Mu Rika Yin Wa’azi da Farin Ciki
DUBA

(Matta 13:​1-23)

 1. 1. Yanzu muna lokacin girbi,

  Domin shukarmu ta nuna.

  Jehobah Ubanmu a sama,

  Yana so mu yi wa’azi.

  Yesu Kristi shi ne ja-gora,

  Ya kafa misali mai kyau.

  Muna murna sosai a koyaushe.

  Don muna shelar bishara.

 2. 2. Muna yin wa’azin bishara

  Don muna ƙaunar mutane.

  Wa’azi na da muhimmanci

  Domin ƙarshe yana tafe.

  Jehobah na mana albarka,

  Yana sa mu murna sosai.

  Za mu riƙe aminci har ƙarshe

  Muna wa’azi da himma.

(Ka kuma duba Mat. 24:13; 1 Kor. 3:9; 2 Tim. 4:2.)