Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 TATTAUNAWA TSAKANIN SHAIDUN JEHOBAH DA MUTANE

Shin Ya Dace Mu Tuna da Mutuwar Yesu?

Shin Ya Dace Mu Tuna da Mutuwar Yesu?

Tattaunawar da ke gaba misali ne na yadda Shaidun Jehobah suke yi wa mutane wa’azi. A ce wata Mashaidiya mai suna Megan tana wa’azi kuma ta haɗu da wata mai suna Shirley.

“KU RIƘA YIN HAKA DOMIN TUNAWA DA NI”

Megan: Ya Shirley, na yi farin ciki da na gan ki a taron Tunawa da Mutuwar Yesu makon da ya wuce. * Kin ji daɗin taron kuwa?

Shirley: E, na ji daɗin taron, amma a gaskiya ban fahimci dukan abin da aka tattauna ba. Na san cewa mutane da yawa suna ɗaukan haihuwar Yesu, wato Kirsimati da muhimmanci fiye da mutuwarsa. Za ki iya sake bayyana mini dalilin da ya sa ya kamata mu ɗauki mutuwar Yesu da muhimmanci?

Megan: Gaskiya ne, mutane da yawa suna yin bikin Kirsimati. Amma Shaidun Jehobah sun gaskata cewa tuna da mutuwar Yesu ya fi muhimmanci. Idan kina da lokaci kaɗan zan yi farin cikin bayyana miki muhimmancinsa.

Shirley: Ba damuwa, ki ci gaba.

Megan: Hakika, Shaidun Jehobah suna tuna da mutuwar Yesu ne don ya umurci bayinsa su yi hakan. Ki yi la’akari da abin da ya faru a dare na ƙarshe kafin Yesu ya mutu. Kin tuna wani jibi na musamman da Yesu ya ci da amintattun bayinsa?

Shirley: Kina nufin Jibin Maraice?

Megan: Ƙwarai kuwa. Ana kuma ce da shi Jibin Maraice na Ubangiji. A lokacin jibin ne Yesu ya ba mabiyansa wannan umurnin. Za ki so ki karanta kalamansa a Luka 22:19?

Shirley: To. “Sai ya ɗauki gurasa, bayan ya yi godiya ga Allah, ya gutsuttsura, ya ba su, ya ce, ‘Wannan jikina ne da za a bayar dominku. Ku riƙa yin haka domin tunawa da ni.’”

Megan: Na gode. Ki lura da umurnin da Yesu ya bayar a ƙarshen wannan ayar: “Ku riƙa yin haka domin tunawa da ni.” Bayan da ya umurci mabiyansa su tuna da shi, Yesu ya bayyana musu dalla-dalla abin da ya kamata su tuna game da shi. Ya ce zai ba da ransa don mabiyansa. Yesu ya faɗi wani batu makamancin haka a Matta 20:28. Ayar ta ce: “Ɗan mutum ya zo ba domin a yi masa bauta ba, amma domin shi bauta wa waɗansu, shi ba da ransa kuma abin fansar mutane da yawa.” A taƙaice, abin da ya sa Shaidun Jehobah suke taro kowace shekara don su tuna da mutuwar Yesu ke nan. Mutuwarsa za ta sa ’yan Adam masu biyayya su sami rai na har abada.

ME YA SA MUKA BUKACI A FANSHE MU?

Shirley: Ina ji mutane suna cewa Yesu ya mutu don mu sami rai. Amma a gaskiya, ban taɓa fahimtar yadda hakan zai yiwu ba.

Megan: Yawancin mutane ma ba su fahimci hakan ba, domin batun hadayar Yesu yana da wuyar fahimta. Amma tana da ban sha’awa sosai. Kafin in ci gaba, kina da sauran lokaci?

 Shirley: E, ki ci gaba.

Megan: Na gode. Bai daɗe ba da na yi bincike a kan batun fansa, saboda haka, zan yi ƙoƙari in yi miki bayani mai sauƙi.

Shirley: To.

