Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 ABIN DA KE SHAFIN FARKO | GWAMNATIN DA BABU CIN HANCI DA RASHAWA

Matsalar Cin Hanci da Rashawa a Gwamnati

Matsalar Cin Hanci da Rashawa a Gwamnati

Cin hanci da rashawa a gwamnati tana nufin mutum ya yi amfani da muƙaminsa don ya amfani kansa. Ba yau ne wannan matsalar ta soma ba. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ba da dokar da ta hana karɓan hanci sa’ad da ake shari’a. Hakan ya nuna cewa tun sama da shekaru 3,500, an riga an san da wannan mummunar ɗabi’a. (Fitowa 23:8) Hakika, cin hanci da rashawa sun haɗa da satar kuɗi ko kayayyakin gwamnati ko kuma yin amfani da kayan aiki ba tare da izini ba. Bugu da ƙari, ma’aikatan gwamnati sukan yi amfani da muƙaminsu don su yi wa iyalansu da abokansu alfarma ba bisa ƙa’ida ba.

Gaskiya ne cewa mutane a ko’ina suna iya cin hanci, amma ma’aikatan gwamnati ne suka fi yin hakan. Wata ƙungiyar yaƙi da cin hanci da rashawa a faɗin duniya ta wallafa wani rahoto mai suna Global Corruption Barometer a shekara ta 2013, kuma a cikin rahoton ta nuna cewa a faɗin duniya, mutane suna ganin cibiyoyi biyar mafi cin hanci da rashawa su ne jam’iyyun siyasa da ’yan sanda da ma’aikatan gwamnati da majalisun dokoki da kuma majalisun zartarwa. Ka yi la’akari da wasu rahotanni da suka tabbatar da wanzuwar wannan matsalar.

  • AFIRKA: A shekara ta 2013, an tuhumi ma’aikatan gwamnati guda 22,000 da laifin cin hanci a Afirka ta Kudu.

  • AMIRKA TA KUDU: A shekara ta 2012, an kama mutane 25 a ƙasar Brazil da laifin yin amfani da kuɗaɗen gwamnati wajen neman goyon bayan siyasa. Hafsan hafsoshin tsohon shugaban ƙasar ma yana cikin waɗanda aka kama.

  • ASIYA: A Seoul, babban birnin Koriya ta Kudu, mutane 502 sun rasa rayukansu a lokacin da wani babban cibiyar kasuwanci ya rushe a shekara ta 1995. Masu bincike sun gano cewa ’yan kwangila da suka gina cibiyar sun ba ma’aikatan gwamnati a birnin cin hanci domin su bar su su yi amfani da jabun kayayyakin gini kuma su ƙeta dokokin kiyaye haɗari.

  • TURAI: Kwamishinar Harkokin Cikin Gida ta Tarayyar Turai, Cecilia Malmström ta ce “girman matsalar [cin hanci da rashawa a ƙasashen Turai] ya fi gaban misali.” Ta daɗa da cewa “babu ɗan siyasa da yake da niyyar yaƙar cin hanci da rashawa da gaske.”

Cin hanci da rashawa ya kafu sosai a gwamnati. Farfesa Susan Rose-Ackerman, wata masaniyar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ce “gwamnati na bukatar yin gagarumin canji a yadda take tafiyar da al’amuranta” idan ana so a yaƙi rashawa. Ko da yake yanayin na iya zama kamar babu mafita, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa tabbas za a shaida gagarumin canji a nan gaba.