Amsar Littafi Mai Tsarki

Mulkin Allah zai canja dukan gwamnatocin ’yan Adam kuma ya yi sarauta a dukan duniya. (Daniel 2:44) Muddin wannan ya faru, Mulkin Allah zai . . .

  • Kawar da miyagu, waɗanda son kansu ke jawo wa dukanmu matsala. “Amma za a datse miyagu daga cikin ƙasan, za a tumɓuke masu-cin amana kuma.”—Misalai 2:22.

  • Kawo ƙarshen yaƙoƙi. “[Allah ya] sa yaƙoƙi su ƙare har iyakar duniya.”—Zabura 46:9.

  • Kawo wa duniya ni’ima da zaman lafiya. “Kowa za ya zauna a ƙarƙashin kuringar anab nasa da itacen ɓaurensa; ba kuwa wani mai-tsoratar da su.”—Mikah 4:4.

  • Sa duniya ta zama aljanna. “Hamada za ta yi farin ciki. Furanni za su hudo a ƙasa da ba ta da amfani.”—Ishaya 35:1, Hausa Revised version.

  • Sa kowa ya sami aiki mai kyau da ake morewa. “Zaɓaɓuna [Allah] kuma za su daɗe suna jin daɗin aikin hannuwansu. Ba za su yi aiki a banza ba.”—Ishaya 65:21-23.

  • Kawar da cuta. “Wanda ya ke zaune a ciki ba za ya ce, Ina ciwo ba.”—Ishaya 33:24.

  • Kawar da tsufa. “Namansa za ya komo ya fi na yaro sabontaka; ya komo kwanakin ƙuruciyarsa ke nan.”—Ayuba 33:25.

  • Ta da matattu. “Dukan waɗanda suna cikin kabarbaru za su ji muryatasa [Yesu], su fito kuma.”—Yohanna 5:28, 29.