Megan: Idan muna so mu fahimci batun fansa, ya kamata mu fara sanin sakamakon zunubin da Adamu da Hawwa’u suka yi a lambun Adnin. Bari mu karanta Romawa 6:23 don mu fahimci wannan batun sosai. Don Allah ki karanta ayar.

Shirley: Ba damuwa. Ta ce: “Sakamakon zunubi mutuwa ne, amma baiwar Allah ita ce rai madawwami cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu.”

Megan: Na gode. Bari mu tattauna wannan ayar. Da farko, ki lura da yadda ayar ta soma: “Sakamakon zunubi mutuwa ne.” Wannan ne ƙa’idar da Allah ya kafa tun farkon halittar mutum, cewa sakamakon zunubi mutuwa ne. Hakika, da farko babu wanda ke zunubi. Allah ya halicci Adamu da Hawwa’u kamiltattu kuma da a ce ba su karya dokar Allah ba, da ’ya’yansu ba su gāji zunubi ba. Ƙari ga hakan, da babu wanda zai mutu. A lokacin, Adamu da Hawwa’u da dukan zuriyarsu suna da begen yin rayuwa har abada. Amma, abubuwa ba su kasance yadda ya kamata ba.

Shirley: Gaskiya fa, Adamu da Hawwa’u sun ci ’ya’yan itacen da aka hana su ci.

Megan: Hakika. Adamu da Hawwa’u sun yi zunubi sa’ad da suka ƙi yin biyayya ga Allah. A taƙaice sun zaɓi su zama ajizai. Wannan zaɓin da suka yi ya shafe su da kuma zuriyarsu.

Shirley: Me kike nufi?

Megan: To, ga wani kwatanci. Bari in tambaye ki, kina jin daɗin dafa alala?

Shirley: Ƙwarai kuwa.

Megan: A ce kina da wani sabon gwangwanin dafa alala, amma kafin ki yi amfani da shi, sai ya faɗi a ƙasa ya lotse. Yaya alalan da kika dafa a gwangwanin zai kasance? Babu shakka, zai ɗauki alamar lotsewar, ko ba haka ba?

Shirley: Haka ne.

Megan: Hakazalika, sa’ad da Adamu da Hawwa’u suka ƙi yin biyayya ga Allah, sun kasance da “taɓo” domin zunubi da ajizanci. Dukan ’ya’ya da za su haifa za su kasance da “taɓo” domin sun zama ajizai kafin su haifi ’ya’yan. Dukansu za su kasance masu zunubi. A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan “zunubi” tana nufin wani abu da muka yi da kuma yanayin da muka gāda. Sa’ad da Adamu da Hawwa’u suka yi zunubi, ba a haife mu ba tukun balle ma a ce mun yi wani laifi. Amma zunubinsu ya jawo wa dukanmu ajizanci da kuma zunubi, waɗanda ke kai ga mutuwa. Kamar yadda muka karanta a Romawa 6:23, sakamakon zunubi mutuwa ne.

Shirley: Amma, hakan bai dace ba. Me ya sa dukan ’yan Adam za su sha wahala har abada saboda zunubin Adamu da Hawwa’u?

Megan: Gaskiyar ki, hakan bai dace ba. Amma ba shi ke nan ba. Allah ya ƙudura cewa Adamu da Hawwa’u za su mutu sanadiyyar zunubinsu, amma mu zuriyarsu muna da begen yin rayuwa ba tare da wahala ba. Dalilin da ya sa Allah ya yi mana tanadin fansa ke nan. Ki sake duba Romawa 6:23. Ayar ta ce “sakamakon zunubi mutuwa ne,” bayan haka sai ta ce: “Amma baiwar Allah ita ce rai madawwami cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu.” Saboda haka, mutuwar Yesu ce ta sa muka sami begen yin rayuwa ba tare da zunubi ko mutuwa ba. *

FANSA CE KYAUTA MAFI TAMANI DAGA ALLAH

Megan: Zan so ki mai da hankali ga wani bayani kuma da ke cikin ayar.

 Shirley: Wane bayani ke nan?

