Ta Hannun Matiyu 20:1-34
20 “Mulkin sama yana kamar wani maigida, wanda ya fita da sassafe domin ya yi hayar waɗanda za su yi masa aiki a gonarsa na itatuwan inabi.
2 Da suka shirya cewa zai biya kowannensu dinari* ɗaya a yini, sai ya tura su su fara aiki a gonar.
3 Da ya sake fita, wajen ƙarfe tara na safe,* sai ya ga waɗansu suna tsaye a kasuwa, ba su da aiki;
4 sai ya ce musu, ‘Ku ma ku je gonata, zan biya ku abin da ya kamata.’
5 Sai suka tafi. Ana nan, sai ya sake fita, wajen ƙarfe goma sha biyu na rana* da kuma wajen ƙarfe uku.*
6 A ƙarshe, wajen ƙarfe biyar na yamma,* ya sake fita, sai ya ga wasu mutane suna tsaye ba sa yin kome, kuma ya ce musu, ‘Me ya sa kuka tsaya a nan tun safe ba kwa yin kome?’
7 Suka ce masa, ‘Domin babu wanda ya ɗauke mu aiki.’ Sai ya ce musu, ‘Ku ma ku je gonata ku yi aiki.’
8 “Da yamma ta yi, sai mai gonar ya ce wa mutumin da ke taya shi lura da aikin gonar, ‘Ka kira masu aikin, kuma ka biya su kuɗinsu, ka soma da waɗanda suka zo ƙarshe har zuwa na farko.’
9 Saꞌad da waɗanda suka zo ƙarfe biyar na yamma suka zo karɓan kuɗinsu, an biya kowannensu dinari ɗaya.
10 Waɗanda suka fara zuwa sun ɗauka cewa za a biya su fiye da sauran, amma su ma an ba su dinari ɗaya.
11 Da suka karɓa, sai suka soma gunaguni a kan maigidan,
12 suka ce, ‘Waɗanda suka zo ƙarshe, aikin awa ɗaya kawai suka yi; amma ka biya su daidai da mu, mu da muka yini muna aiki, muna shan zafin rana!’
13 Sai maigidan ya ce wa ɗaya daga cikinsu, ‘Abokina, ai ban cuce ka ba. Mun yarda cewa dinari ɗaya zan ba ka, ko ba haka ba?
14 Ka karɓi kuɗinka ka tafi. Ina so in ba waɗanda suka zo ƙarshe daidai abin da na biya ka.
15 Ba ni da ikon yin abin da na ga dama da abin da nake da shi ne? Ko dai kana kishi don ni mai alheri* ne?’
16 Haka nan ma, waɗanda suke na ƙarshe, za su zama na farko, kuma na farko, za su zama na ƙarshe.”
17 Da suke hanya zuwa Urushalima, sai Yesu ya kai manzanninsa goma sha biyu zuwa gefe kuma ya ce musu:
18 “Ga shi! Za mu haura zuwa Urushalima, za a ba da Ɗan mutum a hannun manyan firistoci da kuma marubuta. Za su yanke masa hukuncin kisa,
19 saꞌan nan su ba da shi ga mutanen alꞌummai domin su yi masa baꞌa da bulala, kuma su kashe shi a kan gungume; a rana ta uku kuma za a ta da shi.”
20 Sai mamar ꞌyaꞌyan Zabadi ta zo wurin Yesu da ꞌyaꞌyanta, ta durƙusa a gabansa, ta roƙe shi wani abu.
21 Ya ce mata: “Me kike so in yi miki?” Sai ta ce masa: “Don Allah, ka ce waɗannan yarana biyu su zauna, ɗaya a hannun damanka, ɗaya kuma a hannun hagunka a Mulkinka.”
22 Yesu ya amsa ya ce: “Ba ku san abin da kuke roƙa ba. Za ku iya shan abin da na kusan sha?” Suka ce masa: “Za mu iya.”
23 Ya ce musu: “Lallai za ku sha abin da na kusan sha, amma zama a hannun damana da hannun haguna, ba ni nake da ikon bayarwa ba. Ubana na sama ya shirya matsayin nan don waɗanda ya zaɓa.”
24 Da sauran manzanni goma suka ji abin da ya faru, sai suka yi fushi sosai da ꞌyanꞌuwa biyun.
25 Amma Yesu ya kira su, ya ce musu: “Kun san cewa shugabannin alꞌummai suna wahalar da waɗanda suke mulki a kansu, kuma manyansu ma suna nuna musu iko.
26 Kada hakan ya faru a tsakaninku; amma duk wanda yake so ya zama babba a cikinku, dole ne ya zama mai yi muku hidima,
27 kuma duk wanda yake so ya zama na farko a tsakaninku, dole ne ya zama bawanku.
28 Kamar yadda Ɗan mutum ya zo, ba domin a yi masa hidima ba, amma domin ya yi hidima kuma ya ba da ransa a matsayin fansa don ya ceci mutane da yawa.”
29 Yayin da suke barin Jeriko, sai mutane da yawa suka bi Yesu.
30 Sai ga waɗansu makafi biyu suna zaune a bakin hanya. Da suka ji Yesu yana wucewa, sai suka ɗaga murya suka ce: “Ubangiji, Ɗan Dauda, ka ji tausayin mu!”
31 Sai mutanen suka tsawata musu, suka gaya musu su yi shuru; amma suka ƙara ɗaga murya, suna cewa: “Ubangiji, Ɗan Dauda, ka ji tausayin mu!”
32 Sai Yesu ya tsaya, ya kira su, kuma ya ce musu: “Me kuke so in yi muku?”
33 Suka ce masa: “Ubangiji, ka sa idanunmu su buɗe.”
34 Sai Yesu ya ji tausayin su, kuma ya taɓa idanunsu. Nan da nan suka soma gani, kuma suka bi shi.
Hasiya
^ Dinari ɗaya ya yi daidai da kuɗin da ake biyan lebura na aikin yini ɗaya.
^ A yaren Girka, “wajen awa ta 3.”
^ A yaren Girka, “wajen awa ta 6.”
^ A yaren Girka, “wajen awa ta 9.”
^ A yaren Girka, “wajen awa ta 11.”
^ Ko kuma “mai bayarwa.”