Megan: Ayar ta ce: ‘Baiwar Allah ita ce rai madawwami cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu.’ Idan Yesu ne ya sha wahala kuma ya ba da ransa domin mu, me ya sa ayar ta ce fansar ‘baiwa ce daga Allah’? Me ya sa ba ta ce, ‘baiwa ce daga Yesu’ ba? *

Shirley: Hmm. Gaskiya ban sani ba.

Megan: Allah ne ya halicci Adamu da Hawwa’u kuma shi ne suka yi wa zunubi sa’ad da suka ƙi yi masa biyayya a lambun Adnin. Hakika, Allah ya yi baƙin ciki sosai sa’ad da ’ya’yansa na farko suka yi tawaye. Amma nan da nan, Jehobah ya yi tanadin fansa. * Ya ce ɗaya daga cikin halittunsa wanda ruhu ne zai zo duniya a matsayin mutum kamili ya kuma ba da ransa don ya cece mu. Saboda haka, tanadin fansa baiwa ce daga Allah. Akwai wata hanya kuma da fansar baiwa ce daga Allah. Kin taɓa yin tunanin yadda Allah ya ji sa’ad da aka kashe Yesu?

Shirley: A’a ban taɓa yi ba.

Megan: Babu shakka, kina da yara don na ga kayan wasa a cikin gidanki.

Shirley: E, ina da yara biyu, mace da namiji.

Megan: A matsayinki na uwa, ki yi tunanin yadda Jehobah Uban Yesu ya ji sa’ad da Yesu ya mutu. Ina nufin yadda ya ji sa’ad da ya ga aka tsare Ɗansa, aka yi masa ba’a kuma aka yi masa dūkan tsiya. Yaya Uban ya ji sa’ad da aka kafa Ɗansa a kan gungume kuma aka bar shi ya yi mutuwar wulaƙanci?

Shirley: Hakika, ya yi baƙin ciki sosai. Ban taɓa tunanin haka ba!

Megan: Ƙwarai, kuma ba za mu iya sanin yadda Allah ya ji ba a ranar. Amma mun san cewa yana da juyayi kuma mun san dalilin da ya sa ya ƙyale hakan ya faru. Littafi Mai Tsarki ya bayyana mana hakan a Yohanna 3:16. Don Allah ki karanta.

Shirley: Ta ce: “Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya halaka, sai dai ya sami rai madawwami.”

Hadayar fansa tana nuna mana cewa Allah yana ƙaunar mu sosai

Megan: Na gode. Ki lura da abin da ayar ta ce: “Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya.” Hakika, ƙauna ce ta sa Allah ya aiki Ɗansa zuwa duniya ya mutu dominmu. Babu shakka, hadayar fansa tana nuna mana cewa Allah yana ƙaunar mu sosai. Shi ya sa Shaidun Jehobah suke taro kowace shekara don su tuna da mutuwar Yesu. Kin fahimci bayanin?

Shirley: E, na fahimta. Na gode da kika yi mini wannan bayanin.

Akwai wani batu a cikin Littafi Mai Tsarki da za ka so ka sami ƙarin bayani a kai? Za ka so ka sami ƙarin bayani a kan wasu daga cikin koyarwa ko kuma abubuwan da Shaidun Jehobah suka yi imani da su? Idan haka ne, ka sami Shaidun Jehobah don su yi maka bayani a kan waɗannan batutuwan. Za su yi farin cikin tattaunawa da kai.

^ sakin layi na 5 Shaidun Jehobah suna taro sau ɗaya a shekara a ranar da Yesu ya mutu don su tuna da hadayar da ya yi. Wannan shekarar, za a yi taron a ranar Jumma’a, 3 ga Afrilu.

^ sakin layi na 32 A talifi na gaba, za a tattauna yadda hadayar da Yesu ya yi za ta kawar da zunubi da kuma abin da ya kamata mu yi don mu amfana daga fansar.

^ sakin layi na 36 Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa Allah da Yesu ba ɗaya ba ne. Don ƙarin bayani, ka duba babi na 4 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

^ sakin layi na 38 Duba Farawa 3:15.